Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 18

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

  page 18

Tashi Unaisa tayi zaune, bazata iya cewa ga abun da matar tasa ba amman tabbas ta ga tana tura hannun ta ciki tare da rashin gaskiya a tattare da ita.

    Ganin inda matar da batasan ko wacece ba take hararan ta, ta dauke kanta, zuwa can aka fara fita da kayan sannan bakin duk sun mike, yayin da Ammi keta masu Allah ya tsare.

   Mikewa tayi itama ta fita dakin, jitayi yau kamar damuwarta na dawowa dan haka ta fara shiri tare da kiran sunan Afnan.

   Waigowa Afnan din tayi ta dube ta.

  Kishirya muje gidan Yadikko.

  Gidan Yadikko kuma?, shirye shiryen biki fa ake anan gidan ga d’inkin mu can Hamma Modibo ya kawo mana.

    Wanni irin kallo taima Afnan sannan tace, ” nidai inason zuwa, barin je in tambayi Ammi.

   Ficewa tayitayi yayin da Afnan din ta shiga addu’a Allah yasa kada Ammi ta yadda.

     Sallama Unaisa abakin kofar ta shiga tana fadin, “Ammi Ina son zuwa gidan Yadikko.

    Tob Ina Afnan ai tasan yadda take yi in zaku fita.

   Ai Ammi cewa tayi ita bazata ba fah.

    Ke kadai zaki?

   Amsa Unaisa ta bata.

    Toh ai kina da number Modibo  kirasa ki gaya masa.

Jimmm Unaisa tayi cikin faduwan gaba.

   Ammi saina gaya mishi?

  Eh Mana, ai dama in zaku fita Afnan na gaya mashi, baya hanawa kuma kawai dai ya zama da izinin shi ne.

   Jimmm Unaisa tayi zuwa can tace,

   Toh Ammi idan nakira shi me zance?

     Murmushi Ammi tayi tana bin Unaisa da kallo tana fadin, yanzun ke tambaya Unguwar ma sai an koya miki, ai da bakin ki, kin iya mgn, Koda na kula miskilancin ki yafi akan Modibo, bana tashi sanin kina da baki sai ta ku ta had’oko da Magaji, idan kika rufe Ido kina zaro zance kamar Modibo yasha nono ya rage miki.

     Kunyace ta kama Unaisa irin wacce Bata taba sanin tana da ita ba, har tasa tafin hannun ta ta rufe idon ta, aranta take fadin wace ni na Kamo wannan.

     Ganin Unaisa ta rufe fuska Ammi tace’ ” a’a bude fuskar ki, ki kirashi a waya ki sanar masa kada yamma tayi.

    Kawar da kanta tayi tare da fadin, Ammi dan Allah ke ki kirashi.

     A’a babu ruwana, ki kira shi, ko ki tura Afnan ta tambayi miki, ko ma kije da kan ki.

     Jimmm tayi cikin tunanin abun yi, gidan take son ta Bari kuma idan ta tafi aranta bayau zata dawo ba dan hakama bata damu dasu je da Afnan ba.

      Mikewa tayi ta koma dakin su, Afnan ce kwance tana taba wayarta Unaisa tace, Afnan?

   Na’am.

Dan Allah kije ki gaya mishi zanje gidan Yadikko.

     Me zakije kiyi?, muda zamu fara Shirin biki?

    Nidai dan Allah ki tambayi min shi, ai bikin da saura ai.

    Toh ni dai gaskiya bazani ba, ki Kira shi a waya koki rubuta ki tura mishi.

  Jimmm tayi, akarkashin zuciyar ta saita farajin haushin Afnan, daurewa tayi ta shiga rubutawa sannan ta tura.

    Ajiye wayar tayi tsayon lokaci tanajiran amsan sa, amman shiru har aka kwasa kusan awa biyu, ganin yamma nayi ta mike kawai tahau shiri, sosai tai kyau naban mamaki, turare ta fesa ajikin ta kala kala sannan ta kama gashin ta ta nade shi tare da ta daura dan kwali

Ko magana batama Afnan ba ta wuce yayin da Afnan din ke fadin, ” wlh karki fita tunda be amsa ki ba.

    Ko waigowa ma batai ba, bare tasa ran tajita, ficewa tayi ta turo kofar Ammi da Sallama abakin ta tace Ammi na wuce.

   Ke!! Rahma zonan, kin wuce fa kikace?, kin tambaye shi?

   Eh Ammi.

  Zonan Rahma.

   Shiga cikin dakin tayi inda Ammi ta tsareta da Ido tana fadin, Me yace da Kika gaya mishi?

      Ammi na tura fa kusan awa biyu bece komai ba.

   Toh ki kirashi Mana, kilama be gani ba.

    Dan Allah Ammi idan ya shigo saiki gaya Mai.

   A’a bazai yiyu ba Ammi ta fad’a tare da mikewa tana cikin doguwar riga ba’ka me fadi, ta yane gyalesa daga kanta zuwa wuyanta, farar mace kyakyawa da ita, bakace itace ta haifi su Modibon ba, hannun Rahma ta kama fuka fito har zuwa falon, kafadarta ta kwantar da Unaisa  har suka fito farfajiyan gidan, da part dinta tana iya hangen part din Modibo dan haka idon ta akan kofar shiga falon Modibo tace,

   ” Kinga ga kofarsa cen bude, jeki ki same shi?

     Wasa ta fara da hannun ta zuwa can tce, ni fa banson zuwa.

   Sabo da me?

   Matar shi.

  Matarshi ? matar shi Ina ruwan ki da itarshi Rahma?, kinga indai ba wani iko na Allah ba har ki fito bazaku hado ba, candin falon sa ne
.
Cikin kawar da Fuska tace toh Ammi mezance?

     Dariya Ammi tayi sannan tace, ” Rahma wai meyasa kike d’ard’ar ne da Modibo, kije idan kun gaisa kice Zani gidan YAdikko ne Ammi tace inzo na gaya ma.

     Tafiya ta fara sannan ta sake ja ta tsaya, Ammi idan yace min a’a fa agaban mutane.

    Bazaice ba, Ammi ta fad’a zuciyarta cike da dariya tana tunanin ranar da Rahma zata tare agidan Modibo.

      Tana kallon ta harta fara taka matakalar da zata sadata da falon Modibo, sannan ta juya ta koma ciki.

    Sannun a hankali ta isa bakin kofar, abude take iska na kada labulen me dan karan kyau.

     Sallama tayi daga ciki taji Muryan mace ta amsa.

   Shiga tayi inda sukayi Ido hud’u da Safna tana zaune kafarta daya Kan daya.

   Kallo d’aya taga Modibo ya mata sannan ya kara gyara zaman sa.

    Cire idon ta tayi akanshi ta tsaya tana wasa da hannun ta ta gaidashi ya amsa sannan ta gaida Safna.

     Shiru falon yayi na dan lokaci zuwa can tace, ” Ammi ce tace inzo ingaya maka zani gidan yadikko.

    Zaki gidan yadikko kiyi me?

  Shiru tayi batace komai ba, illa wasa da hannun ta da take.

   Safna ce ta kwashe da dariya.

  Shikuwa cewa yayi karki fita bada yawuna ba, wuce gi koma babu inda zaki….

   Juyawa tayi tun kafin ya rufe baki, afusace ta baro gurin, saidai har tai nisa tanajin dariyar Safna.

    Tana shiga falon Ammi ta fashe da kuka sosai, Ammi ce ta taso tana fadin, ” Yaya ?

     Kuka kawai Unaisa keyi daker ta iya bude baki ta gayawa Ammi yadda akayi sai dai Unaisa Bata rufe baki ba Ammi tace,  bashi bane, cike da
fada Ammi tace wai ke har yanzun baki banbance Modibo da Magaji?

   Cikin kuka Unaisa tace, Ammi wlh shine.

   Nace miki bashi bane, Magaji ne.

  Allah Ammi shine yana zaune fa agaban matar sa.

    Hmmm, to kibar kukan inazuwa….
Ammi na mikewa kiran Modibo na shigowa wayar Unaisa, ganin shine tai saurin yin jefa da wayar

Kallon ta Ammi tayi sannan ta kalli wayar, hannu tasa ta dauka, Kiran farko ya katse wani na shigowa,duk da cewa wayar ta fashe be hanata ganin  sunan Modibo ba, dagowa tayi ta sake kallon Unaisa tace, ” Ke ki nutsu kinji ko, gashi nan yana Kiran ki dauka.

   Tana Mika mata wayar Kiran ya yanke, wayarta ta d’aga ta kira Modibo bayan ya dauka tace kana Ina ne?

   Ina gida Ammi.

   Magaji fah?

  gashi Yana Nan Ammi.

   Toh gafa Unaisa tanata kuka tazo tambayan ka ka mata wulakanci..

   Ammi banga sakonta ba sai yanzun nakira bata dagaba, yanzun Magaji yake cemin tazo, ta fito na kaita.

