
BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO
PAGE 49
Dada ce tai dariya, itama Yadikko dariya tayi sannan tace, ” Modibo bamu da ishashshen lokaci yanzun, ko bata nan Dada zata iya bada sadakar kayan, ke kuma Unaisa idan akwai abun da kike so kije ki dauka sauran abadasu sadaka babu amfanin barin kayan.
Unaisa bata iya cewa komai ba domin har ga Allah batason a bada kayan kuma batasan dalilin jin hakan ba.
Muryan Modibo taji yana fadin, babu wani abu ma da zata dauka duk za’a bada.
Yadikko ne tace, a’a kabarta ta dauki duk abun da ranta keso, Juyawa Yadikko tayi ta kalli Dada tace, “ina kayan suke?”
Mikewa Dada tayi tana fadin, ‘muje ki gani, Yadikko ce ta mike tabi bayan ta dan haka Modibo ma ya zunguri Unaisa, wani irin kallo tamai sannan ta mike tabi bayan su.
Suraj ne yabi ta da kallo sannan ya kalli Modibo yace, “lallai kana fama, wannan matar taka miskilace ta karshe.
Murmushi Modibo yayi tare da lumshe ido sannan yace, ” kuma a haka nake son kayata ba…
Ai daman bance baka santa ba, son da kake mata a bayyane yake, domin ka zurma da yawa.
Eh na zurma ɗin, hakan ma da kake gani ina boyewa ne sabo da gudun samun matsala.
Wacce irin matsala kuma?, hmmm Modibo kenan, ai babu wani abun da yake boyuwa daga gare ka wlh, soyayyar yariyar nan bayyane yake ƙarara acikin idon ka.
Haba?
Kwarai kuwa, saidai ka boye ma mara hankali.
Baka fahimceni ba, ina mgn akan Ita Rahma ne, akwai abubuwan da bana bude mata su sabo da Safna, kasan mata da gori, da soyayyar da zan numa mata saita narkar dakai.
Dariya Suraj yayi tare da fadin, ” ni daman nasan duk daren daɗewa zakayi auren soyayya, auren zabin ranka, dan lokacin da akayi auren ka da Safna nasan ba ra’ayin ka bace, kuma koda ka auri Rahma ban dauka ma zakayi zaman aure da ita ba sam, amman daga baya sai naga abun ya canza.
Murmushi Modibo yayi, sannan yace, ni tunda na ganta nake jin ina son rayuwa tare da ita, a wancan lokacin ni kaina ban dauka cewa soyayya zata shigo ciki ba, amman nasan inason kasancewa da ita tamkar acikin jinina yake, saidaga baya nake ganin inda na rasata bazan Ina zansa raina ba.
*****
Ki daina biye mata Dada, duk ki bada kayan sadaka
Yadikko toh abada suturon sai a barmin gado da katifar.
Kiyi me dasu?, Yadikko cema mata wannan tambayan.
Cikin sauri ta sunkuyar da kanta tare da wasa da kunbunan hannun ta, tana fadin, toh Yadikko idan wata rana ya sake koro ni fah?
Da sauri Yadikko ta kalleta sannan tace, wanni irin tunani ne wannan?, babu inda zai koreki, idan ma hakan ta faru mu baki dauke mu iyaye ba?
kara sunkuyar dakai tayi sannan tace, Yadikko Ni nafiki jin dadin zama dakin Innawuro, gidanta shine gatana Yadikko domin abaya inda babu gidan saidai inyi yawo a titi, kuma kayanta sun min amfani, kowa ƙina yayi sai Dada kaɗai…..
Hannu Yadikko tasa ta rufe bakin Unaisa, sannan ta jawota ta kwantar kan jikin ta tana share mata hawaye take fadin, ” bar kuka kinji ko?, insha Allahu keda Modibo mutuwa ce zata raba ku, kuma mun riga mun zama daya.
Wata rana zai iya korata Yaddiko.
Bazai koreki ba, jiyan ma bacin rai ne, waya Yaddiko ta daga ta kira Modibo bayan ya shigo tace, ” Rahma tace tana son gadon sabo da wata rana in ka koro ta.
Dariya Modibo yayi sannan ya kalli Unaisa yace, ku daina biye mata, kame kame kawai take, yaso ya faɗa ma Unaisa wata mgn saidai kunyan idon Dada ya hanashi faɗa, dan haka ya kwar da kai yana murmushi, tare da faɗin, Mama ku bada dukka kayan kawai.
Modibo na tsaye Dada ta fara fito da suturon Innawuro da suka sha ajiya cikin wasu akwatuna, tasss ta fito dasu yayin da tana fitowa dasu Modibo nabin fuskan Yaddiko da kallo, saidai har suka kare beka wani canji daga fuskan yadikko ba, dan haka ya shiga zurfin tunani zuwa can ya tsinkaya muryan Yadikko na fadin, toh ai inaga tunda Innaworo tana da ‘yan uwa su yadace suzo su kwashi kayan sai ace musu Rahma tace ta yafe.
Dada ce tace, ” toh wata kila yanzun su karba amma shekarun baya cewa sukayi basa so.
Toh ki tuntubar su sai kiyi duk yadda ya dace.
Modibo ne yace, babu sauran suturar ne sukenan wadɗa nan?
Eh su kenan tun ranar da zamu tare anan na haɗe su guri daya.
Ajiyan zuciya Modibo yayi saidai har yanzu zargin yaki barin sa sai kallon dakin yake yagani babu wani abu amman bega komai ba.
Yadikko ce tace Modibo muje, yamma nayi, Dada zatayi abun da ya dace, da haka suka fito wannan karon Modibo gaba ya zauna yayin da Yadikko da Unaisa suka zauna abaya, sallama sukayi da Dada har suka fita gate tana daga musu hannu.
Shiko Modibo tun daga lokacin ya zama tamkar mara lafiya, yayin da wata zuciyar kece masa kawai ya fito ya gayawa Yadikko zargin sa wata kila ta hakan a samu mafita.
Juyawa yayi ya kallesu ita da Yadikko sannan yai shiru yana tuna yadda Dada ta bashi labarin haihuwar Unaisa, sannan ya tuna yadda yadikko ta ke bada labarin haihuwar ɗanta, da yadda Moh’d ya faɗa inda ya bayar da jaririn har ma da komawar da yayi akaki koda kaisa gidan mutumin tare da nuna mutumin abun tsoro ne shida matar sa, sannan ya tuna yadda Dada ta bashi labarin yadda kowa ya guje yariyar sabo da ganin babu wadda yasan labarinciki ajiki wadda take ikirarin ita ta haife ta, haka Modibo yaita tattara labarin tare da haɗesu waje daya, yana me kara tabbatar da tunanin sa cikin ransa, sosai yake son yayi mgn da Yadikko saidai yana tuna gargadi Ammin sa, dan haka ya kwanta akan kujeran ya lumshe idon sa.
Hotunan tsofaffin guda biyu ne da ya taba gani hannun Unaisa suke masa yawo a ido, acikin zuciyar sa yace, hoton Baffah zai iya yin amfani agurin Moh’d.
Tunani ya kara zurfafawa inda zai yi ya neme hoton cikin sauki, hakan nan yaga ya fara tuna dakin Innawuro, ada inda Unaisa tai rayuwa ita ɗaya nan ya tuna wani akwatin karfe kato dake kasa wadda yaga kamar zama Unaisa keyi kansa tamkar dai ta mai dashi kujerar ta wadda yake sanye da wani karnakeken kwaɗo.
Ajiyan zuciya yayi acikin ransa yace yanzun ina akwatin yake, ban ganshi ba anan dakin da kayan yake…
Da tunanin wannan akwatin cikin ransa suka isa gida, lokacin dare ya riga yayi, atsaitaye Yadikko sukama Ammi sallama yayin da take ta mata Allah ya huta gajiya, bayan sun fita ta kalli inda Rahma take ta dauke kanta adaidai lokacin da Unaisa ke fadin, ” Ina wuni Ammi?
Cikin daure fuska sosai Ammi tace, ” bazan Amsa ba Rahma, ai kin nuna min iyaka ta, ki tashi kiban guri.
Sunkuyar da kai Unaisa tayi tare da face, ” Ammi kiyi hakuri, shine yace fa In fitan mishi a gida fa.
Da ya gaya miki haka da ina da mutunci a idon ki aini zaki fara gaya mawa?, yanzun inda Afnan ce haka ta faru gare ta ina zata je?
Ammi ce ta wurgawa Unaisa wannan tambayan?
Jikin ta sanyin sosai tace, nan “
Toh ke meya hana kizo ki gaya min, ko ana nuna miki wani banbanci ne a tsanin ku?
A’a Kiyi hakuri dan Allah Ammi.
Haba Rahma, kinban mamaki wlh, raina ya ɓaci, na nuna ma Modibo kin kyauta ne kawai sabo da yabar wannan saran Amman Sam abun bemin dadi ba, duk ranar da kika kara min haka bazan yafe miki ba.
Hawaye Rahma ta share ganin inda ran Ammi ya bace, sai dai Modibo na shigowa shima sai taga Ammi ta kara hade ranta, zama yayi shiru bayan wani lokaci yace Ammi har yanzun baki huce bane, gafa Rahma.
Aini matsalar ta kabar furta wannan kalmar kawai ban sonta.
Insha Allahu Ammi nabari.
Addu’a Ammi tai masu sannan tace su tashi suje su huta, Modibo ne ya fara mikewa yayin daya tsaya yana kallon Unaisa dake kokarin mikewa.
Gaba ya sata sannan sukama Ammi sallama, koda suka koma dakin su kai bakace sune sukayi faɗan nan ba, raba dare sukayi suna more junan su yayin da zuwa wannan lokacin ta fara sakin jikin ta dashi.
Sosai Ammi ta dage mishi da magani ganin yabarcin abincin gida Safna gafara data hankalin ta, domin ta riga ta fara amfani da maganin,
kuma ance karta cire rana gashi yau har sati biyu kenan baya cin abincin kowacce cikin su kamar yadda Ammi ta bada Umarni.
Rahma ma taso ta tada hankalin ta ganin yabarcin abincin nata, sosai abun ya dameta, duk da bata son kaima Ammi karar sa wannan karon saita tsintan kanka da gayawa Ammi.
Nan Ammi ta rarrasheta tare da cewa wata matsala ce naga tason kunnu kai yasa nace yabarcin abinci ko ina nan da wani lokaci komai zai daidaita.
Tunda taji haka ta kwantar da hankalin ta, haka har aka dauki tsayon wata uku, zuwa wannan lokacin abubuwa da dama sun faru ciki harta karin auren Suraj, da Rahma akwai komai na bikin duk da cewa tayi nauyi, har yanzun bakin haushin Suraj ɗin take, ko gaisuwa bata hadu, tun yana ganin abun wani iri har ya saba.
Yadikko kuwa har yanzun ciwonta na nan tayin shi atsaitaye dan haka duk ta rame ta lalace, gashi yanzun duk ciwon da zataji bata kwanciya duk cikin kokarin nunawa mutane bata da damuwa.
So da yawa Suraj da Daddy su Suraj din suna yawan kamata tana kuka saidai da an tambaye ta saitace abune ya faɗa mata ido, sosai hakan ke daga hankali mukusan tan da.
*****
Cikin Unaisa yayi tsini sosai, ayanzun daker take zama daker take tashi, bata da wani buri ayanzun daya wuce sauka lafiya, balakin kosawa tayi ta haihu hakama Modibo dauki suke yi sosai duk wani abun bukata na haihu Ammi ta tanada, itako Safna akullum muguwar addu’a kawai take ma cikin.
Misalin ƙarfe bakwai da rabi na safiya Modibo na kwance yayin da kan Unaisa ke kwance akirjin sa yana shafa gashin kanta tare da lumshe ido.
Wayar Modibo ce tai kara dan haka yai saurin dubawa, Ammi ce dan haka yai saurin dagawa.
Shiru taji yayi sai dai har yanzun bebar wasa da gashin kanta ba.
Zuwa can taji yace, Subuhanallahi tare da zame hannun sa daga kan Unaisa.
Cikin sauri ta tashi zaune, kusan a tare suka tashi yayin da Unaisa tace menene?
Tsaki yaja, sannan yace, Yadikko ce babu lafiya, gata nan ma wai an kawota gurin Ammi.
Runtse ido tayi sannan tace, Allah sarki.
Tsaki Modibo ya sake ja sannan ya mike yasaka jallabiya, harya nufi kofa taga ya tsaya yana rike da kofar tsayon lokaci har tagaji tace, Hamma yadai?
Cikin sauri ya waigo ya kalleta sannan yace ba komai, cikin dakin ya dawo yana fadin ki bani key mota, dauka tayi ta mika masa sannan ya juya ya fita.
Yana fita tai tunanin zuwa taga jikin Yadikko dan haka tayi wanka ta shirya cikin duguwar riga me faɗin, karamin hijjabi ta sanya sannan ta daga waya ta kira Modibo.
Bugu biyu ya dauka saidai taji kamar akan hanya yake dan taji karan motoci.
Hamma Modibo nima inzo in gaida Yadikkon?
ajiyan zuciya yayi sannan yace kije, Ni bana nan nama fita, kiyi zaman ki acan har in dawo.
Bakayi wanka ba fab Amma kadawo kayi wanka mana.
Ai nayi Nisa Unaisa.
Ina zaka ba kace yau ba inda zaka ba?
Kamawa tayi, ninama fara fita daga cikin Abuja yanzun haka?
Zuwa Ina Hamma?
Zan nemo ma Yaddiko magani, kimin addu’ar samun nasara.
Toh Hamma Allah yasa adace”
Amin
Ka’ida Suraj ne?
Ni daya ne, ba wadda yasan natafi, karki gaya ma kowa kinji?
Toh yau she zaka dawo?
Yau ɗinan insha Allahu.
Da haka sukayi sallama ta nufi ɗakin Ammi, Yadda taga jikin Yadikko Abun babu daɗi, saidai bayan Ammi taita mata fada ta fara sakin jikin ta har tana dam saka baki a hirar tasu.
Unaisa najin yadda Ammi keta cigiyar Modibo, kuma kowa ya kira shi wayar shi kashe har dare, lokacin duk su Suraj da Magaji sunzo ganin jikin Yadikko harda Muftahu, Afnan ma tun rana take gidan itama tana dauke da cikin ta, Kabir take ta jira yazo su tafi, hira ake adakin Ammi sosai yayin da jifa jifa Yadikko na saka baki.
Misalin Ƙarfe 08:00pm Modibo ya dawo tunkan ya shigo Magaji ya leko ta window sannan ya juya yana cemasu Ammi ga shinan ya dawo, juyowa ya karayi inda ya hangi motar Daddy su Suraj ya faka motar sa a bayan ta Modibo.
Komawa Magaji yayi ya zauna yana cewa Gama Daddy nan yazo.
Ammi ce tace nidai yabar min ita nan ta kwana biyu.
Adaidai wannan lokacin Modibo ya shigo, kaucewa yayi ya koma gefe nan Dada ta bayyana Hannun ta rike da wata bakar jaka me dan karan kyau.
Sosai kowa ke mamakin ganin Dada, Shigowan Daddy su Suraj yasa su Magaji mekewa suna kokarin fita yayin da Daddy yace a’a duk su zauna kawai.
Zama Sukayi gaba daya yayin da Daddy yace, Modibo ina jakar?
Daukan Jakar Modibo yayi agaban Dada ya mikawa Daddy, shima Daddy daukan Jakar yayi ya isa gaban Yadikko ya ajiye tare da fadin, kinsan wannan jakar?
Cikin ya mutsa fuska Ammi take kallon jakar zuwa can ta girgiza kai alamar a’a
Baki santa ba?
eh ta waye ne?, Yadikko ta tambaya.
Girgiza kai Daddy yayi tare da fadin, bude ciki dai ki duba.
Cikin sauri tasa hannun ta ta bude zif din dare dasa hannun ta ta fito da kayan dake ciki tana warewa, kayan jarirai ne masu dan karan kyau, daga kayan Yadikko take da kawar warewa juya kayan tayi sannan ta daga wata farar riga me dan karan kau cikin sauri Kum ta juya tai saurin kallon Suraj…..
13 comments