Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 page 21

Posted by

BA LABARI BOOK 2 page 21

 

BA LABARI BOOK 2
By
Fadila lamido

page  21

Safna lafiya?, me ya faru?

Ammi cewa yayi in tafi gida.

Bangane ki tafi gida ba?,  fada kuka yi?

  A’a Ammi, haka nan naga dai sai fad’a kawai yake yi, zan kwanta anan da safe sai in wuce.

   Babu inda zaki Safna mikewa Ammi tayi tana fadin, Ina zuwa…

  Sai dai tana mikewa Yadikko na shigowa, ganin yadikko Ammi tace’ lafiya?

     Lafiya lau Yadikko ta fada, juyawa tayi ta kalli Safna sannan tace, ” muje falon to.

   Falo suka fito, Yadikko ta fara zama sannan Ammi ta zauna tana fadin, “yau bakiga Safna a part dina ba?

   Naganta lafiya ko?

  Ita da Mijin ta.

Allah ya kautaa Ammi ta fad’a sannan tace Modibo ya taso ni.

   Jimmm Ammi tayi zuwa can tace, Wai me?

    Ki baShi da matar shi, amman Hajiya kema ai ba haka ake yi ba, kefa kawai ajiya aka baki, kuma me Kaya yazo karban kayan sa sai ace be isa ba wannan wanni irin karfin hali ne.

   Ai wai sabo da wannan ya taso ki, ai begama karfin hali ba sai nan gaba, bari kiji abun da ya faruwa, Wani abokin Abban su ne yazo neman ma d’ansa auren Rahma, shine duk yabi ya susuce, daga dakin Abban nasu tun bakin Basu fitaba ya dare min tsiya anan, waishi ala dole lallai sai tare agidan sa nan take.

   Dariya sukayi gaba daya yayin da Yaddiko tace, ai haka din shine kadai mafita.

  Yanzun ke kin goyi da bayan abashi ita ayau kamar yadda yake so?, ai wannan ma ba abu bane wadda zai yiyu, da ace Yana shigowa da Rahma gidan nan aranar ta tare shikenan, amman karfa ki manta nan ya ajeye min ita, kowa anan ya santa, yanxun ana neman shekara ta biyu kenan sabo da Allah  saikawai da tsakar rana yace zai dauketa yau saikace yaki.

    Toh Hajiya kina da ‘yar gaskiyar ki kema, amman dai duk da haka kidaure ki bashi matar shi gaskiya tunda ya nuna hakan yafi so.

  Wlh kinji na rantse Bata tare yanzun ba, dan yanzun ma jarabawa suke saiyayi hakuri saita gama, sannan kuma a part din shi banga gurin zaman ta ba sai yayi gyara, nufin shi haka zai kwashe ta ya kaita Bata da ko tsinke salon kishiya ta raina ta, Ina tunanin fa duk kayan Safna ne acikin gidan Nan

    Hajiya idan ya ajeta a dakin sa fa?

    Nidai nafi bukatan ya nutsu yayi gyara sannan yayi mata kayan aure sannan ya dauke matar shi.

    Yanzun dai bazaki badata ba yau din kenan.

    Bazan bada ba kuwa ko yafi kuturo naci.

   Mikewa Yadikko tayi tana kokarin fita Ammi tace, ” ga Safna ki mayar masa da ita.

    A’a wa ya aike ni, gida zani dare yayi, mikewa tayi ta fice yayin da Ammi ta biyo bayan ta tana fadin, ” babu Sallama?

   Allah ya tashe mu lafiya Yadikko tace sannan tayi waje, cikin motar ta samu Modibo, saukowa yayi ta shiga ta zauna tare da fadin, ” Kasan halin Ammin ku dai basai na gaya maka ba, toh tace ita ala dole saika gyara guri zaman Rahma sannan kayi mata kayan aure Kamar yadda akema kowacce mace.

     ka kwatar da hankalin ka, kayi gyaran Kamar yadda tace, sai ka tsaida ranar daidai data kare karatun.

  Yadikko ni banson haka fah gaskiya….

  Kayi hakurin Modibo.

  Shikenan Saida Safe ya fad’a yana kokarin wucewa, zo Yadikko ta sake Kiran shi, dawowa yayi ya tsaya.

     Kome Safna tai maka kayi hakuri, nasan kana cikin fushi kada ka bari laifin wani ya shafi wani…..

   Toh Yadikko nagode Saida safe.

    Juyawa yayi yayi da Suraj yaja motar Yana fadin, ” Mutumina a huce haka.

      Shigewa yayi batare da ya juyo ba, ya shiga ba jimawa Ammi ta shigo Safna nabin bayan ta.

    Dagowa yayi ya kalleta, gyara fuskan shi yayi kadan  tare da mata Sannu, har yanzun fuskan shi babu walwala.

       Amsawa tayi sannan tace, me Safna ta maka zakace ta tafi gidan su da daddaren nan?

    Ammi Rashin kunyan tamin.

  Cike da mamaki Ammi tace, tace maka me?

   Fad’#’a na mata ta ta fita a fusace harta buga min kofa.

  Jimmm Ammi tayi acikin ranta take dariyar Modibo domin dai tasan a kule kawai yake afili kuwa cewa tayi, ” toh Allah ya baka hakuri miji, me mata, juyawa tayi ta kalli Safna tace ke kuma idan gin gansa cikin irin wannan yanayin ma kibar masa mgn ma indai Bata zama dole ba.

    Amsawa Safna tayi sannan Ammi ta fice, har yanxun Safna na tsaye inda Ammi ta barta tama rasa abun da zatayi, tsayon lokaci ta dauka a tsaye sannan ta bude baki ahankali tace kayi hakuri.

       Shikenan ya wuce, ya fada batare daya kalleta ba.

      Ahankali ta sake cewa, akwai abun da zan kawo ma ne?

     Babu ya fada ahankali…

      Juyawa tayi tana fadin, saida safe.

                  ******

Momy haka kawai fa ban mishi komai ba.

yaushe ya fara hakan?

  Yau ne Momy kawai, yadda hankalin shi Yake a tashe yau Koda aka fasa auren be shiga damuwa haka ba.

Kuma kince bake kika Bata mishi rai ba?

  Ammi lafiya lau muka rabo da Safe nan.

     Toh ko a Office din nasu aka bato mishi rai?

  Beje ba yau, Abba ne ya Kira shi kawai yaje falon sa ba inda yaje yau, kuma yana dawowa ya dawo a birkice.

    Toh inga Abban nasu ne halan, duk yadda akayi daga nan ne.

   Baki fa yayi kawai yace yazo su gaisa.

     Toh me ya faru?

   Ina wannan yariyar fa?, Momy ta tambaya.

Rahma?

Ita fa tana nan acikin gidan?

  Tana nan Ammi, amman shifa bayama wani kulata Momy.

Ai bazai kulata ba, inda zai kulata kusan shekaranta biyu agidan ai, ki sake jikin ki babu wacce zata shigo miki cikin gidan ki, shi kuma ki barni dashi, ki kwanta kiyi baccin ki, kina da uwa wacce take tsananin kaunar ki, bazan barki kiyi zaman kishi ba, ki mike kafa cikin gidan ki kiyi abon da ranki ke so, idan har zai iya yin rayuwar aure da yariyar nan toh zai iya yi da uwar shi.

     Ajiyan zuciya Safna tayi sannan tace nagode Momy, sai munyi waya da safe.

   Allah kaimu, yanzun abun da zamu maida hankalin mu akai shine mu fara neman haihuwa, mikewa tsaye zamuyi karkiga Yana nuna miki be damu ba, munafuki ne yaro ne Modibo.

   Toh Momy, nifa daman abun na damu na, sabo da duk wannan auren da ake cewa yayi shi sabo da rashin haihuwar ne, inda na haihu da babu wadda zaiyi wata mgn.

                  *****

Safna ce ta shigo cikin dakin su, inda ta hangi Unaisa kudundune cikin lallausan bargon su me taushi.

    Mamaki ne ya kamata, ahankali ta isa bakin gadon tadan bude barkon tana leken fuskanta..

   Bacci taga tayi tana sauke numfashin ahankali, Mamaki ne ya kamata

      Dan tabata tayi kadan.

     Bude idonta tayi a hankali ta sauke su akan Afnan.

     Wai Bacci kike yi?

  Toh me zanyi idan banyi bacci ba?

Aini wlh nadauka bazakiyi bacci ba, yadda naga Hamma Modibo ya shake miki wuya dazon na dauka yau kwanan kuka zaki yi.

     Dariya Unaisa tayi har ya Bata sauti sannan ta gyara kwanciyarta tare da fadin, ” Saikace da?, ni wlh Mamaki ma ya bani, kawai sai naga mutum daga Sama, kinsan na dade banganshi ba.

    Aiko yau dai kin Mai kyakyawan gani kawai sai naji tayau, Kai Hamma Modibo akwai zafi.

     Tashi Unaisa tayi ta zauna tare da shafa kumatun ta idan Modibo ya mara tace, ” Kinsan wani abu?”

     a’a

  Naji zafin Marin da yaimin sosai ba kadan ba, amma yana cewa in wuce muje, naji nafi bukatar mutuwa ta.

     Dariya sosai Afnan tayi sannan tace, kina nufin da ki tare gidan sa gara mutuwa?

     Toh Afnan ta Yaya zan fara rayuwa dashi? aini in naje gidan shi kun tata zanyi, ta yaya zan fara rayuwa dashi.

    Hakane fa, shima dai Hamma Modibo yaci ya fara aiko soyayyar shi, dan ya janye hankalin ki, amman shi sai inga yana daure fuska koda yake wani lokacin Yana cewa inje in gaidar masa da Ammi, kare ke mgnr tayi cikin dariya.

   Itama Unaisa dariya tayi, sannan tace, “toh me kike nufi?”

   A’a Amma ba Mamaki matse ki yake, Ammi ma da naje nace mata wai Hammana nagaida ki saita tabe baki tace kwanta abun ki.

       Baki da Mutunci Afnan, ni baya wani tabani.

      Ke dai aunty Unaisa ki fadi gaskiya.

   Hmmm Afnan kenan, me zan boye miki?, shiyasa soyayyar ki da Kabir take birge ni, idan kina rayuwa damasu irin halin sa sai nake tunanin ko hawan jini bazai kama ka ba, sabo da mutun ne me fara’a da wasa da dariya wani abun ma da gangan yake fada dan nai kawai kayi dariya.

    Ke kuma dake mayar dariya ce sai kita tayi ko.

   Eh Mana  wlh ko hango shi nayi sainayi dariya kuma kema fa haka kike?

   Allah?

   Da Gaske wlh, Rahma ta fada tana mikewa.

   Toh Hamma fa shi ya yake?

    Wanni Hamman?, Magaji ko *Fahat*?

     Dariya Afnan tayi tare da fadin, ” lallai ma Aunty Unaisa wato Fahat ma kike cewa.

     Ai gara ki kirashi da sunan soyayya zaifi.

      Kinji ki, ke abun da ya dame ki kenan ko?

       Kina nufin ke soyayya bata dame ki ba?

Ni ban sani ba Safna, ko Ina so ko banso ma ni sam bansani ba.

    Baki sani bafa kike??

  Eh Mana, kinga fa, nina farko nataso cikin wata irin rayuwa me wuyan kwatantawa, wlh bani da niyayyar aure Sam, ban taba kawowa cewa zanyi aure ba, nadauka Allah ya halliceni ne kawai inyi rayuwata ni daya in koma ga Allah, kwatsam sai kawai Allah ya sako shi cikin rayuwa ta, bashi bane na farko daya fara son shiga rayuwa ta ba, amman shine mutum na farko daya fara nuna min sai nabi Umarnin shi ko inaso ko bana so, a karshe ya taho dani da auren shi akaina, hawaye Unaisa ta share sannan tace, “dan haka ina ganin bansan wata soyayya irin wacce kike fada ba, kuma shima nasan ba irin wacce kike fada yake min ba, domin da irinta ne da tuni ya nemi da intare agidan shi.

      Cikin sanyin jiki sosai Afnan tace, niban gane ba, kina nufin ba soyayyar aure kuke ma juna ba, am dan Allah kina son Hamma na??

    Afnan bansan inda zan kwatanta miki yadda nakeji shi ba, yayi min komai a rayuwa, daza a tambayeni ace min waye madubin rayuwata, toh zance shi ne, idan nace madubina Ina nufin wadda nake kwaikwayo, kusan shine komai nawa domin ya tare min abubuwa da dama.

      Kenan kina nufin ba Soyayyar irin ta aure a tsakanin ku?

   Har kinsa gabana ya fadi Afnan, dan Allah kibar sa irin wannan abun cikin tunanin ki, banajin zan iya, kuma shima banajin zai iya Afnan.

     Hmmm amman kuma kina son shi fa Unaisa, lokacin da zaiyi auren nan har Ammi Saida ta gano tsananin kishi a idon ki, shima kuma ya gane dan na taba jin shi Yana cewa Ammi kinfi aunty Safna kishi.

     Afnan wannan lokacin ma ni bansan me nake yi ba wlh.

   Kallonta Afnan taitayi tsayon lokaci sannan ta mike duk ajikin ta a sanyaye.

                              *****

Alhaji Amman ban zaci zaka aurar da ita yanzun ba?

   Komai lokaci ne ai, ita kadaice mace Allah ya bamu, tunda ta samu miji gara amata aure.

Shikenan Ammi ta fad’a a sanyaye.

   Yauwa addu’ar ki kawai muke so, sun kawo komai an kuma karba, har mun taida rana

   tab din, amman shine ko ayi shawara dani.

    Nayi shawara da ‘yan uwana ai, kuma Magaji da Modibo ma anyi komai agaban su, matar Modibo *Rahma* za’a kaita dakin ta ranar da za’akai Afnan gidan mijin ta.

     Haba Alhaji, duk Nan da sati 4 din?

      Amsa Abban yabawa Ammi da eh.

   Gaskiya Alhaji mu bamu shirya ba, akwai sayayyar da nake son nai mata kafin ta tare.

   Bamaso, kinar kayan ki, duk abun da akama Afnan za’a mata, ko akwai wani abu kuma?

   Akwai Alhaji.

  Toh inajin ki?

  Aina Modibo zai aje Rahma?

Idan kintashi daga nan kishiga Part dinsa kiyi kallo ana Kan aiki yanzun haka.

   Yawu Ammi ta hadiye sannan tace, toh ai shikenan, Allah ya tabbatar da alheri.

   Ameen waddan addu’ar sukafi bukata shiya na gaya miki, da sai ana saura mako guda zan gaya miki.

   A’a gara da aka gaya min, meyai zafi.

                            *****

Unaisa ce tsaye jikin motar Kabir wadda Afnan zata aura, hira yake sosai tare da Basu dariya, Unaisa ce keta kyalkyalar dariya yayin da Afnan ke fadin, ” wlh idan kika biye mashi sawa zai cikin ki yai ciwo.

Dariya Unaisa ta Kara sawa, hakan yayi daidai da shigowan motar Modibo cikin gidan.

   Tundaga gate din idon shi ya sauka akan ta, dariya kawai yake hangowa akan Fuskan ta idon ta akan Kabir gyalen ta ya hanga rataye a kafan ta guda daya…….

4 comments

  1. Pingback: Sciences_2025
  2. Pingback: scammers
  3. Pingback: AsterDex

Comments are closed.