     Sauke wayar Ammi tayi sannan ta kalli Unaisa tace, tashi ki wanko fuskarki kizo kuje yace zai kaiki, Magaji kuma ki barni dashi inaganin saina mishi Mummunan furuci tukuna zai kiyaye ni.

     Mikewa tayi tayi ta share fuskarta kawai, kamar tace ta fasa zuwa saidai kuma Ammi na tsaye agurin.

                           *******

Acikin motar ta samu Modibo shine matukin ta, fuskarta ta hanga daure tamau, cikin sanyin jiki ta bude gefen sa ta shiga ta zauna, yadda ya ke kallon ta yasa ta kasa rofe motar hannun sa taga yayi saurin mikowa kamar zai riketa dan haka ta buga tsalle ta fice amotar.

    Tsaye tayi akasa tana kallon jikinta, gyalen ta na cikin motar ta barshi hakama takalmin ta, daurewa taga ya sakeyi kamar be taba dariya ba yace, ” shigo muje”

     Nina fasa zuwa.

    idan Kika Bari na sakko ranki zai baci.

   Nufar Motar tayi tana zare Ido, Zama tayi tare da fadin, dan ya rasullahi karkamin komai.

    Dauke kansa yayi daga kallon ta, tana rufe motar taji ya kulleta, tare da fadin Ke wacce irin yariya ce?, baki da hankali ne?, abun nan yana min ciwo, zan fara dukan ki wlh, jariyar ce ke kokuwa baki gani ne?, duk abun da nake gaya miki bakya ganiwa?

   Ayanzun ba masifar da yake bane yafi tada mata hankali, yadda yake figar motar yana fada, gani take kamar motar zata kifa sabo da yadda yake figarta.

       Kallon shi take sannan ta kalli hanyar, sabo da tsabar firgice ta kasa cewa komai fada kawai yake, bata taba tunanin zasu isa lafiya ba dan haka lokacin da suka shiga gidan su Yadikko ta saki ajiyan zuciya tare da kokarin fita a motar.

    Saidai wani tsawa taji yayi wadda yasata zabura ta kalleshi, kin maidani mahaukaci ne Ina mgn kin barni, kareke mgnr yayi tare da cifko yatsunta ya matse ta yadda take ji acikin jikin ta.

      Runtse idonta tayi tare da fadin, dan Allah kayi hakuri, ban kalleshi bane bare na gane, hawaye ne ya zubo mata dalilin rad’ad’in da takeji a yatsun ta, zuwa can taji hannun yayi sauki, kafin ta bude idon ta taji Karan rufe motar sa alamar ya fita, dan haka ta bude idon ta hango shi tayi yayi nisa a tafiya kamar zai tashi sama.

    Sanyi jikin ta yayi sosai ta dade acikin motar sannan ta fito tana kallon yadda hannun ta sukayi jawur, rasa abunnyi tayi dan haka kawai ta kwanta ajikin a motar.

                       ******

  Kwance yake akan cinyan Yadikko, cikin sigan lallashi take tura hannun ta cikin kashin kanta tana fadin, Malam yi hakuri, ka tashi ka gaya min meya bata maka rai haka?, rabon da naganka cikin irin wannan halin nad’ad’e.

    Saukan Numfashin sa kawai take ji, shigowan Suraj yasa Yadikko ta d’aga kanta ta kalle shi.

   Shima Suraj kallon su yayi sannan yace menene  Mama?

       Ai bemin mgn ba Suraj kasan shi da fushi.

   Allah ya kauta toh, shine ya baro yariya awaje shi ya taho shagwaba?

   Wacce yariyar? Yaddiko ta tambaya?

Shigowan Unaisa adaidai lokacin yasa suka dago maida hankalin su wajen ta.

   Yaddiko ce tace shigo zo ki gays min lafiya.

   Jim shigowanta yasashi mikewa kokarin ficewa yake Yaddiko tace zonan ka gaya min waye ya Bata maka rai.

    Yana tsaye bakin kofar yace bakomai Yadikko kidai mata fada tana sakin kanta da rashin wayau Magaji na mayar da ita mahaukaciya, Ina son abin ya tsaya ahaka banson yai nisa.

   Malam toh kai ka dakatar da Magajin mana.

  Yadikko laifinta ne, kina ganin ta haka…..

  Bai kai ga karasawa ba karan wayar sa ta katse shi, kallon wayar yayi sannan yai saurin amsawa cikin ladabi yayi Sallama, jimmm yayi tsayon lokaci sannan yace Innalillahi wa Inna ilaihir raju’un….

 

8 comments

  1. Pingback: โซรา168
  2. Pingback: stapelstein
  3. Pingback: fruit cash

Comments are closed.