IMG 20211225 WA0024

Furucinovel ya samu bakuncin Sadnaf

Posted by

Furucinovel ya samu bakuncin Sadnaf

 

Furucinovel ya samu bakuncin shahararriyar marubuciyar nan Nafisa Nuhu Wadda akafi Sani da Sadnaf.

Sadnaf tace, “ta samu kalubalai a rubutun Labarin ta na farko, me suna LALATA, inda aka yankewa labarin hukunci da Sunan Littafin batare da an bibiyi labarin ba, duk da cewa labari ne da yake dauke da wani Muhimmin darasi”

Ga ta bakin Marubuciyar Nafisa Nuhu wato Sadnaf

T1. Da farko zamuso miji takaitaccen tarihin ki.

Sadnaf: Sunana Nafisa Nuhu wadda akafi Sani da Sadnaf, Ni Yar garin Kano ce, agarin Kano nayi primary secondary har da higher institution, Ina da Aure da Yara uku.

T2. Awacce shekara Kika fara rubutu.

Sadnaf: Na fara rubutu a 2017.

T3 Zamu so muji abin da yaja hankalin ki kika fara rubutu.

Sadnaf: Tun Ina karama Ina da san karance karance, ko wane irine, daga haka na taso da son nayi rubutu, nakan rubuta shirme indai nayi Shiru zanji labarai nata zuwar min kwakwalwata, ahaka har na fara rubutun.

T4 Masha Allah, zuwa yanzun Littafan da kika rubuta sunkai nawa.

Sadnaf: Na rubuta litattafai sun Kai Sha takwas.

T5 Zamu so muji sunayen su daga bakin ki.

Sadnaf: Lalata
Rashin hakuri
Barauniyar amarya
Daga taimako
A sanadin group
Yatsunmu ba daya ba
Mak’otan juna
Kukan kurciya
Bakin dare
Zamani
Rana zafi Inuwa k’unna
HUDAH
Karambani
Naga ta kaina
Sabon salon yaudara
Illar aminci
Laifi tudune.

T6 Masha Allah, kin taba saida littafi.

Sadnaf: Eee na siyar da yawa ma

T7. kina da Kungiya koko kina rubutu ne kawai batare da kina cikin wata Kungiya ta marubuta ba.

Sadnaf: A’a Ina da kungiya, inacikin memba na Kungiyar EXQUISITE WRITERS FORUM.

T8 Da kyau, Acikin littafin ki da kika rubuta wanne yafi kwanciya miki arai.

Sadnaf: A cikin litattafan da na rubuta Ina San Daga taimako.

T9 To amman wanne masoyan ki sukafi ihu akan sa.

Sadnaf: Daga taimako da Naga ta kaina.

T10. Tunda Kika fara rubutu wanni kalubalai Kika fuskanta.

Sadnaf: Na fuskanci kalubale a rubuta labarina na farko wato lalata, inda yawanci a lokacin basu ma karanta labarin ba ballantana su san me yake d’auke dashi,sunan novel din kawai yasa suka yanke hukunci labarin batsa ne, a duk novels Dina nafi fuskantar challenges da nake rubutawa.

T11. Daga karshe wanni Kira Zakiyi ga ‘yan uwanki marubu ta.

Sadnaf: Toh Kiran da zan yiwa Yan uwana marubuta shine su ringa hakuri da makaranta su kuma ringa sanin irin labarin da zasu rubuta.

Toh Hajiya Sadnaf mungode, furucinovel suna miki fatan alheri tare da fatan nasara a rayuwa.

 

Tambayoyi da gabatarwa: Fadeela Lamido.

 

 

4 comments

  1. Pingback: สล็oต PG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *