Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 20

Posted by

BA LABARI BOOK

BA LABARI BOOK 2

By

FADILA LAMIDO

PAGE 20

Jimmm ya danyi sannan yace, a’a

  Daya saurayin ne ya kalli Modibo yace kullum fa suna tare da Afnan?

  Kila cikin kawayen tane Modibo ya fada yayin da Abba yace toh bakomai zan mincika inji daga Ina take,
.
Ganin Abba ya dauke idon sa akan shi  yai maza ya fice, part din sa ya nufa yana daf da isa ya dawo da baya, juyawa yayi idon shi jawur ya isa part din Ammi, Nan ma har ya tura kofar Ammi ya sake ta, tare dajan tsaki ya juya, dakin su Afnan ya nufa, tura kofar kawai yayi ya shiga adaidai lokacin da Unaisa ke kyalkyalar dariya, be yi wata wata ba ya rike wuyan rigar ta cikin daga murya yake fadin, ” me kike nufi da tura wani gurin Abba?

     Cikin rashin fahimta take raba Ido tare da fadin, ” Ni?”

   Au tambayata kike yi?, saukan Marin dataji yasata saurin runtse Ido tare da dafa gurin .

    Ammi ce arude ta turo kofar ta shigo tunda yazo kofarta taganshi tsakin da yaja ya tabbatar mata wani abu na faruwa dan haka ta biyo bayan shi.

    Ganin shi cakume da Rahma ta Kara rikicewa, cikin tsawa take fadin, “Modibo menene haka?, me tayi.

     Huci kawai yake ya fada cikin hargagi.

     Hannun sa Ammi ta kama wadda yake wuyan Unaisa tace yi hakari ka sake ta.

     Ban bare hannun sa tayi daker Yana cigaba da huce, me ta maka?

   Huce kawai yake dan haka Ammi ta maida hankalin ta ga Rahma tace ke me Kika mishi?

       Cikin matsancin kuka tace nima bansani ba Ammi.

   Modibon ta sake kallo, sai huci yake, gefen da Afnan take tsaye a firgice Ammi ta kalla sannan tace, ” Afnan bamu guri.

    Cikin sauri Afnan ta fita tana tafe tana waiwaye.

     Modibo me ya faru?, Ammi ta tambaya bayan ta tsare shi da idon ta.

    Kawar dakai yayi tare da sauke ajiyan zuciya.

   Bakajj ne Ina mgn ka kasa amsa min nace me ta maka?

    Ammi wani ta tura gurin Abba wai yazo da iyayen shi neman auren ta.

  Kallon ta Ammi tayi sannan ta koma bakin gadon ta zauna a gefen Unaisa tana fadin, ” anzo gurin, menake gaya maka tun can baya??

   Kawar dakai yayi can gefe tare da shafa sumar sa.

     Cikin kuka Unaisa tace Ammi bani na tura su ba, bansan ma kwata kwata da zancen ba.

     Rufe min baki agurin, mara hankali kawai, Modibo ya sake fada cikin daga murya.

  Kai Banson hauka, kasan kana kishin ta ka barta saka saka, tuni nake ce maka ka dauki matar ka amman kakiji, kace sai tayi karatu toh ai ga irin ta Nan, gashi nan kaga abun da ake gaya maka.

     Toh ta tashi muje Modibo ya fada kansa a sunkuye.

     Kuje Ina?

     Kasa amsawa yayi dan haka Ammi tace kana nufin ka tafi da ita ta tare yau?, ai ba kaza bace, kaje kayi tunani kaza kadai ake ma haka, mutum ce ita dole zaka bata lokaci ta shirya.

    Batare daya dago kansa ba yace, ” Ammi Shirin me zata yi? ta wuce muje kawai.

    Wlh baka isa ba Modibo, kaje ka nutsu sannan kasa rana, kuma ranar dole ya zama ta kare jarabawar ta tunda suna kanyin shi a yanzun, sannan ka shirya yin duk wasu abubuwa wadda akewa Amarya ita ma ka mata.

    Batare dayace komai ba ya juya ya fice har yanzun afusace yake.

      Daga Ammi har Unaisa bayan sa sukabi da kallo, bayan ya fita ne Ammi tasa hannu tana sharewa Unaisa hawaye tana fadin, ” Rabo dashi Rahma, kishi ne ya rufe masa ido”

   Ammi fa bani na turo su ba.

   Naji ki kwantar da hankalin ki shi kanshi ma kishi ne yasa shi fadin haka din.

    Daker Ammi ta rarrashi Unaisa tai shiru sannan ta fice ta bar dakin.

                       *****

Shine yazo min da zancen neman izzini ‘yata, saidai da mgnr tai nisa saina gane ba akan Afnan suke mgn ba, wata ce daban, to nidai nasan babu wata budurwar yariya a gidan Nan bayan Afnan koko kinyi bakuwa ne ban sani ba.

    Dan diriricewa tayi cikin rasa abun yi, batason tamai karya dan idan yagane karya ce bazaiji dadi ba, dan haka gara ace ta fada masa gaskiya kawai, dagowa tayi tana fadin, ” Ina tunanin akan matar Modibo suke mgn”

    Matar Modibo? Safna ?

   A’a Wannan dai Amaryar tasa Rahma.

   Toh ton naji, shiru yayi alamar nazari sannan yace, amman ba haka sukace ba sunan ta, sunan da suka gaya din na tambayi Modibo yace be Santa ba.

      Unaisa suka ce halan?

  Yauwa haka .

Dole yace be santa ba, toh me zaice Alhaji, matar sace yaji anxo neman auren ta, ai yazo yanata hauka.

  Au matar sa?, amman wanni irin roko yake mata dahar lalacewar takai haka? idan ba lalacewa ba ta taya za’azo neman auren matar aure.

     Babu komai Ammi ta fad’a.

  A’a da komai,  ai matar aure ta fita daban, meyasa tun da ya auri Safna ba’a taba zuwa neman auren ta gidan nan ba.

   Jimmm Ammi tayi sannan tace toh Alhaji ba zancen boye boye, yariyar nan har yanzun ba tarewa tayi ba, makaranta yasata suna tafiya tare da Afnan, tuni nayi nayi dashi ya dauki matar shi yace min a’a ba yadda banyi dshi ba yace saitayi karatu.

   Karatu ko?, lallai Modibo ya raina ni, nasha tambayan shi tun baya sai yace min aita tare, ni zai mayar mahaukaci, waya Abba ya dauka dake gefen kujera ya shiga kiran Modibo.

     Ciki kankanin lokaci saiga Modibo, tunda yaji Kiran yasan kawai ma akan mgnr ne, fada Abba yaita zazzaga masa Yana hanasa ya kare kansa  gaba daya be bashi kofa ba, duk inda yaso yin mgn yaki dan haka ya sukuyar dakai yaji fadan Abba, akarshe yace ya tashi ya tafi.

    Part din sa ya koma ransa abace ji yake kamar yace wayyo Allah.

             Shima Abba fadan sa ya mayar kan Ammi, ta inda yake shiga batanan take fita ba, shiru tayi har yagama sannan ta bashi hakuri.

   Hakurin me zaki bani, bayan kun ga, ma zubar min da mutunci ta Yaya zan iya bude baki ince masu yariyar da sukazo neman auren ta suraka tace ce”

       Hakurin dai abin ta cigaba da bashi tsayon lokaci.

Shiko Modibo bayan ya zauna afalon sa rasa inda zaisa kansa yayi bashi da wani buri illah ya bude idon sa ya ganshi kusa da ita, ji yayi yai masifar kosawa ya ganshi gata gashi sosai hankalin shi ya yake a tashi irin wadda baya tunanin ya tabajin hska akan kowacce mace, Kiran yadikko yayo bayan sun gaisa yace,

      Yadikko Akwai laifine dan nace Rahma ta tare yau?

    Jimmm tayi sannan tace, Babu laifi Modibo ai matar ka ce babu me hanaka duk inda zaka kaita.

   Toh Yadikko tun rana nake rokon Ammi amman taki sam.

     Ka mata wani abu ne??

   Yadikko idan ma nayi mata wani abu wannan inace nida itane kawai, dan Allah Yadikko indai inda damar cewa abani ita to kisa baki Ammi ta bani ita adaren nan.

    Modibo, Amman me yake faruwa?

   Daga baya zan miki bayani Yadikko.

   Toh shikenan yanzun dai kayi hakuri da safe zanzo na same ta……

    Yadikko bazan iya bacci ba, inzo in dauke ki ne?

      Jimmm tayi sannan tace, a’a bari Ina zuwa zansa Suraj ya kawo ni.

         Sauke wayan yayi tare da ajiyan zuciya Safna ce ta shigo hannun ta dauke t da Babban tare na kayan abinci, tsugunawa tayi ta direshi a kasa saidai tun kafin ta dago kanta ta dubeshi yace, ” dauke kanyan ki banci “

     Duban shi dayi da mamaki akan fuskarta, Bakaci to me zakaci?

Banson mgn Safna kwasheshi kawai ki wuce abun ki.

   A’a, Hamma ko namaka wani abu ne?

    Kawar dakai yayi tare da lumshe Ido zuwa can ya bude su adaidai lokacin da Safna ke fadin, ” idan wani abu nama ka yafe min.

   Wani uban tsawa ya buga wadda yasa ta barin miya batare data sani ba, sosai jikin ta yahau rawa, Ido ta kura masa gaba daya tama rasa abun da zatace masa, mikewa tayi afusace ta fita tare da buga kofar ta karfi.

     Mikewa yayi tare da fadin, Ke! zonan.

   Ahankali ta turo kofar ta tsaya, wa kike zagi?

    Hamma Modibo banyi ko mgn ba….

Kishiga hankalin ki kinji na gaya miki, Dan nace banson surutu kike buga min kofa, ni abokin wasan ki ne?, ke, fita kiban guri, ki tafi gidan ku.

   Wani irin kallo ta masa jin yace ta tafi gidan su, tsayon lokaci ta dauka tana kallon shi sannan ta juya ta fita.

       Tana tafe tana tunani cikin ranta, da ace agarin nan take babu abun da zai hanata tafiya domin abun ya Bata mata rai sosai babu laifin zaune babu na tsaye, part din Ammi ta nufa domin cikin wannan daren batasan Ina zata ba, tafe take tana hawaye.

     Tana shiga part din Ammi motar su Yaddiko na tsayawa, Modibo ne ya taho suka gaisa da Suraj sannan ya gaida Yadikko, cikin gidan ta nufa yayin da Suraj da Modibo suka zauna cikin motar……