Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 17

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

                       PAGE 17

Runtse idonta tayi tsayon lokaci yana kallon ta.

   Ahankali yace, yi hakuri kibude idon muyi mgn, ashirye nake daki tare ko yau ne, kawai na iya hakuri ne sabo da Ina son kiyi karatu bawai wani abu, tsintan kansa yayi da cigaba da cewa, ”  wannan auren kuma kakanmu ne ya matsa, akwai alkawarin auren tunkafin haduwa ta da ke, shiyasa yanzu din ma bance a’a, ba, hannunta ya kara matsawa yeyin da yaji wani taushi ya ratsa shi, lumshe Ido yayi sannan ya sake cewa, ” naji dadi dana kalla zallar kishina akwayar idon ki.

   Ni a’a.

Ke a’a me?

Kina da kishi,  naji dadin hakan, sabo da sai kanason  mutum tukana keke kishin sa, kuma kishin hallita ce, toh Amma zanso ki dan rage shi….

     Kokarin kwace hannun ta tayi dake cikin nashi, cikin sauri ya rike hannun dakyau yana fadin Ina zuwa?

      Bacci nakeji.

  Me yasa bakima mutum Uzuri ne Rahma, inason ki fahimci ne, gaba daya nagama gane inda kika dosa, nagane me kike nufi dan haka kibar boye min, Dan na fahimce ki, yanzun abu daya nake so nima ki fahimce ni.

       Rahma kinason ne nazama daya daga cikin munafukan maza?, kinaso ne dole saina bud’e miki cikina, san nan hankalin ki ya kwanta?, indai ba haka kikeso ba toh ki sa ki ranki, ni kadai ya dace kiduba ba Safna ko wata can ba.

      Shiru yayi tsayon lakaci yana kallon ta zuwa can yace barin miki abun da kike so, sau daya na taba ganin yariya ko yanzun muka hadu a hanya bazan iya ganeta ba.

     Sunkuyar dakai kawai tayi, sosai taji babu dadi yadda yake fadin kishin sa take, alhalin shi da ita babu wani alamar dake nuna cewa mijin ta ne ko kauna daga gare shi.

     Sakin hannun ta yayi ya mike tare da fadin, Saida safe.

       Har yakai kofar Bata dago ba, dan haka ya saki kofar ya dawo ciki, tsaye yayi tsakiyar falon tare da fadin zo Nan.

      Karwar dakai tayi tare da juya baya

Kitashi kizo nace ko?

   Ahankali ta mike tafara takowa tana wasa da hannun sa.

   Hannun sa yasa ya jawota jikin shi.

  Kirjin sa ta fada yayin dayasa hannun sa yazagaye ta dashi tare da kankameta kam ajikin sa, duk iya rawan da yakejin jikin nata nayi besa ya saketa ba, tsintan kansa yayi da lumshe ido na tsayon lokaci, wani irin abu ne yake tsarga masa daker ya iya nufar kunnen ta da bakin sa, cikin rada rada yake fadin, ” karki bari kowa ya gane abun dake damun ki, ki saki ranki kiyi harkokin da mutane cikin walwala, bana son a gane lagon ki, ke tawa ce, kisa azuciyar ki kamar hanta da jini.

    Rawa kawai jikin ta keyi ba gane komai take ba har ya gama mgnr sa ya dago kansa daga kunnen ta, saidai memakon taga ya saketa sai wani labari ya canza, domin gani tayi yana bin wuyanta yanata faman sinsina, kara rikicewa tayi sosai.

  Shiko Modibo gaba daya ya kasa barin ta, sai yayi kamar zai dago saiya sake maida kansa, numfashin sa kawai takeji ajikin ta, yayin da jikin ta ke kara rawa sosai, abune wadda yazo mata abakon yanayi, bata taba gani ba, domin ita gidan su ko tv babu, kara gigicewa tayi saidai yana rike da ita duk da Yana jin rawan jikin ta besa ya barta ba.

     Gani tayi yana kokarin dawo da fuskar sa saitin tata dan haka ta fara kautar da kanta, kara taro kanta take tare da mamakin sa, cikin ranta take fadin, ” menene haka, ko amafarki bata taba tunanin haka ba daga gareshi, kokarin kwace kanta take saidai duk irin kokarin da take Saida yai narasar cafko bakin ta, tun daga wannan lokaci rasa a inda kanta yake tayi zuwa ta fara jin gemon sa na yawo afuskarnta, koka ne ya kwace mata cikin numfarfashi sosai ji tayi yana shafarta kadan kadan hakan ya kara gigitata ta saki kara wadda yasa dole ya saketa.

     Agoje tayi tabar dakin cikin matsanancin haki.

       Modibo kuwa bakin gadon ya laluba ya zauna tare da dafe kansa yana fadin, Kash 😬

    Sosai takejin sa arikice, abun da take ji yanzun ko alokacin samar taka beji shi ba, cikin ransa yake fadin, menene haka?

                      ****”

  Yadda ta shigo arikice yasa kowa ya daga Ido ya kalleta, daganin ta kasan ba acikin hayyacin ta take ba, tana tafe tana waigen bayan ta.

     Magaji da Muftahu ne suka bita da kallo yayin da Ammi ke fadin, Magaji ne ko?

    Kofar Unaisa ta kalla sannan ta mike aguje ta shige toilet din Ammi, duk kallo suka bita dashi kafin suka farajin kakarin aman ta.

    Ammi ko har yanzun fadi take Magaji ne.

   Ammi gani kusa dake kita fadin nine fah.

     Sai yanzun ta juya ta kalle shi tare da mikewa tana kokarin fita, bayan ta Magaji yabi hakama Muftahu, Afnan kuwa bayan Unaisa tabi.

    Ammi ce ta fara tura kofar cikin da firgice, cak ta tsaya ganin Modibo zaune abakin gadon yana danna wayar sa kafarsa daya kan daya.

       Au Kaine?, Ammi ta fad’a tana bin sa da kallo.

   Nine Ammi.

Lafiya dai ko?

Mikewa yayi yana fadin, ” lafiya lau Ammi.

   Magaji ne yace, ” toh Ammi gashi nan dai kingani, inda ni tagani tazo ahaka sai aga laifina.

     Ajiyan zuciya Ammi tayi tana bin Modibo da kallo, gani tayi idon shi yayi ja, Bata son ta tsawaita bincike dan haka barshe ya raba ya wuce, jikin shi babu wani kwari.

      Daki su Ammi suka koma bayan sun ga fitan Modibo, adaidai lokacin da Unaisa take fitawa Afnan rike da ita.

    Sannu Ammi ke mata, hakama Muftaho keta fadin Sannu yana binta da kallo.

       Ammice tace yaya meke damun ki.

  cikin sauri ta dafa kanta tare da fadin, kaina ne’

   Toh sannu taho ki kwanta Ammi ta fad’a tana nuna mata gadon ta, ganin su Muftaho taki kwanciya.

    Afnan ce tace taho muje mu kwanta.

   Kai Unaisa tai saurin girgizawa tana kallon Kofar dakin.

    Sallama Magaji yaiwa Ammi, Muftaho ma mikewa yayi suka fita atare.

                          ****

Magaji ka fahimci wani abu kuwa?

Kamar me?

  Meka fahimta tsakanin Modibo da Wala Habaru?

Gaya min kawai tunanin ka.

Ina tunanin fa yana sonta, zama aure kuma zai da ita, ni sai yanzun ma nake mamaki yadda ada har mukayi tunanin zai saketa, ka duba yariyar fa kagani, kalar hutawa ce, ko Safna dake tagama da iyayenta babu abun da zata nuna mata.

     Zata nuna mata asali Mana, yariyar Bata da wani asali, sannan kuma kasan d’an kauye be iya samun guri ba ranar nan bakaji mgnr da take gaya min bane, Bata  bari na rufe baki dana fada take bani amsa.

   Dariya Muftaho yayi tare da fadin, toh ai Zama da madaukin kanwa, ai haka Modibo yake yi tamkar jira yake ka fada ya mayar maka, kuma kasan Allah, wlh son ta yake.

  So?, Modibo?

  Kana Mamaki ne?, tafi Safna komai fa, yama za’ayi a hada, ko ita waccen yar gidan Malam liman dinan da za’a bashi tako kama kafar ta ba.

  Jimmm Magaji yayi yanzun kana nufin zaman aure zai da ita a matsayin matar sa?

  Eh Mana, aini tuni na zubar da makamai na, ko yanzun Ina zargin tabata yayi fa, baka yariyar a gigice ba?

   Modibo??

  Shi fa, me kake tunani, wai kana ganin kamar yariyar Bata Kai bane ko kuwa yaya ne?, Bari kaji idan Modibo na tsaye yariyar na tsaye ka dinga nazarin su zakane abun da nake gaya maka, wlh Modibo na masifar son yariyar nan, basarwa kawai yake yi, itama kuma tana son shi.

  Eh idan kace ita yariyar tana son shi na yadda, domin tun a gidan su nake zargin haka, shi kadai takema mgn, amman Modibo zanyi mamakin ace Yana son yariyar nan sabo da yanayin gidan su, shikenan yariyar Bata da dangin uwa Bata da na Uba

   Hmmm shikenan, nidai Ina baka shawara ka fita harkar yariyar nan, wani tsareta a hanya wani cacan vaki da ita gara ka bari sabo da kar azo a samu matsala, ayanzun ko Modibo beson tama dai matsayin matar aure take kuma duk abun da ya faru mara kyau yanzun zakaji ana cewa Matar yayan sa yaima kaza, akwai mata awaje kasan inda zakaje ka same su, gara kabi komai ahankali.

   Hmmm da alama dai ka janye?

Eh nikam na janye, Suraj ma ya janye, kasan yanzun hankali shi yana gurin Yadikko, a kullum hankalin baya jikin ta.

         Daganan hirar tasu ta koma kan rashin lafiyan Yadikko.

Daren yau kasa bacci tayi, duk inda ta waiga shi take gani, saidai hakanan taji ta samu saukin daga zugin da zuciyarta ke mata, tunasa take tare dajin nishadi na shigarta, har washegari da safe batar tunasa ba saidai Bata ganin zata iya hada Ido da Modibo ayanzun, duk da cewa shikadai yai kid’an sa yai rawar sa, amman abun nauyin shi take ji.

      Bayan kwana biyu wadda yai daidai da saura kwana shidda bikin Modibo.
da Safe suna zaune adakin Ammi ita da Afnan Ammi ce ke sanar dasu yau yau za’a kai kayan auren Modibo.

  Take Unaisa taji gabanta ya fadin, bata Kara tsinkewa ba Saida taga  dagin su mata sunata shigowa, kayan aka bubude ana kallo.

   Rahma nadaga kwance akan akan gadon Ummi tajin maganganun da matan keyi, duk yaba kayan suke kowa na cewa sunyi kyau, ba kallon kayan tayi ba saidai abun Mamaki ta gefen idon ta saita hangi wata mata na wurga Ido cikin rashin gaskiya tana tura hannun ta cikin Babban akwatin dake gaban ta.

  Gaba daya Unaisa ta waiga ta kalli matar, itama Matar cikin sauri ta dago ta kalli Unaisa sukai Ido 4, cikin sauri ta waiga ta kalli jama’ar dake wajen kowa na harkokin sa, juyawa tayi ta kalli Unaisa cikin ranta take fadin wacce shegiyar yariyar ce wannan, harara ta gallawa Unaisa tare da zare mata idon…….