
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 24
Saida ta isa gaban shi tukuna ta tsaya, daker ta iya bude baki tace, zan wuce.
Kallonta yayi sama da kasa sannan ya wuce ta ya shigo cikin dakin Ammi.
Afusace ta fice adakin.
Modibo ko Zama yayi akujerat dake gefen gadon Ammi yana fuskanta Ammi da Yadikko tare da fadin, ” sannu ku”
Amsawa sukayi sannan ya tambayi Yadikko jikin ta, yayin data amsa masa da Alhamdulillahi
Unaisa kuwa wasa take da hannun ta, idon ta a kasa, sai dai daka kalle ta kasan tana cikin fushi sabo da yadda fuskanta yake a yamutse.
Ajikin ta taji Yana kallon ta, dan haka ta dago ahankali tace, Ina wuni?
Saida ya kare mata kallo sannan yace lafiya lau.
Tanajin ya amsa ta mike ta fice adakin, binta yayi da kallo harta fice sannan ya fuskanci su Ammi.
Itama Ammi saida Unaisa ta fice adakin sannan ta maida hankalin ta kan Modibo tana fadin, ” wannan zaman zai yiyu kuwa, gidan su daya, nifa banson tashin hankali.
Yadikko ce tace aikuwa dai sai anyi da gaske matsawar guri daya zasu zauna.
Ammi ai nace kije kigani kinki zuwa ne, an yi gyara sosai, gefen kowa daban, falona ne kawai zai iya hada su dake tsakiya, kowacce zatayi harkokin ta batare da daya tama sani ba.
Hmmm Modibo bakasan irin wannan zaman ba da zaiyiyu daka raba masu gida.
Yadikko in kin fito kizo muje ki gani, insha Allahu babu wata matsala.
Hira sukaciga dayi daga nan zuwa can Yadikko ta mike zata tafi, Modibo ma mikewa yayi ya biyo bayan ta.
Suna tafe suna hira har suka iso gurin sabon ginin da aka yi gefen na Modibo, sosai aka kawata gurin, ta Sabuwar kofar dake gefen tasa suka bi, inda ya bude kofar suka shiga, doguwar hanya ce suka wuce Sannan falon ya bayyana wadda ya kawatu sosai, komai yaji acikin sa, saidai babu komai, Kofofi dake dama sukabi na ma dakunan bacci ne guda biyu kowanne da bayi acikin sa.
fitowa sukayi falon inda Modibo ya sake bud’e wata kofar madaidain kitchen ya bayyana wadda aka kawata shi, nan Yadikko ta shiga fadin masha Allah, a lallai guri yayi kyau, ya kamata Hajiya ta shigo taga gurin nan.
Nata ce mata tazo ta gani ai taki ne, kuma kinga ko Safna bazata had’o da ita ba.
Gaskiya ya kamata tazo taga gurin yayi kyau, kuma tsarin yayi, aini na dauka hade gurin akayi gaba daya.
A’a amma ga kofa can da zata kaini falo na, muje Yadikko.
Tahowa sukayi ya bube kofar inda Babban falon sa ya bayyana, Zama Yadiko tayi daga daya daga cikin kujerun falon tace, a yayi sosai, wata kofar ya sake nuna mata yana fadin kinga waccen kofar itace zata Kai mutum falon Safna.
Yaba gurin ya dikko ta sake yi sannan ta fito ta kofar falon Modibo Yana biye da ita abaya yayin da Yadikko ke fadin, ” Toh ai shima can din tunda an gama gyara yakamata a kawo kayan Rahma ko akwai abun da za’yi ne kuma?
A’a Yadikko aini ku nake jira, Ina bin Ammi a hankali ne, Dan naga kamar bata son bani yariyar.
Zan mata Mgn tunda ankai na Safna yau, har bakin motar ya rakata ta shiga sannan sukayi Sallama ya koma ciki.
Wannan karon ta kofar Safna yabi, Yana turo kofar yaji sheshshekar kukan ta, shiga yayi yana me kallon ta sosai take kuka, Zama yayi ya daura kafarsa daya kan daya tare da binta da kallo ganin yadda take kuka.
Tsayon lakaci ya dauka yana kallon ta sannan yace, ” me ya faru?”
Ai kana kallo agaban ka yariyar Nan ta wulakanta ni, bakace bata komai ba.
Lallai Safna, ya fad’a idon sa akan ta, waton bance komai ba?, ai inace idan akwai wadda zaice bance komai ba toh Rahma ce, ke ai abun da ranki ke so kika yi.
Amman kana kallo fa wannan ‘yar yariyar tasa hannun ta hankade ni sannan dan Bata da kunya har tana daga hannu zata mare ni, wlh da ta sake ta mareni saina nuna mata ita rorarriya ce.
Jin jina kansa yayi sannan yace, da nazo ne in rama mata marin da Kika mata, amman ganin da nayi kina kukama ya wadar tar, saidai ina son ki aje wannan acikin ranki, daga yau karki sake daukan hannun ki ki kaishi jikin ta, yadda kike da muhimmanci agurina itama haka take shi.
Bangaje ni fa tayi.
Ko me tamiki ki gaya min, idan kuma ni bazan miki yada kike so ba ki gayawa Ammi, barema ni ban yadda ta bangaje ki ba.
Uhum lailai ma kana goyon bayan tane, da fa Marina zata yi, ganin ka ne ta fasa.
Eh nagani, kuma naji dadi da taga mutuncina ta fasa din, amman ke kin nuna min banda mutunci a idon ki, tunda har Kika mareta gabana, duk da tsawa dasu Ammi ke miki, ‘yar karamar yariya rafiki hankali?, kina kallo fita taso yi amman data ganni agurin saita koma, ke ko sai Kika tunkaroni cikin fushi Kamar zaki angaje ni, naso dakin gogi jikina wlh saidai a kwashe ki agurin.
Cikin Mamaki take kallon Modibo tsayon lokaci ta dauka sannan ta girgiza kamta tare da had’eye wani abu me zafi.
Sannan kuma naji kina ce mata rorarriya, kin taba ganin an roro mutum??
Shiru tayi.
Tambayan ki nake ki bani amsa”
a’a, ta fada ahankali.
Toh karki kara, babu wadda ake rorowa, hanyar daya ce, itace aure, yadda aka Samar dake haka aka Samar da ita, idan kin kama kanki basai ance mata ta mutuntaki ba, idan kika watsar da kanki kuma ko ance mata ta mutuntaki tun tanayi wata rana dole zata band’are, so gwara ki kama kanki.
Hawaye kawai Safna ke sharewa tana kallon Modibo ya mike ya fita yayin da zuciya tacigaba da kuna.
****
Wai ke Unaisa menene haka? me aka miki?
Ba komai.
Ai nasan amiki wani abu tun da naga kina shigowa kikai amai, akwai mennene dan Allah?
Safna ce ta mare ni.
Zaro Ido Afnan tayi tare da fadin, mari?, kika tsaya?
Akwai su Ammi da Yadikko ne agurin shima yana tsaye.
Tab d’i aini in nice bazan Bari ta sauke hannun ta batare dana daura mata mari ba.
Abun dake damuna kenan Afnan dana rama bazanji haushi ba, kuma fa bece mata komai ba, Unaisa ta fad’a yayin datai saurin sa hannun ta ta share hawayen ta.
Zaice mata, na tabbatar sai ya mata fad’a.
Bawani nan.
Wlh garkiga laifin shi.
Hawaye Unaisa ta sake sharewa sannan ta mike taje ta wanko kuskan ta.
Washegari da Safe Safna kwance gefen Modibo, ahankali ya matsa daf ta ita tare da rungumota jikin shi Yana fadin, kina bacci ne?
Ido na biyu ta fada a hankali.
Lumshe Ido yayi jin dumin jikinta anashi, duk da cewa baya ta bashi.
Akwai mgnr da nakeson nai dake.
Toh inajin ka.
Kinsan komai yana da lokaci, tuni Mai martaba yake son nakara aure amman hakan be yiyu ba.
Gabanta taji ya fadi sosai dan haka duk ta bude kunnen ta.
Cigaba yayi da cewa, na dauki hakan a matsayin Allah ne be nufa ba, duk da cewa wasu na surutai akai, komai lokaci ne, Safna ?
na’am
Rahma zata tare ranar auren Afnan.
Zaburi Safna ta ture hannun Modibo ta tashi zaune, juyowa tayi ta kalle shi tana fadin, Hamma Modibo?, shine sai ana saura kwana 4 zaka gaya min?
Tashi yayi ya kishigila Yana fadin, naga ba sabon aure bane, abu ne wadda kikasan dashi kowa ma yasan dashi, tarewa ne kawai.
Kuka Safna tafara cikin kukan take fadin, ” shiyasa ashe har take iya daga hannun zata bigeni, sabo da taganin takai matsayin da zata kwanta da Mijina , toh ni ka sake ni sai ka zauna da ita ita daya.
In sake ki?
Eh ka sake ni
Sabo dame?
Sabo da ban yadda da wannan cin amanar ba, bazan zauna da ita wannan wawiyar banziya kazama ba, in bandama wulakanci da cin mutunci ta Yaya zaka bude baki kace min zaka tare da ita, ban yadda ba kaje ka nemo sabon aure.
Inje in nemo Sabo aure?, kina da hankali kuwa Safna?, matatace fa zata tare, toh ita nata auren me kike nufi dashi, kuma da kike cewa baki yadda da auren cin Amana ba wanni amanar aka ci miki?
Wlh wlh bazan yadda ba saidai ka sakeni ka zauna da ita.
Yadda ta rufe idon ta yake kallo sannan yace, Safna kizo ki zauna muyi mgn, haba menene haka, ki kwantar da gankali.
Cikin kuka tace banda sauran kwanciyar hankali, idan zaka hadani da yariyar, wlh natsane ta Kamar yadda na tsana mutuwata banson ta ban kaunarta.
Cikin tsawa yace, Safna wai meye kike yi haka?, aure nawa nazo miki da labarin su, Baki tabamin haka ba sai akan wannan da kin riga kinsan da auren, tarewa ce kawai fah.
Dole kace min kawai tun da da alama kana sonta, daman tun jiya nake mamakin ka, yanzun ka zafi wacce make so koni ko ita.
Kansa ya shafa sannan yace, zoki zauna.
Ni bazan zauna ba.
Kizo ki zauna nace zan mareki fa.
Cikin da fushi tazo ta zauna tare da juya mashi baya.
Juyo ki kalle ni.
Ahankali ta juyo suna fuskanta juna.
Kallon ta yayi sama da kasa sannan ya kama hannun Safna duk biyu tare da fadin, Safna banson rigima, banta tunanin zakiyi haka ba, amman duk da haka na miki uzuri, kishi ba karya bane, dan Allah kibi komai a hankali…..
Ni Hamma Bazan iya ba, indai wannan yariyar ce saidai ka zaba daya.
In zabi me?, Ina son ki, itama ina sonta, uwata ce ke da zaki tasani in zabi daya, karfa kiga ina lallabaki ki kawo min iskanci.
Kana son ta kake cemin?
Kallon ta yayi sama da kasa sannan yace, ” Eh Ina son ta, zaki dake ni ne?
Jifa ta fara Kai masa da duk wani abun da yazo hannun ta ganin abun nata bana hankali bane ya mike ya isa gabanta, mari yakai mata mekyau wadda yasata dawo cikin hankalin ta da kallo ta bishi tana rike da kumatun ta.
Afusace yake Yana huci sosai yake fadin, fita min agida.
Bazan fita ba saika bani takarda ta.
Ashe kuwa zan miki duka, kifita nace banson ganin ki.
Yadda yai mgnr cikin buga tsayawa yasa ta zabura, wannan ne karo na farko da irin hakan ya faru a tsakanin su, dakin ta ta nufa a fusace ta dauki mayafin ta ta fice tana tafe ta kuka tare da Kiran Momy.
Modibo ko bakin gadon ya koma ya zauna tare da dafe kanshi, tunda take zuwa mata da labarin aure Bata taba nuna tashin hankalin ta irin wannan ba.
*****
Washegari da misalin karfe 8 Unaisa da Afnan suka shigo dakin Ammi cikin shirin su na zuwa lalle, akan gadon Ammi ta hangi Safna idon ta duk ya kunbura da alama anan ta kwana.
Gaida Ammi sukayi sannan suka mata Sallama suka fito alokacin Safna waya take.
lallai sukaje can suka wuni sai yamma suka dawo ita da Afnan da yaran mijin Yadikko guda biyu, iri daya aka masu ita da Afnan sosai sukai kyau, misalin 5 na yamma suka dawo, tun a harabar gidan suka gane baki sun fara zuwa farin ciki ne ya lullubeta alokacin data shiga dakin Ammi ta hango Dada, har yanzun Safna na kwance a gadon Ammi .
Jikin Dada ta fada sai a yanzun da kula da matan malam ayuba da suke zaune gefen Dada, kwance take ajin Dada taje wata mata na fadin Masha amaren sun dawo kenan.
Runtse Ido Unaisa tayi, aranta take fadin Amarya dai.
Wata mata ce ta taso daga mazaunin ta ta raho tana leken fuskan Unaisa, Masha Allah matar ta fada Ina me daura idon ta afuskan Unaisa tana fadin, wannan ce amaryan Modibo na?
8 comments