Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 31

Posted by

BA LABARI BOOK

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 31

Da Saurin sa ya shiga part din Unaisa abakin kofar ya dan gyara wuyan rigar sa sannan ya shiga ciki.

Shashakar kukanta ya fara jiyowa dan haka ya karasa gaban gadon yana me kallon yadda ta cure guri daya tana kuka.

Cikin sauri ya hau gadon sannan ya daga bargon ya zauna agefe tare da dagota ya daura jikin sa yana fadin baki da lafiya haka meyasa baki kirani ba, haba Unaiss.

Kokarin komawa gadon take tare da ture shi, shiko kara riketa yake ajikin shi yana fadin, tsaya mana menene haka?

Ganin ba yadda zatayi ne ta kwanta kawai, domin kara wahalar da kanta take yi.

Kansa yake mannawa a wuyanta tare da fadin, Sannu ko, kinci abincin rana?

Bata iya bashi amsa ba, dan haka yaci gaba da shafa jikin ta tare da manna kansa a wuyan ta, rasa ta ina zai fara yayi domin be saba yin jinyan mace irin haka ba, kusan ace wannan ne karon farko da yake jinya da kansa, Ya wance Safna saidai ta tashi da Dan ciwon kai ko zazzabi wadda dakanta take cewa akaita asibiti, dan haka abun yazo masa a bako.

Afili ya fara fadin, me zanyi ne, ko asibiti zan kaiki, Anya ma kuwa kinci abincin?

Kanta ta d’aga alamar eh.

Jimmm yayi zuwa can ya daga waya ya kira Ammi, kamar jira take ta dauko tana fadin, ” Modibo kun dawo ne yame jikin.

Alhamdulillah Ammi mun dawo tun dazon, naso in shigo Amman sai Suraj yamin waya Wai ‘yarki babu lafiya.

Wacce ‘yar kenan?, Ammi ta tambaya.

Rahma, Modibo ya fada ahankali.

Allah sarki, shi Suraj din Ina yaji.

Ina tunanin tayi waya da Yadikko ne.

Cikin sanyin jiki sosai Ammi tace Allah sarki bani ita.

Wayar ya karawa Unaisa yana fadin ga Ammi.

Kasa cewa komai tayi, daga can cikin wayar taji Ammi na fadin, Zazzabin ne ko aman ne Rahma?

Murya kasa kasa tace duka ne Ammi.

Toh Sannu, yanzun nan zan turo Dr Halima tazo ta dubaki, kin ci abin dai ko?

A’a

A’a ? rabon ki da abinci tun yaushe ?

Jiya da dare Ammi.

A’a, ikon Allah, toh shikenan zan Aiko miki da Abinci.

Wayar ta mika masa yasa akunne, jinsa tayi yana fadin, ” Da safe muna kokarin karyawa ne Abba ya sanar dani Magaji babu lafiya, kuma tunda na fita Ammi sai yanzun na dawo.

A’a ban Kira ba, ya sake fada cikin wayar, jimmm, yayi, zuwa can ya sake cewa, toh zan kitaye Ammi.

Sauke wayar yayi, sannan ya kalli Unaisa ya lumshe idon sa, bayan kusan minti talatin Dr Halima ta iso, har cikin dakin Modibo ya shigo da ita, yana tsaye daga bakin gadon yake nunawa Dr Halima Unaisa.

Gaisawa sukayi da Unaisa sannan ta Mika hannun ta ta taba jikin ta tana fadin, meke damun ki.

Zazzabi ta fad’a a hankali, Muryan Modibo taji yace, Dr harda Amai.

Idon Unaisa ta kalla tare da fadin, inace Amarya ce ?

Shima Modibo Yana kallon Rahma data sunkuyar dakai yace Eh amarya ce.

Kwanan ta nawa kenan, ko mun samu karuwa ne??

Murmushi Modibo yayi tare da shafa kansa Yana fadin, “babu wani karuwa Dr , ita wannan dabi’ar tace Zazzabi da Amai, da hankalin ta ya d’an tashi saita yi.

Kallon Unaisa Dr Halima tayi tayi murmushi sannan ta Kara taba jikin ta tana fadin, kwanan nawa ne yau?

Kwana biyu fa.

Dariya Dr Halima ta sake yi tare da fadin, lallai akwai aiki, rubuce rubuce tayi a takarda sannan tace toh zan mata Allura biyu yanzun…

Batakai ga Rufe baki ba Unaisa tace aban magani ne.

Kina tsoron Alura ne?

Ni ba’a min Allahura ne kwata kwata.

Ana mata Dr, barin baku waje maganin ma sai an yi fama take sha.

Ficewa yayi ya koma falon ya zauna, tsayon lokaci Sannan Dr Halima ta fito, takardan data rubuta magani ta mikawa Modibo, tana fadin, tace bataci abinci ba dan haka banyi allurar ba, a sawo mata wannan maganin zuwa gobe sai muyi waya inji yadda jikin yake.

Amsawa yayi da toh, saidai acikin ransa bayajin Dadin Abun da Unaisar ke yi, shi bazata gaya mishi bataci abinci ba saidai ta dinga gaya ma wasu.

Fita yayi ya sawo Maganin sannan ya dawo, ya samu Ammi ta Aiko mata da abinci tana ci, dan haka ya koma gefe ya zauna yana kallon ta.

Yi yayi kamar baya kallon ta harta gama, saidai ba wani sosai taci ba, tsakura kawai tayi, maganin ya Mika mata, nan ma komawa yayi gefe Yana cigaba da kallon ta ta gefen idonta harta gama sha.

Gyra gurin yayi sannan ya kwashe kayan, yayin data koma gadon ta kwan ta.

Ganin haka Modibo ya koma dakin sa, wanka yayi ya shirya, sannan ya Kira Safna a waya, cikin ganganin lakaci tazo, yana ganin ta yasan akwai abun dake damun ta, batare daya kalleta ba yace meke damun ki?

Ba komai.

Gefen gadon ya nuna mata kusa dashi sannan yace zoki zauna.

A’a

Ban gane a’a ba, Ina ce miki ki zauna kina cemin a’a?

Cikin kawar da Fuska tace ai naga wannan duk cikin lokacin Amarya ne.

Cikin Ido ya kalle ta, sannan yace, ” eh amman kuma kema kina da hakkin in gaida ki insan halin da kike ciki.

In wannan ne ai Part d’ina ya dace kazo, ni da naga haka ma na dauka haka kuka tsara.

‘Dagowa yayi ya kalleta cikin Ido, tare da fadin, “ni da wa?”

Kai da Amaryan.

Kizo ki zauna nace ko?

Nifa bazan zauna ba, ai ita har d’akin ta kake bin ta, ni ko baka kwana a dakina saidai na biyo ka.

Okey, kema yanzun kin daina kwana nan kenan?

Eh.

Safna, rigima kikeji kuma?, ko abun ne ya motsa?

Ni ba komai Hamma Modibo, kawai kowacce ta tsaya a part din ta, Kai ka dinga zuwa yafi.

Bazai yiwu ba Safna, kizo ki zauna muyi mgn.

Ni bazan zauna ba….

Batakai ga rufe baki ba ya daka mata wata muguwar tsawa, dan haka ba shiri ta zauna din Kamar yadda ya bukata.

Kallon ta ya cigaba dayi fuskan shi cike da fushi, sannan ya fara fadin, ” zaku hana min kwanciyar hankali ne?, wacen tace kaza, wancen tace kaza, nifa bazan dauki iskanci ba, Ina miki mgn kina min taurin kai, akwai alamar har yanzun baki sannin ba, fada yai tayi yayin da Safna ta fara kuka.

Sai da yayi me isakar sa Nan yai shiru, tsayon lokaci sannan ya juya ya kalli Safna yace, “meke damun ki??”

Bakomai, ta fada ahankali.

Akwai.

Wasa ta shigayi da hannun cikin yanayin fushi.

Safna kishi ne ko?

Cikin sauri ta juya masa baya.

Kijuyo mana muyi mgn, d’an adam ne ni tara bai cika goma ba, idan kinga akwai rashin adalci ki futo ki gaya min kan hakkin ki da kikaga na danne miki, amman bana son nai mgn amin shiru.

Batare data jiyo ba tace, Amma ai ita tana yin shirun ai ko.

Sunkuyar da kansa yayi yai murmushi sannan ya dago Yana fadin, “ita wannan dabi’ar tace, haka take, yanzun ma ai tana mgn. su Magaji sune shaida.

Jimmm tayi sannan tace, toh ita me yasa kake binta har daki kuma har ka kwana acan?

Sabo da nasan konace tazo bazatazo bane shiyasa.

Kenan ni ballagaza ce da nake zuwa?

A’a, bance ba, ke Kika fad’a.

Hakane Mana, Nima bazan kara zuwa ba….

Be bari ta karasa ba yace, “ki daina gaya min abin da kika dama Safna, bazai yiyu ba abun da kike fada.

Kawar da kanta tayi ta share hawaye adaidai lokacin da Modibo ke fadin, ” nasan kina da kishi amman ban dauka kwana biyu da yariyar nan tayi acikin gidan na har Zaki tada rigima haka ba, kuma da safe ba haka kike ba kila dai akwai waddan suke zuga ki ne.

Ni babu me zugani Hamma, kawai dai naga ita baka iya mata fad’a ne Kamar kana nuna tafi karfin ka.

Bata fi karfina ba Safna, kawai idon ki ya rufe ne, na lura abun yai miki ciwo shikenan, mubar mgnr, daga yau zamu gyara, ko ba shikenan ba?

Kawar dakai tayi can gefe, kallon ta yayi, duk yanayin ta ya canza ya riga yasan kishine kawai ke damun ta yanzun ko daidain akayi bazata ganshi a daidai ba

Hira yadan taba da ita kadan, Saida ya tabbatar da ta saki jikinta sannan ya koma gurin Unaisa.

Bacci take gaba daya ta jike da zufa, kuma da Alama tana Jin dadin baccin.

Hannun sa yasa ya yaye mayafin sannan ya kwaanta ta bayanta tare da jawota jikin shi ya rungume.

Tunda ya fara yaye mayafin ta tashi saidai Bata bude Ido ba.

Kwance take akirjin shi yayin da kamshin sa ya hado da nata, abun take ganin ya mata banbara kwai dan haka tama kasa cewa komai, Wai Modibo meji da tsare gida tare da kama mutuncin sa shine ya bari har ya bude mata tsaraicin sa, Kara tura kanta tayi cikin kirjin shi, ji tayi Kamar ta shige rami sabo da kunyan abun da tagani daren jiya nashi.

Yadda take tura kanta kirjin shi ya tabbatar Masa data tashi, ya san kunya ne yake sakata, sosai yadda take nuna jin kunyan shi hakan ke bashi nishidi fari kal yake jin zuciyar sa.

Shafa lallausan gashin kanta ya shiga yi, yana fadin, ” Allah yasa baki fushi ba Unaiss, na tafi na barki tun safe gashi baki da lafiya, Magaji ne bashi da lafiya, kuma bansan cewa jikin naki yayi zafi haka ba, meyasa baki kirani ba ki gaya min halin da kike ciki.

Jinta shiru ya sake fadin, ” Maganin zugi, nace ko kinyi fushi ne?”

Shiru ta sakeyi sai dai ko dataji ya kirata da maganin zugi saida ta lumshe ido, wadda ta rasa dalilin ta nayin hakan.

Har yanzun Yana shafa kanta yace, “idan kinyi fushi ki yafe ni, dan nasan fushin ki na angayu ne, idan ranmu ya ‘baci kawai sai mu yi amai abun mu, idan kuma an bamu haushi sai jiki ya d’au wuta Kamar zafin rana, koba haka bane, uhum, maganin zugi ?

Yadda yai mgnr yasa tayin murmushi batare da ta shirya ba har ya bada sauti wadda sai bayan fitarsa ta shaida abun da tayi, har ciki ransa yaji sanyi dan haja ya saki ajiyan zuciya.

Agida ya wuni be sake fita ba, saidai yaje masallaci ya dawo, ganin anyi sallah, mangariba ya fara son ya shigo mata da mgnr zuwa dakin sa, tsintan kansa yayi da rasa ta inda za’ayi ya gaya mata, Yana cikin shirya yadda zai billo mata, Suraj ya kira Modibo, da saurin sa ya dauka dan daman jire yake dashi, saidai Yana dagawa Suraj din yace, ” gamu a falon ka da Mama, ta matsamin da daddaren nan Saida na kawo ta……

7 comments

  1. Pingback: ยางยอย
  2. Pingback: winomania
  3. Pingback: situs toto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *