Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 27

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido

Page 27

Sallama ya rangada tare da tura kofar.

Tunda taji Sallamar sa gaban ta ya fadi, tanajin takunsa yayin da jikin ta ya dauki rawa sosai.

Gefen  ta ya zauna tsayon lokaci yana kallon ta, duk da cewa jikin ta rawa yake amman duk da haka wasa da hannun ta take yi tana rufe cikin mayafi.

Tsayon lakaci ya zauna agefen ta har ta farajin rawan jikin nata na raguwa.

Duk wannan zaman da yayi idon shi na kanta, tundaga sama har kasa yake kallon ta, shi kadai yasan abun da yakeji cikin ranshi, idon shi ne ya sauka akan zanen lallain kafar ta, Saida ya gama kare mata kallo sannan ya mika hannun sa ya bude fude mayafin dage kanta ya sauka a kafad’ar ta, Ido ya zuba mata yayin data sunkuyar dakan ta a kasa.

Kula yayi hawaye na zobo mata, cikin dan haka ya mika hannun shi ya dago kanta yana kallon cikin idon ta, sau daya ta kalleshi ta rufe idon ta, sai dai kallo dayan da ta mai ya tafi cikin zuciyar ta domin Koda ta rufe idon ta shi d’in dai take gani.

Cikin wata irin Murya taji yace, ” bude idon ki ki kalle ni”

Kokarin kawar dakai take dan haka ya rike kanta da kyau tare da kura mata ido.

  Bude idon ta tayi sannan ta sake mayarwa ta kulle, ahankali ya sake matsawa daf da ita, Zabura tayi ta ture sa sannan ta mike tsaye tana raba Ido.

    Kallo ya bita dashi tana tsaye a tsakiyar dakin garin tashima har ta yarda mayafin nata, sama da kasa ya kalle ta, dariya ta bashi dan haka ya dan dara sannan yace Ina zaki to?

    Laben ta na kasa ta kama ta dan ciza tare da Satan kallon shi.

    Nace Ina zaki?

  Kawar dakai tayi da saurin, jin sa tayi ya sake fadin, ” ki dawo ki zauna nace.

  Ganin har yanzun tana tsaye agurin yasa shi mikewa cire Babban rigar sa yayi sannan ya shiga kwance agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa yana fadin, ki dawo ki zauna karki lalata min dare na, na dad’e Ina jiran wannan ranar, nasanki nasan halin ki, haka kema Ina tunanin kin san halina, kodai ba duka ba, duk da cewa yanzun ba da bane, Nan ba YOBE bane, bakuma dakin Ammi bane, nan gidan mijin ki ne, akwai hakokina da yawa akan ki ayanzun, haka kuma kema akwai naki akai na, amman nasan bakisan mahimmancin naki hakkin ba ayanzun,  bazan biye miki ba dan nasan yarinta ke damun ki, kwanaki kina tambayana wai auren mu na gaske ne, toh yau ne alkawarin ya cika, yau zan baki amsa.

   Zuwa yanzun tsaye take car a tsakiyar dakin ita daya tasan me take ji.

Kizo ki zauna nace ko?

  Ahankali ta fara takowa ta zauna agefen kamar ace mata tak ta zura a guje.

      Ki zauna da kyau ko.

   Gyara zamanta take tare da fadin, ” bani da lafiya fah.

   Eh, na sani Ammi ta gaya min, kina zazzabi ko?

   Kai ta daga tare da kallon shi.

Toh karki damu, Ina da maganin shi zazzabin naki har  da amai ma ko?

   Eh ta sake cewa, a daidai lokacin daya nufi toilet din dake cikin dakin, be jima ba ya fito da alama alwala yayi Yana gyara hannun rigarsa yake fadin jekiyo alwala.

Taso tayi musu domin tasan Shirin tabata yake saidai batasan ta Ina zata fara yin musun ba, mikewa tayi ta nufi toloil din , Saida tayi amai gurin alwalar sannan ta gayara komai ta fito.

    Tana fitowa ta samu hijjabi ta aje gefen gadon dauka tayi ta sanya, sannan ta isa inda taga ya shinfida sallaya yana zaman jiran ta.

Binsa tayi yana Jan musu sallah, bayan sun idan taso ta rigashi tashi agurin saidai bata Ankara ba taji ya rike kan ta, mamaki Abun ya fara Bata yayin da take ganin Kamar bashi bane ba, har ya gama ya saketa bata iya bude idon ta ba tajin sa zaune kusa da ita tsayon lokaci sannan taji mikewan shi, Karan kofa taji alamar ya fita adakin.

   Bude Ido tayi tana kallon dakin gani tayi babu Baban rigarsa daya aje agefen gado, dan haka tai saurin mikewa tana addu, ar Allah yasa kada ya dawo, kwanciya take son yi duk da cewa babu bacci a idon ta, gashi kayan jikin ta sun dameta, Akwatin ke jere ta nufa da sabbin kayan bacci ta fara jin karo gasunan jere kala kala, masu Dan dama dama ta samu tasa sannan ta nuke wadda ta cire ta ajiye, sai yanzun ta kula be dauki a agogon sa ba, dauka tayi ta isa gaban madubi ta aje nan ta sake ganin wayoyoshin akan madubin jimmm tayi aranta take fadin zaidawo…..

   Bata gama tunanin ba taji motsin sa dan haka tai saurin hayewa gadon tare da jawo bargon ta rufe jikin ta, fuskan ta kofar tayi sannan ta rufe idon ta yayin data bude su a hankali ta Sata kallon shi.

  Duk da dai Bata bude idonta sosai ba Amman gani tayi kamar kayan bacci ne ajikin sa, sosai kwarjinin sa ya kara firgita ta, domin gani tayi kamar ya kara tsayo da da girma gaba daya a idon ta, gefen gadon ya zauna da ledoji a hannun sa, waigawa yayi ya kalleta sannan yace tashi ki zauna.

     Bata motsaba dan haka yayi murmushi tare da sake fadin, Rahma tashi ki zauna nasan kinajina.

  Kasa yi Masa musu tayi, tunkan ta bude idon ta tafara jin kamshi na tashi, ledar dake gaban shi taga yana budewa.

   Satan kallon ta yake yayin da take Dad’a Jan bargon tana kara rufe jikin ta.

      Matso nan kici.

  Nakoshi ta fada tana kawar dakai.

   Sai kin ci, Modibo ya fada yana turawa gabanta bayan ya bude bakin ledan.

    Na koshi.

Ina wasa dake ne?, angaya min yau kwata kwata bakici komai ba, saboda fargaban da kikasawa kanki, maza kici ki kwanta kiyi baccin ki, amman idan bakici ba wlh abun da kike gudu shine zai faru, garama kici.

   Satan kallon shi tayi inda taga ya kawar da kanshi dan haka ta jawo ledan gabanta, mikewa yayi ya nufi kofar fita yana fadin kuma ci zakiyi sosai.

Kasancewar akwai yunwa a cikinta ta shiga cin naman tare da Addu’a Allah yasa babu abun da zai mata, be jima ba ya dawo hannun shi rike da kofi wadda ke cike da Madara me sanyi ya mika mata amsa tayi tana mebin bayan sa da kallo.

Gaban madubi ya isa ya dauko wayarsa sannan ya dawo ya zauna gefen gadon, ta gefen idon sa yake satan kallon ta, sosai yaga taci naman sannan ta shanye madarar, daga inda take zaune ta jawo hijabbin datai sallah dashi ta saka sannan ta mike ta shiga toilet, bin bayanta yayi da kallo fuskan sa cike da Murmushi, acikin ransa yake fadin yau naga yariya da karfin hali, wai toilet dinma da zata shiga sai an wani zura hijjabi, dariya ya sake yi, tare da jin tana Kara shiga ranshi, mikewa yayi ya dauki ledan da kufin ya nufi kitchen dasu, nan take ya tuna da daren farkon shi da Safna, duk wannan abun da yaiwa Unaisa Safna da kanta tayi kayan ta bakuma dan bazai iya yid’in ba saidai Bata nuna  bakunta ba.

    Unaisa kuwa bakinta ta wanke sannan ta fito adaidai lokacin da Modibo ya bude kofar Yana dawowo, ganin tana rabe rabe yace kizo ki kwanta abunki.

    Tacan gefen ta zagaya tahau gadon. saidai wannan karon bata cire Hijabbin ba, bece mata komaiba harta rufe jikinta ta juya mishi baya.

     Zama yayi gefen kadon ahankali ya miker da kafarsa akan gadon, zaune yake, ya jingina bayan shi da allom gadon, ganin yajita shiru yace toh adai yi addu’a.

  Nayi, Tafad’a ahankali,

Toh kin kyauta, Saida safe kenan?

  Kaita daga dan haka yayi murmushi sanan ya fara danna wayar sa, tsayon lokaci ya dauka zaune agefen ta sannan yaji alamun tayi bacci dan haka ya kwanta nan inda yake.

                           *****

   Modibo ne zaune akujerar dake gefen gadon yayin da Unaisa kokarin gyara gadon tana sanyi cikin riga da saket da atamfa, tsinkayan muryan sa tayi yana fadin, ” Yau nayi kwanan wahala, agefen gado aka tura ni, sannan aka juya min baya, yanzun haka ma jikina duk ciwo yake  min, duk wata gaba dake jikina ta sage.

    Cak Unaisa ta tsaya sannan ta juya ta kalleshi, sai dai shi ba ita yake kallo ba waya ne manne a kunnen shi, dan haka ta zauna kawai abakin gadon tacigaba dajin shi yana cigaba da cewa, ” toh Yaya zan yi da ita?

      Kallon shi ta sake yi wa yake gayamawa, ta tambayi kanta, mikewa tayi tacigaba da gyara gadon.

    Zuwa can taji ya gama wayar ran ta taji duk ya bacci me zaisa ya gaya ma wani haka, tana tsaka da tunanin taji yace, ” Anuty jiya da dare nasha  wahalan gurin Bacci, wuyan shi ya karyar, tare dasa hannun sa ya matsa alamar yana masa ciwo, tare da fadin, ” kinga nan?, ba’a mgn, ciwo yake min sosai, ban saba irin wannan bacci  ba.

   Sake kulewa Unaisa tayi dan haka ta dauke kan ta.

Mikewa yayi tare da fadin, ” Ina zuwa barin je  in fadawa Safna ko na samu ta danna min jiki na.

   Da saurin sa yake tafiya harya bude kofar yajiyo ta cikin siririyar Muryan ta tana fadin, Karka gaya mata haka.

     Batare da ya jiyo ba yace zaki  tausa min ne?

    Kamar bazata amsa ba zuwa can ya bude baki daker tace, Eh

  Sakin kofar yayi sannan ya dawo gadon ya kwanta, zagayowa tayi ciki da haushin sa aranta, ahankali ta daura hannun ta gafadar shi ta danna.

   Washhhh Allah na, taji ya fada cikin wata irin Murya, kawar da kanta tayi batare data kalle shi ba, matsawa tai tayi, daga kafa zuwa wuyan shi, nurfaffashi yake sauke wa  tare da fadin Washhhh

  Gani take tamkar ba Modibo da ta sani ba, sai wani Shan yaji yake Kamar mejin sanyi, tsayon lokaci ta dauka ta nayi sannan taji shi shiru, leka fuskar shi tayi taga kamar baci ya dauke shi, dan haka ta koma kan kujarar ta zauna tana kallon sa, yadda ya beje agodon take kallo, watoh haka ne yafi son yayi, dan be samu yayi jiya ba yake ciwob jiki, kila so yake abar mishi gadon ko kuma ya kwanta akaina, ta fada tana me kura masa Ido, yanzun yau Yaya zanyi kenan.

  Bacci yayi sosai, tun misalin 8 ya kwanta sai goma ya tashi, wanka yayi ya shirya cikin manyan kaya sannan ya dubi Unaisa yace, ” na gan ki yau da kwarin ki kika tashi, naji dadi dana daure na bada wannan bashi, Allah yasa ki biyani da dadin rai, nima gobe in tashi da karfi na, hannun ya mika mata, tare da fadin, ” Muje part d’ina Safna tana jiran mu,

7 comments

  1. Pingback: Jaxx Liberty
  2. Pingback: Mega Moolah
  3. Pingback: Go X

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *