
BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido
EXQUISITE WRITER’S FORUM.
Page 30
Cikin sauri Unaisa ta dago suka had’a ido, sai dai Bata da kwari ko muryan Bata amsa, domin kuwa muryan ta a shake yake, sannan jinta kawai take gata Nan ne dai, dan haka ta maida idon ta kasa.
Ke! raina min hankali zakiyi ne?, Safna ta sake fada afusace.
Batare da Unaisa ta dago ba tace, “ba sunana ke ba”
Okey, Ashe ba sunan ki ke ba?, yaya sunan naki yake to?
‘Dagowa Unaisa ta sake yi ta kalli safnan sannan ta sake maida idon ta kasa tana fadin, ” ki tambayi mijin ki”
Lallai ma yariyar nan baki da kunya, na kula a fe’ke kika zo, toh bari kiji ki dawo da hankalin ki jikin ki, idan ba haka kuma ni zan miki saiti.
Wannan karon Unaisa batace komai ba, wasa tacigaba dayi da hannun ta hakan ya kara fusata Safna, domin ta tsana a tana mgn amata banza, kuma tasan tanajin ta Sarai.
Kallon tsana tai tabin Unaisa dashi, zuwa can tace idan kinajin yunwa kici abincin, idan kuma bakici saiki bari, domin wadda kike ma shagwabar baya nan, ni kuma ba baiwar gidan ku bace.
Lumshe Ido Unaisa tayi tana sauraron Safna, son tashi take agurin saidai kuma tana gudun kada ya dawo ransa ya bacci dan haka taci gaba da zama.
Itako Safna aduk lokacin data kalli Unaisa ranta baci yake yi, dan haka taita Jan tsaki zuwa can tace, “wai ni nake mgn kika yi kunnen uwar shegu Dani, dama fa dan kauye be iya samun waje ba, idan yaga waje sai yace zai baza shanya, toh ni babu wulakantacciyar da zatazo ta fitine ni.
‘Dagowa Unaisa ta sake yi ta kalli Safna, sosai kalamin ta ke mata zafi cikin zuciya, ko muryan Safna bason jinta take ba, kawai dai tana daurewa ne.
Itama Safna Kara fusata take sabo da yadda Unaisa tai tsit, dan haka tasa hannun ta kara ta hankada abincin dake gaban Unaisa, Kan cinyan ta ya bare, yayin da Unaisa tai saurin tarewa tare da mike wa tsaye tana kalllon Safna da ke zafga mata harara.
Wani bakin ciki ne ya ciwota, dan haka ta Kara matsa ta dauki abinncin da Modibo ya bari ta jefi Safna dashi sannan taja tsaki ta wuce.
Mikewa Safna tayi bakin ta abude tana bin bayan Unaisa da kallo, bayan ta wuce ta maida hankalin ta kan gurin da kakayo barin abincin, kaca kaca ta gani, komai ya watse, jikinta ta kalla duk ya baci, dan haka ta kuma maida hankalin ta ga ahanyar da Unaisa tabi, tuni idon ta ya tara kwalla, afusace ta nufi kofar da zata sadata da Part din Unaisa, tana tura kofar a cikin tsananin fushi da baccin rai, falon Unaisa ne ya bayya harta Kai tsakiya taja ta tsaya, cikin yanayin dake nuna ta shiga tunani, acikin ranta take fadin, ” idan kuma Hamma Modibo ya dawo ranshi zai bacci, zaicimun mutunci, cikin sauri ta dafe kirjin ta tare fita da sauri dan kada ya sameta a awajen, gurin da suka yi barin abincin ta shiga gyarawa tanayi tana kallon kofar, Saida tagama tass sannan ta wuce part dinta tana maida hawaye, gaba daya rasa me zatayi tayi, dan haka kawai ta dauki wayar ta ta danna tare da karata a kunnen ta.
Tsayon Lokaci Momy take sauraron kukan da Safna take rairawa, Bata hanata ba, domin tasan kishiya akwai zafi, zuwa can tace ya isa, menene ya faruwa?
Tsagaitawa tayi da kukanta tare da fadin, Momy yariyar bata da kunya, idon ta atsaitsaye yake, sannan abun da yafi tayar min da hankali bakiga yadda Modibo ke tarairayarta ba, Momy kamar bashi ba.
Safna kema kina da matsala Ashe?, nace miki kisa ranki a inuwa zanyi maganin abun, menene kuma zaki dinga koke koke, ai irin wannan sai kisa a zargeki, da kina da hankali dasai ki nuna ma Modibo kin fishi son ta, da ace Zaki iya da komenene Modibo zaiyi mata saiya nemi shawaran ki.
Bazan iya ba Momy, banson ta natsane ta me kautanarta ma ni ban son shi.
Toh naji Safna, idan bazaki iya wannan ba, saiki kama kanki, karki yadda wani ma ya hango kinta da kikiyi, tunda babu abun da ta tare miki, kinga Safna idan baki nutsu ba zan cire hannu na akanki,
Toh Momy amman fa yau naso namata duka wlh.
Zaro idon Momy tayi tare da fadin, ” kina hauka ne? ai sai asaki agidan radio, kwananta biyu agidan miji uwar gida ta mata duka, karki soma, wlh mijin ki kinfi kowa sanin halin sa, a tsaye yake, wlh Modibo ba mutunci garai ba zai iya sakin ki Safna, Allah yasa dai baki tabata ba?
Ajiyan zuciya tayi sannan tace bantaba ta ba Momy, amman Raina ya ya baci nayi sututai.
Karki kara, ki nunawa Modibo kin fishi son a zauna lafiya, idan kikayi haka nikuma zakiga abun da zanyi, da kanta zata tattara kayanta ta koma inda ta fito idan kuma tace ita ‘yar me naci ce sai mu zuba.
Ajiyan zuciya Safna ta sake yi akaro na biyu sannan ta tace nagode Momy, har naji sanyi ni yanzun bani da buri illah inga auren Nan ya mutu.
****
Unaisa ce ta fito wanka ranta bace, gaba daya komai baya mata dadi, ga jikinta dake cewo sosai, ga tarin haushin Safna, tursasa zuciyarta taitayi, dan kada Modibo yaga tama matarshi rashin kunya, batasan me yasa komai idan ya kasan ce daga gurin Modibo yake duk kinta da abun bata iya wulakanta shi, da ta dago Ido da nufin bama Safna amsa saita tuna kar Modibo yaga ta mishi badaidai ba, amman badan tana tsoron Safna bane ta barta, asalima tana tsananin jin kishin Safna akarkashin zuciyar ta, sosai takeyiwa kanta fada akan zafin da take mata aduk lokacin da taji Modibo ya kira Koda sunan Safna ne, ba ason ranta take jin zafin ba.
Kwanciya tayi batare da tanajin Dadin kwanciyar ba, tana cikin wannan halin Kiran Ammi ya shigo wayar ta dauka tayi ta gaidata.
Cikin tsananin tausaya mata ta amsa domin taji yanayin muryan ta kamar na me mura, jimmm tayi tana tuna Kamar haka taji muryan Afnan jiya, yau kuma ta Unaisa, cikin dan daburcewa tace shikenan sai ajima, zamuyi mgn amjima kinji.
Da toh kawai Unaisa ta iya amsawa tare da lumshe idonta, karfe 11 har yanzun bata sa komai a cikin ta ba.
*****
Yanzun meye ke damun ka?, Modibo ya tambaya yana tsare Magaji da idon sa.
Naji dadi, kawai yanzun bacci nake ji.
Abba ne yace maganin da kasha ne, saika je ka kwanta, mikewa Magaji yayi yayin da Muftahu ya rike shi suka fita.
Abba ko kallon sa ya mayar kan Modibo yace, “Amasallaci fah ya fadi, Ashe ya kwana beyi bacci ba, wai ya kwana da ciwon kai, meke damun yaron Nan ne?, bana yadda dashi Modibo, kasa mishi Ido da kyau kada abun da ya faru abaya ya sake faruwa yanzun.
Abba zan kula, insha Allahu ma ba haka bane, ai yanzun ya canza.
Nadaice maka kasa Ido sosai akanshi.
Amsawa Modibon yayi kawai da toh domin ya fahimci akwai damuwa akan fuskan Abba.
*****
Zazzabi ne me zafi ya sake rufe Unaisa wadda ya haifar mata da rawan sanyi, rufa tayi gaba daya gabar jikin ta ciwo take mata, zuwa can taji amai na taso mata dan haka ta tashi a rikece tayi bayi, sau uku tayi amai sannan ta dawo ta kwanta, wayarta ta dauka tsintan kanta tayi da Kiran Yadikko.
Yadikko suna zaune ita da Suraj taga kiran Unaisa, tashi tayi zaune cikin sauri ta dauka dan haka Suraj ya bita da Ido.
Shashakar kuka take yi sosai dan haka Yadikko tace, “Rahma?, lafiya meya faru?
Yadikko dan Allah kizo.
Inzo in miki me Rahma meke faruwa?
Yaddiko ni banni da lafiya zazzabi nake yi
Yadikko bani da lafiya narasa inda zan saka kaina.
Wani irin numfashi ta sauke wadda yasa Suraj mikewa da sauri, domin indai tayi irin wannan alama ne na ciwon zuciyarta nason tashi.
Cikin haki take fadin, ” kinrasa inda zakisa kanki kuma Rahma?, Ina Modibon yake?
Bayanan tun safe ya fita, nata amai Yadikko ga zazza, ni bani da lafiya kizo ki tafi dani.
Inzo inje dake Ina?, barin Kira mijin ki, ya zaifita tun safe be waiwaye ki ba…..
Yadikko karki kirashi, yau ya koma dakin Matar shi ai kwanana biyu da zuwa.
Jimmm Yadikko tayi ta alama akwai surutun zazzabi ajikin Rahma Tafad’a cikin zuciyarta, mikewa tayi da wayar a hannun ta tana fadin Ina zuwa gani Nan zuwa.
Wayar Suraj ya karba daga hannun Yadikko yasa a kunnen sa yana fadin,” ke meye?
Shiru tayi jin muryan Suraj ta kasa cewa komai.
Me kike so ? ya sake fada cikin daka tsayawa.
Yadikko tazo.
Bazata zo ba, bakisan Bata da lafiya bane Zaki dinga kiranta kina d’aga mata hankali, saboda shagaba ta mike yawa, idan Modibo baya nan Ina muta nen dake cikin gidan, shi Modibon bashi da waya ne ki kirashi Mana, idan kika sake Kiran layin nan saina miki wulakanci wlh tallahi, katse kiran yayi tare da kashe kawar gaba daya, gefen Yadikko ya aje wayar sannan ya fice a fusace.
Bayan ya fito harabar gidan su ajiyan zuciya yaita maidawa, bayan ya nutsu ya Kira Modibo Yana dagawa yace kana inane yanzun?
Ina gida yanzun muka dawo da Magaji daga Asibiti beji dadi ba.
Kashiga part din ka ne?
Yanzun dai zan isa.
Toh saika hanzarta, Amaryan ka bata da lafiya, kuma ka gargadeta karta sake Kiran mama tana d’aga mata hankali.
Dallah gafara Malam….
Katse Kiran yayi batare da yaji me Modibon zai fada ba, takawa ya fara yi, domin komawa gurin Yadikko.
Modibo ko cikin gudu gudu ya shiga gidan, burin shi kawai yaga awanni hali Unaisa take ciki……
6 comments