Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 22

Posted by

BA LABARI BOOK 2 PAGE 22

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

EXQUISITE WRITER’S FORUM.

PAGE 22

Itama Unaisa tunkan ya karaso gurin ta ganshi dan haka ta hadiye dariyar ta.

Ganin yana sauka amotar ya kallo su  yasa Unaisa tai saurin yin sallama da Kabir ta nufi gida.

Haka nan ta tsincin kanta da sauri karya cin mata duk da ba lallai ita din zaibi ba, harta nuf su sai kuma ta canza tunanin dan haka ta juyo da baya zuwa dakin Ammi.

Ta shiga ba jimawa shima ya shigo, Zama yayi ya gaida Ammi sannan yadan kalleta kadan ya kawar dakai.

Tsayon lokaci suka dauka shida Ammi suna mgn sama sama duk da cecwa itma Ammin yau Kamar batajin yin hirar dashi.

Zuwa can ya mike yabar dakin.

Ammice ta juyo ta kalle Unaisa tace ke kuma lafiya kuwa?

   Lafiya lau Ammi.

A’a kodai ke da Modibon ne, naga Kamar kina ra’be ra’be ne?

    A’a Ammi ai…..

Karan wayarta ya hanata karasa fadin abun dataso fada, Modibo ne dan haka tai saurin amsawa tare da Sallama a bakin ta.

    Be amsa Sallama bar ji tayi kawai yace, ” Kina dakin Ammi ne har yanzun?

   Ahankali tace, eh

   Tashi ki koma dakin ku.

Tam, tace tare da mikewa, da kallo Ammi ta bita ko ba’a fada ba tasan Modibo ne.

 Har ta isa daki wayar na hannun ta Zama tayi gefen gadon, cikin sanyin jiki sosai tace, ” Na fito”

  Uhum, yayi kyau, tambayan ki zan yi.

 Tam, ta fada a hankali.

Kinaji na

Eh inaji

 Inason ki gaya min menene Aure?

Jimmm tayi tsayon lokaci ta kasa cewa komai.

Shima shiru yayi yana sauraron ta

Baki sani ba?

   Nasa ni.

  Toh Ina sauraron ki.

  Kasa mgn tayi, domin batama san ta Ina zata fara ba.

Tun da kin kasa mgn ni banrin gaya miki, “aure shine had’a wata irin alaka
tsakanin mace da namiji, wannan yana nufin had’e rayuwar su ta zama daya.

haka nan kuma makomar su ta kasan ce guda daya, kuwace irin al’umma akwai irin matsayin da ta ba wa aure.

Ajiyan zuciya taji yayi cikin wani irin murya kasa kasa taji yacigaba da cewa,

” Aure a musulunci wani dauri ne da
yake halatta wa ma’aurata, mace da
miji jin dadi da junan su, ta hanyar
saduwa irin ta Jima’i da saura ma’amaloli, Allah subbannahu wa Ta’ala ya halicci mace daga hakarkarin namiji
ya kuma sanya soyayya da tausayi a
tsakanin su, kamar yadda ya gaya
mana a Alkur’ani mai tsaki.

Nisawa taji ya kara yi sannan yace, ” kina jina kuwa?

Ahankali tace eh, saidai tuni kafafuwan ta suka gaza daukan ta jin kalmar jima’i abakin Modibo.

Cigaba yayi da cewa, “Wannan yana nuna mana cewa alaka tsakanin mace da namiji Allah ne ya kulla ta tun fil azal abin da kuwa Allah ya had’a  babu wanda ya isa ya raba shi, Wannan shi ne yasa a d’abi’ance kowanne namiji yana bukatar mace, haka kuma kowace mace tana bukata namiji, Wato kowane daya ba zai iya wadatuwa da kansa ba, ya rayu shi kad’ai, dole sai dai  had’e da wanin sa.

 Duk ilahirin jikin Unaisa rawa ya dauka, jin irin wad’an nan kalmomin abakin Modibo, bata taba tunanin jin irin su daga gareshi ba, acikin ranta take tunanin, shi bayajin nauyin furta irin waddan kalmomi ne, jinshi tayi yaci gaba da cewa,

” Miji yana da hakkoki a kan matar sa, wad’anda ya wajaba ta kiyaye da su, kuma ta sauke nauyin su, Allah Madaukakin Sarki ya ce,

“Suma mata  suna da kwatankwacin abin da yake kansu da adalci, ma’ana suma mata suna da hakki a kan maza, irin hakkin da maza suke da shi a kansu. don haka kowa ya baiwa d’an uwansa
hakkin sa da adalci.

Hakkokin Miji akan matar sa suna da yawa, kuma suna da girma, saboda haka Manzon Allah (S.A.W) yake cewa hakika ni da zan umarci wani ya yi sujjada ga wanin Allah, da na umarci mace ta yi wa mijinta sujjada, mace ba zata biya hakkin Ubangijin ta ba, har sai ta bayar da hakkin mijin ta, kuma da zai
tambaye ta kan ta, alhali tana kan
siddin raqumi da baza ta hana shi
ba.

Tsintan kanta tayi da zubar da hawaye, yana furta kalmomin suna tafiya zuciyarta kai tsaye.

Alama yaji tana kuka dan haka ya fara tunanin takaita zancen sa, duk da cewa be nuna mata yasan tana kukan ba, zaman shi ya gara sannan ya cigaba da cewa,

“Daga cikin hakkokin miji a kan
matar sa, wadanda ya wajaba ta
kiyaye su, kuma ta sauke su, akwai yi masa biyayya, musulunci ya
umarci mace ta yi wa mijinta
biyayya cikin abin da bai sabawa
Allah madaukakin Sarki da Manzon
Allah (S.A.W) ba.

Ya inganta a cikin hadisin Abu Hurairata (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce Idan Mace ta sallaci biyar din ta, ta
azumci watan ta wato Ramadan ta
kiyaye farjinta, ta yi wa mijinta
biyayya, za ta shiga Aljannah daga
kofar da taga dama daga cikin
qofofin Aljanna.

Biyayyar mace ga mijinta wajibi ce, kuma idan mace ta saba wa mijin ta, ta ki yi masa biyayya, to zata wayi gari a cikin fushin Allah, har sai mijinta ya yarda da ita, ya daina fushi da ita.

Shiru yayi yana sauraron Unaisa, wadda zuwa yanzun kukan ta Baya boyuwa, kuka take sosai harda shashsheka yayin da idon ta yayi jawur tana rike da wayar a kunnen ta.

  Ahankali Modibo yace, ” Kuka kike yi?, ki daina kuka, ina tunatar dake ne dan naga kamar kin manta nauyin dake kan ki, ko kinfi son in barki kiyi abun da kikaga dama?

Ahankali cikin murya me cike da kuka
tace, a’a

Yauwa Aunty na, kinsan shi aure daraja gare shi, manzon Allah (S.A.W) ya ce wa wata mata ki duba, meye matsayinki a wurin mijinki, domin shi ne Aljannarki ko wutarki, biya Masa bukatar Aure Wajibi ne akan mace ta biya wa mijinta buqatar sa ta aure, ta amsa masa a duk lokacin da ya bukace ta, manzon Allah (S.A.W) ya ce

“Idan mutum ya kira matarsa zuwa
ga shimfidar sa, ba ta zo ba, ya
kwana yana mai fushi da ita, to
Mala’iku za su la’ance ta, har sai ta
wayi gari,

Sai dai baya halatta mace ta yi wa mijinta biyayya wajen kwanciyar
aure in tana tare da wani uzuri da
shari’a ta yarda da shi, kamar idan
tana cikin jinin al’ada ko biki, ko
kuma in tana azumin farilla, ko idan
ya neme ta dubura, ko yayin da take
cikin aikin hajji ko umara, da
sauran su, saboda yarda da haka
sabawa Allah ne kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, babu da’a ga wanin abin halitta cikin saba wa mahalicci.

Jin har yanzun kuka take yace shikenan ya isa haka, kibar kuka kinji kanwata, dazon na ganki kina dariya gaban mijin daba naki ba, raina ya baci sosai…..

 Kayi hakuri, Unaisa ta fada ahankali

  Nayi ai,  amman daker fa na taushi zuciya ta, am kina da hijjabai ne?

   Eh.

  Toh dan Allah ki dinga sawa kinji.

    Ahankali tace Tam.

Toh sai anjima Bari na barki haka, amman ki daina kuka tunasarwa ce kawai na miki.

Sauke wayar tayi tare dajin wani irin Mummunan tashin hakali, wato duk nauyin nan daya zayyanu yana nufin akwai su akai na kenan?

Ina son in tambaye shi amman bazan iya ba, kuma banda wanda zanma wannan tambayan sai shi, wayarta ta kalla tsintan kanta tayi tana rubutu cikin sa bayan ta gama ta tura mishi.

     Komawa tayi kan gadon ta kwanta rufda ciki, sosai hankalin ta yake a tashe, hawaye ne ke zobo mata tana sharewa.

                    ******

Hamma Modibo wani zancen auren ne ya tashi naga sai gyra ake yi?

 Juyawa yayi ya kalleta tare da cigaba da gurza soson wankan ajikin sa yake fadin, ” a’a, kawai dai Ina ‘karawa gurin fad’i ne.

 Nidai idan aure zakayi ka gaya min kawai.

    Safna nataba boye miki labarin aure ne?

    a’a

Atoh mezaisa na boye miki?

    Haka ne, aiko ana gamawa can gefen zan koma…..

Haba?, Modibo ya fada Yana kokarin jawo towel ya daura a kugun sa.

   Da Gaske.

  Yafi naki ne?

  A’a befi ba, amman yanayin tsarin gurin ya burge ni.

Toh karfa kitashi ki koma can wata rana nayi aure nasa anan kuma kizo kina korafi.

  Jimmm tayi sannan tace zanyi shawara.

  Toh kiyi da wuri, idan aka gama aikin can gurin bazan baki ba, sannan kuma idan kinason nabaki shawara kiyi zaman ki anan sabo da yafi girma idan kina son gyara sai a miki.

   Jimmm tayi zuwa can tace shikenan, amman dai aure zaka zyi ko?

Gyara jikin sa yake Yana fadin, baki yadda ba kenan.

      Na yadda shikenan.

Hannun sa ya mika ya dauki wayar sa, sako ya gani daga Rahma dan haka ya gyara tsayowar shi ya bude sakon tare da daura idon sa akan rubutun.

     * _Yanzun duk wannan nauyin daka lissafa akwaisu akaina?, Ina nufin auren da Dada tace an mana nawasa ne kona ko na gaske_*?

     Dariya ce ta kwace mishi batare daya shirya ba.

      Cike da Mamaki Safna take kallon yadda yake dariya, idon shi akan wayar sa.

   Zuwa can taga ya waigo ya kalleta sannan ya aje wayar.

     Batace mishi komai ba har ya gama shiryawa ya fita.

                    *****

Naga Sakon ki dazon, meyasa baki tambayeni ba tun lokacin da muna wayar?

   Shiru tayi tana kwance ruf da ciki akan gadon su, yayin da Afnan ta fito wanka tana shiryawa.

    Na lura kuruciya ke damun ki, shine yasaki wannan tunanin, kuma akwai abubuwa da dama wadda baki sani ba, barin yi afani da wannan damar in sanar dake ranar daurin auren Afnan zaki tare.

   Gigicewan da tayi yasata kwarewa sakin wayar tayi agigice ta nufi bayi, amai ta shiga kwarawa cikin Mummunan tashin hankali, Afnan ce tabi bayanta tass ta amaye abun da daci, daker Aman ya tsaya suka fito yayin da Afnan ke fadin menene, me aka gaya miki cikin wayar?

     Hawayene ya zubo mata layi bibbiyu tana fadin, Afnan kinji wai nice zan tare agidan shi ranar auren ki?

     Ajiyan zuciya Afnan tayi, sannan tace, eh naga Ammi Bata gaya miki bane shine nai shiru.

     Da Gaske ne kenan?

    Da gaske ne Unaisa, ni banga abun tada hankali ba.

Cikin matsanancin kuka tace, Afnan bazan iya ba, ko zaman minti goma ne idan yana gurin takura nake yi, ina daukan shi da daraja bazan iya zaman aure dashi ba.

    Dariya Afnan tayi tare da fadin, idan ke bazaki iya ba aishi zai iya.

    Shima bazai iya ba Afnan.

    Cike da haushi Unaisa Afnan tace, toh shikenan, tunda bazai iyaba kema bazaki iya ba ai takwana gidan sauki, saiku zurama juna ido, juyawa Afnan tayi tana kokarin fita take fadin ninatafi dakin Ammi.

   Zama bakin gadon tayi sannan ta shiga kiran Dada, Kamar jira Dada take ta dauka.

     batare darayi Sallama ba tace Dada wai kinji ranar bikin Afnan yace wai zan tare.

   Eh Unaisa ai daman zaman ya isa haka.

jin kukan Unaisa yasa ta bude baki cike da mamaki tace au Unaisa kina nufin har yanzun baki son aure ne?

 Dada nifa Uba na dauke shi.

  Au toh, abun haka ne?, ashe bazaki iya zaman aure dashi ba?

 Eh, Unaisa ta fada tana share hawaye.

 Katse Kiran Dada tayi taita kiranta taki dauka, gajiya tayi dan haka ta sauke wayar, zuwa can tai shiru tawan lokaci, tashi tayi aguje ta sake komawa bayi, aduk lokacin data hangota ita da Modibo zaune guri daya saitaji tashin hankali, amai 4 tayi sannan ta nufi dakin Ammi idon ta jawur.

9 comments

  1. Pingback: พรมรถ
  2. Pingback: top webcams
  3. Pingback: webcam coins
  4. Pingback: Huaylike
  5. Pingback: pgslot
  6. Pingback: นิยาย
  7. Pingback: pgslot
  8. Pingback: Blub

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *