IMG 20211226 WA0054

BAYA BA ZANI BOOK 2 PAGE 1 to 3

Posted by

BAYA BA ZANI BOOK 2 PAGE 1 to 3

 

BAYA BA ZANI🥥🥥🥥🥥🥥🥥
Book 2

By
Fadeela Lamido

Wattpad fadilalamido

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*® _PEN: WRITER’S ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

1-3

 

Abdullahi ya ture daga garesa, ya ware idanun sa waje”

Shikuwa Abdullahi tuni ya sandare waje daya cak idon suka makale”

Abokan Umar ne suka fara murna, yayin da cikin fara’a suke bashi hannu, tunanin su ya shammace su ne amsan hannun nasu kawai yayi, yayin da idonsa ke canza launi zuwa jah”

Abdullahi kuwa lokacin daya dawo hayyacin sa daker ya iya lalabu motar da yazo cikinta ya fada”

Ganin haka abokanshi suka rufa masa baya sukabar wujen”

Dattijo kuwa kallon kowa yake daidai ranan nan nasa hade zuwa can yaji karfin jikinsa kamar walkiya yabar wajen”

Jiyake kamar karya koma gidan sai dai yanason ya Kara tabbatar da abun da kunnensa ya jiya masa”

Sakkowa kawai yayi cikin motar batare daya rufe murfin ba yai cikin gida kansa asama kamar wani zaki baya duba gaban shi”

Toh fah innalillahi wa inna ilaihir raju’un Mama data hango shigowa Dattijo ta fada”

Itako Umma cikin sauri ta taho tana fadin Kai Kai kalli gaban ka karka takawa mutane Yara”

Kafin ta rufe baki tuni ya shige dakinsa, Dan bayajin zai iya mgn wannan lokacin”

Can cikin dakinsa ya shiga tare da fadawa kan godu shikadai yasan abun da yake ji”

Mama ce tai saurin bisa dakin har ciki ta bishi ganinsa rufada ciki yasa tai turus lallai me afkuwa ta afku”

Kai! Dattijo Yaya akayi?

Dattijo bakajina?

Umma taji tana fadin ai kinsan bazai tankaki ba, daidai kenan ya mishi kyau hakan”

Cikin matsanancin haushi Umma mama tace toh ke da kike wanan mgnr kinsan meya faru ne?

Cikin tabe baki tace be wuce ace andaura masa aure ba, yayi kyau, Kuma inji kayi musu ko jayaya da mgnr mahaifin ka, juyawa tayi ta fice cikin zafinta yayin da mama tabi bayan Umma da harara”

Zuwa can ta maida kallonta ga Dattijo, Kai! Dattijo aure aka daura maka? dawa aka daura ?

Har yanzun be motsaba, dan haka Mama ta juya tana fadin Amman Alhaji be kyautaba wlh”

Fitowan ta tsakar gida ta samesa cike, dalilin ‘yan daurin auren da duk dawo, kowa bakin sa bude, Ina angwayen, nan sukejin an daura auren Umar da Asma’u, take, gurin ba gaban mama kadai ya fadi ba hardana Umma salatin tashiga yi yayin da duk gidan bikin ya hargitse kowa da abun da yake fadi”

Itako aunty Maryam fadi take kanbura,uban can, Yaya Dattijon da Asma’u, sunan wani abu wai doya da manja,🤔 yayin da Aunty naja ta kwashe da dariya tare da nufan dakin Umma”

Asma’u ta hango nannande kan gado takara fashewa da dariya tare da jawota”

Bude ido tayi tana kallonta itama Najah kallonta take tana kyalkyata dariya sannan tace”

Sannun da baccin asara, kina nan kina bacci an daura Miki aure da Anne”

Jitayi kamar numshinta zai dauke, kokarin sakkowa take ta fadi kasa”

Dariya Najah ta sakeyi sannan tace”

Natsu dan Ubanki, ba kina kin tsani Anne ba, gashinan ai zakiga Anne ganin idon ki, taf Amman baba ya iya tsiya”

Shiru tayi kamar wadda ruwa yacita nazari take tasan bawasa aunty najah ke mata neman hawaye tayi ta rasa illah wani Abu daya tokare mata wuyanta”

Daker ta iya mikewa ta fito nan numshinta ya kusan daukewa jin kowa zancen da yake kenan, guri daya ta kandare jikin bango tana fadin nashiga uku, ba komai take tunawaba ayanzun illah abun daya faru tsakanin ta Abdullahi”

Nashiga uku take fadin tare da zamewa kasa kasa wani irin uhu ta kurma tare da zubewa akasa”

Da gudu sukayo kanta yayin da Umma ta sameta asume, kubani ruwa kawai take iya fadi”

Shafa mata ruwan ta shigayi ahankali ta fara sauke numfashi zuwa can Kuma ta fashe da kuka tana maimaita nashiga uku umma Inna kizo ki cece ni na mutu kawai yaruwata ta lalace”

Duk da fadan da kowa dake wurin ke mata abun da take maimaitawa kenan Babu saran dainawa”

Mutane ne makil akanta sai birgima take yayin da samarin dake cikin dangi keta kyalkyata mata dariya”

Alhaji Babbane ya shigo ana cikin wannan halin, ganin guri ciki yace manene haka Kuma”

Asma’u ce ke kuka aka bashi amsa”

Korar samarin yayi waje sannan yace wa mata kowa taje ta kama harkanta, Mika hannu yayi ya rike hannun Asma’u yana murmushi ya shige falonsa da ita yayin da Mama ta rufa masa baya”

Amman Alhaji baka kyauta ba, wannan hadi beyiba Sam, Yaya za’ayi a dauki Asma’u abawa Dattijo sabo da Allah?

Hmmm, ni ai yayi min hakan, Dattijo danane inada damar da zan zaba masa matar aure Kuma nazaba masa Asma’u, fita ki bani guri banson mgnr banza”

Ficewa tayi cikin fushi yayin da ya mayar da hankalin sa kan Asma’u kinga, Asma’u bar kuka kijin, kibar Kiran kin shiga uku Babu ukun da kika shiga Dattijo ai yayanki ne shima kamar Abdullahi kibar tsoronsa kinji ko”

Girgiza kai take tare da fadin a’a Baba dan Allah Baba ka taimake ni zan mutu baba wlh Baba zan mutu”

A’a kul Baba ya fada yana zare mata idanu, ki nutsu Asma’u inba hakaba ranki zai baci, kintaba ganin bacin raina?, Karkiso gani ki maido hankalin ki jikin ki, kinga auren nan?, Mutukaraba ne bar zaton akwai mafita, insha Allahu sainaga ‘ya’yanki keda… 🤔 Me kike cemasa ne ma?🤔

Kara fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita, dan haka ya mike cike da mazurai”

Ke bakijin lallashi ko, zaki rufe min baki kosain naki kashi?

Kunshe kukan tayi Baba Dan Allah ka ceceni Baba”

Naji rufe bakin ki to”

Kunshewa tayi hardasaka hannunta ta rufe bakin”

Karki Kara yin kuka kinji ko, tashi ki shiga ciki kiyi wanka sai kizo muga yadda za’ayi”

Ficewa tayi da sauri tuni fuskanta ya kunbura”

Tagumi Alhaji Babba yayi yariyar tabashi tausayi ganin irin kukanda take kaman ranta zai fita”

Bayan fitan Asma’u Umma ce ta shigo ta zauna nesa da Alhaji Babba, Amman Alhaji baka kyauta ba wannan ai zalinci ne, Yaya za’ayi adauki Asma’u ‘yar kankanuwa da ita abawa Dattijo, Kuma ma kana sane da kiyayyar dake tsakanin su, haba Alhaji?

Hawaye Umma ta shere yayin da Alhaji yace”

Kin gama?

Ni bangama ba, yariyar tabani tausayi wlh, haba wanne irin Dattijo, dama dai Abdullahi ne, na tabbata da Abdullahi aka bata wannan kukan da takeyi bazatayi shi ba, ni tuni ma dauka nake Abdullahi mjin Asma’u ne lokaci kawai muke jira ganin yadda suka shaku da juna”

Idan zaki iya saurarata ki saurara mani, inason gaba dayan ku ku sani, bakai tsaye na ya yanke hukunci ba, haka Allah ya rubuta daman can Asma’u matar Dattijo ce ba Abdullahi ba, nima da haka naso, naki furtawa ne gudun samun matsala, amman idan zaki lura duk yariyar da Mahaifiyar sa ta zaba masa bana yadda sai dai nace ya zabo da kanshi, tunani na Wai ku zai furta Asma’u” amman sai naga ya kawo wata daban, hakan ya tabbatar min da bakomai tsanin sa da Asma’u, dan haka ku kwantar da hankalin ku wannan auren Allah ne ya daurashi bani ba”

Sosai Umma ta samu nutsuwa tare da fadin Allah yasa hakan shine mafi Alheri”

Yauwa ko kefa”

***********

Zuciyoyi guda uku cikin tsananin damuwa da fargaba tare da tashin hankali”

Dattijo ji take shine yake da damar yin bakin cikin wannan auren da akai masa gani take yau duk duniya Babu wadda yakaisa bakin ciki, yana yin da Abdullahi yakejin kamar numshinsa zai dauke, ga zafin soyayyarsa ga Asma’u wacce harta kaisu ga aikata sabon Allah ga shi an rabashi da ita an daura mata aure da dan uwanshi mafi soyuwa agare shi” zaune yake cikin wani gini wadda aka fara shi ba’a Kara ba yaci kuka ya koshi har ya godewa Allah ji yake kamar ya gudu yabar garin baki daya, a fali yake fadin”

Allah sarki Asma’u, nashiga uku, anrabani da ‘yar cilligata, anrabani da farin cikin rayuwata an rabani da abin da yake sani nishadi nashiga uku Ina zansaka kaina, ya zanyi ne?, Ina zan saka kaina? Zan gayawa Baba ne ince inason Asma’u bayan ya daura mata aure da Dattijo? Idan nai haka banyiwa Dattijo hallaciba amatayin sa na wadda yamin komai a rayuwa, dalili daya ne zai iya warware auren nan nace nayi amfani da Asma’u, amman ta Yaya zan iya bude baki in kalli tsabar idon Baba ince nayi masu amfani da yariya?, Yariyar ma wacce ayau taki amatsayin matar yayana Dattijo Umar dina, mafi soyuwa agareni, tun Ina Dan karami yake dawainiya dani yana jana jikinsa tamkar abokinsa duk da cewa ya girme min😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭 kuka sosai Abdullahi keyi tare da fadin Allah ka dauki raina👏🏻👏🏻

Yadan samu nutsuwa Dan haka ya Kira wayar Umma”

Abdullahi kana Ina ne??

Cikin kokarin gyara muryansa yace”

Ina gidan su abokina”

Toh me kakeyi can din nan mutane nata neman ka Kuma anta Kiran ka baka daukan waya?

Umma tsoron dawowa gidan nake, Ina ya Dattijo”

Ai tunda ya shige dakinsa be fito ba har yanxu, toh ya za’ayi?

Hmmm Umma Asma’u fah?, tana ta kuka ko”

Itama gata can tunda tasamu lbr take kuka”

Yawo ya hadiya Umma kibata wayar?

Tahowa Umma tayi jikin gadon ta mikawa Asma’u wayar cikin sauri ta amsa domin ta kosa daman tai mgn dashi”

Kuka take rairawa cikin wayar, yayin da Abdullahi ke saurarota, yana share hawaye, Asma’u na cutar dake ko?

Ganin fitan Umma tace, Ya Abdullahi, ka gayawa Baba dakai zamuyi aure, Kai nake so Yaya Abdullahi karka min haka karka bari hadani da muguncan dan Allah ka cece ni😭😭

Anriga an hadaki dashi Asma’u, Baba beyi shawara da kowa ba, bani da huja daman ba ariga an daura bane ayanzun ke matar Dattijo ce”

Nashiga uku Ya Abdullahi abun da ya faru tsakanin mu fah?😭😭😭😭

Shine Abun da yake sakani kuka Asma’u ayanzun shine yafi damuna”

Yaya Abdullahi kaifa kace kaine zaka aure ni ka rufa min asiri ka taimakeni ya Abdullahi”

Cikin matsanan cin kuka yace”

Asma’u mafitar daya ce tall, shine inje inkai kaina gaban Baba in gaya masa abun da ya shiga tsakanin m…..

A’a Abdullahi karka gaya Baba zaiyi tirrr dani, zai iya tsine min Baba, Inna zata tsane ni wlh😭😭”

Hmmmm Asma’u natafka babban kuskure laifi nane Asma’u duk nina jawo wannan abun, narasa meyashiga kaina Asma’u nayi kuskure, tunanina inason auren ki na manta cewa kana nakane Allah na nashi Kuma na Allah shine daidai”

Yaunzon shike nan Ya Abdullahi shikenan ya tabbata na auri Dattijo dan Allah kayi wani Abu kayi wani Abu dan darajar annabi karka bari akaini gidan Dattijo👏🏻

Yaya zanyi Asma’u? ninasan kila mutuwa zanyi, Ina son ki fiye da inda baki zato vansan meyasa Allah ya jarabcini da haka ba kiyi hakuri Asma’u”

Cikin kuka tace nima mutuwa zanyi ai, kaima kasan bazan taba rayuwu Babu kaiba, kuka ne ya kwace mata dan haka ta kashe wayar tare da fashewa da kuka”

Kuka taci ta koshi sai can wajen karfe tara Umma ta dawo jin har yanzun Asma’u kuka take yasata fadin”

Asma’u ke ko gajiya bakiyi?, Kitashi kisawa ranki salama kiyi sallan ko kyaji dadi wannan kokekoken bashi bane mafita haka Umma taita lallashinta da taikakonta tayi Alwala ganin jikinta babu kwari tace tayi salar azaune”

******************

Misalin 11:00pm
Abdullahi ya dawo, tsakar gidan Babu kowa, karewa gidan kallo yayi sannan ya nufi dakin Dattijo”

Mansir abokin Dattijo ya gani falon yana zaune ya amsa waya wuce shi yayi ya nufi dakin Dattijo”

Rufda ciki ya sameshi tsakiyar gadon sa, kallo ya kare masa lallai Dattijo yana cikin damuwa”

Zama yayi abakin gadon Yama rasa me zaice masa, zuwa can ya mika hannunsa ya roko na Dattijo”

Zafi yaji jikinsa rau dan haka ya haye gadon, irin kwanciyar da Dattijo yayi shima ita yayi, sannan ya Mika hannunsa ya ruko Dattijo, Yaya Umar kayi hakuri kaji, dan Allah kayi hakuri, hakuri yaita bashi har tsayon wani lokaci sannan yaga yana kokarin tashi zaune”

Toilet ya shiga bayan kusan minti talatin da shigarsa Abdullahi na zaune yaji an dake kofar toilet din”

Furgita yayi sosai Dattijo ya gani tsaye wanka yayo idonsa jawur dan haka yake cewa ya kadawo hayyacin ka dan Allah”

Hmmm bakomai Abdullahi, shikenan abun da yafi bata min rai wai hardakai aka hada baki akaci mutuncina”

Bansan komai ba Yaya, Baba beyi zancen da kowa ba”

Tafiya yake zuwa gavan madubin dake dakin yana fadin”

Shikenan ai shike nan jeka abun ka”

Zubewa yayi akasa ya rike kafar Dattijo Yaya Dan Allah kayi hakuri wlh baba beyi shawara da kowa ba nagaya maka”

Dagoshi yayi ya rungu me tare da shafa bayansa me jiran kiris, nan Abdullahi ya barke da kuka, yayin da hakan ya karawa Dattijo tausayin Abdullahi sosai yake shafa bayansa har Abdullahi yai shiru”

Tare suka fito falon da shi da Abdullahi yayin da Mansir yayi dariya yace”

Ango kasha kamshi”

Tsaki Datttijo yayi tare da zama gefen Mansir”

Ango ango Mansir ya sake fadi”

Kabari banaso Mansir ✋🏼

Dariya sosai Mansir keyi yayin da Dattijo ya Kara hade fuska”

Tsokanarsa Mansir yaitayi sai dai yaki kula sa Abu kadan yace ango”

Daren ranar Dattijo Abdullahi Asma’u Babu wadda ya runtsa yadda sukaga rana haka sukaga dare”

Yau Asma’u ta tashi fuskanta kunbure dalilin kukan dataci jiya haka shima Dattijo da ciwon ka ya tashi dalilin tunanin da yake Wai shi aka hada da wannan yar yariyar”

Mikewa Asma’u tayi tacewa Umma zani gida”

Gida Asma’u?🤔 Kidai zauna agama biki”

Umma ni gida zani ni bazan tsaya wani biki ba”

Cap matsalata dake taurin kai Asma’u, ki koma ki zauna saina tambayo Baban ku”

Nidai a’a Umma karki tambayoshi kibari harna tafi sannan”

Ke! Kishiga hankalin ki dawo nan ki zauna wannan auren dai an riga an daurashi garama ki nutsu”

Hawaye ta fara sharewa tarasa ma me zata ce, hawayenta yaki tsayawa tana zaune da Hijjabi tana share hawaye”

Kaya Umma kesawa taji Asma’u tace”

Umma ni ban son shi, wlh na tsaneshi, ku rabani dashi dan Allah😭😭

🤔 Toh ai sai kije ki gayawa Baban ku”

Hawaye ta sake sharewa Ke kigaya masa ni dukana kilama zaiyi”

A’a nikam banzuwa tunda bakijin mgn”

Wlh Umma idan a ka hadani dashi saina kasheshi”

Hmmmm ni dama zakibar surutun idan kika kamasa a can ki kashe shin aida yafi”

Umma ni tsoronsa nakeji Dan darajar annabi Umma”

Banza ummta ta mata
Kuka ta cigaba dayi Umma tai banza da ita zuwa can ta barta adaki ta nufi dakin Alhaji shida Mama ta same su kamar ma fada suke, sannu ta masu sannan tace”

Alhaji Asma’u fa har yanzun batabar kuka ba, nayi nayi ta bari taki bari, yanzun ma mikewa tayi wai gida zata”

Murmushi Alhaji yayi sannan yace”

Kirawo min ita”

Bayan fitan Hajiya wayarsa ya dauka ya Kira Dattijo kazo Ina son ganin ka”

Ko minti 5 beyiba saiga Dattijo”

Akasa ya zauna kusa da Baba kamar yadda ya saba”

Gaida Baba yayi sannan Baba yace”

Dattijo yau lallai kana fushi dani bakazo ka gaishe ni ba”

Bahaka bane baba kaina ne yake min ciwo”

Toh Allah ya sauwake, sai Kuma kaji an daura aure”

Sunkuyar da kansa yayi eh Baba”

Ido Baba ya zuba masa yana kallon yadda yasa kansa akasa sannan ya sake cewa”

Toh baka min godiya ba?

Wani kuttun bakin ciki ya hadiye sannan yace”

Nagode”

Umma ce suka shigo ita da Asma’u ganin Dattijo yasa ta kankame Umma”

Tare suka zauna tana makale da Umma yayin da mama ke zabga mata harara”

BABA ne yace toh Alhamdulillahi Ina kyautata zaton bazaka bani kunya ba Umar, kaga Asma’u karamar yariya ce kayi hakuri da ita, nasan halinka sarai Dattijo kana da zafi amman Ina baka shawara akan Asma’u ka rangwanta fushin ka”

Juyawa yayi ya kalli Umma yadda Asma’u ta makalkaleta yace”

Ke Asma’u zo nan”

Kukane ya kwace mata, tare da fadin Wayyo Allah, na nashiga uku, wlh banson shi baba banasa son shi, kurafamin asiri”

Dagowa yayi ya kalleta irin kallon dabe taba mata ba jinjina kansa yayi tare da yin kwafa harya bada sauti sannan ya maida kansa kasa”

Duk ihun da Asma’u keyi yana jinta”

Baba dan Allah karku hadani dashi, abani koma waye ko almajiri ne abani kar ahadani dashi wlh Baba bana sonshi😭😭

Ganin duta gigice Alhaji ya buga mata wani uban tsawa dayasata yin shiru batare data shirya ba”

Tahowa ta farayi cikin rakiyar Umma ta zauna agaban Alhaji Babba yayin da duk ilahirin jikinta ke bari gata ga Dattijo agaban Alhaji Babba”

Shima yaki dagowa ya kalleta kansa akasa”

Bani hannun ka, Alhaji ya fada yayin da ya tsare Dattijo da ido”

Hannunsa ya mikawa Baba ya rike, sannan Baba ya ruko hannun Asma’u, yasa akan na Dattijo tare da fadin rike dakyau Umar”

Balakin rawa hannun Asma’u keyi kan hannun Dattijo saidai ya kasayin abun da Babansa yace bakin ciki ke cinsa wai wannan yariyar aka aurara masa”

Umar dakai nake ka rike da kyau nace………

Mmn Yazeed🖊

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *