Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 50

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 50

Kamar yadda Yadikko ta daga kanta ta kalli Suraj shima haka ya bita da kallo, rigar dake rike a hannun ta tasake kallo sannan ta kuma kallon Suraj, zuwa can kuma ta aje kayan ajikin ta, ta ɗebe wasu , tasss ta fito dasu, yayin daga can karshe ta hangi wani zanin da bazata taba mantawa ba, kokarin mikewa take cikin rikecewa gaba daya ta rasa a inda take, gani take kamar mafarki take yi ba gaske bane, muryan ta cike da tsananin ruɗewa tace, ” Alhaji ina ka samo wannan kayan?, da wannan zanin ina ka gan su?, jaririna fa?, ina yake Alhaji?, ina aka ga kayan ba’aga jaririna ba?, ko mafarki nake yi ne?,, ku girgizani in farka…..

     A’a banason haka, dakata ba mafarki bane, idon ki biyu, ki maido da nutsuwar ki jikin ki kinji abin da zan gaya miki.

      Tuni hawaye suka fara biyo fuskan yadikko dan haka Ammi tai saurin zuwa ta rike ta, Modibo ma yana rike da hannun yadikko yake faɗin Yadikko ki nutsu mana.

          Ammi ko juyawa tayi ta kalli Alhaji tana fadin, Alhaji kasamu a ruɗa ni, kayan nan daga ina?, Moh’d ya kawo su?, ko kuwa yaya akayi, ni kaina naso in shaida kayan nan, wannan kayan da irin so akai goyon Suraj, ko Basu bane toh hakika sunyi kama sosai.

       Gaba daya dakin hankalin su nakan Yadikko da take a rikice sai faman zare ido take yi.

       Daddy Suraj ne yace, Tabass domin wannan kayan tun na Suraj ne mafiya ta ta sawo su ba yan kasan nan bane.

       Alhaji ni wai daga ina kayan suka fito?

    Yadikko ce tace Moh’d ya kawo yana son ya karasa ni, Moh’d ya dage sai ya tura min bakin cikin da zaiga bana raye….

    A’a Ba Moh’d bane Daddy ya faɗa yana kallon cikin idon yadikko, juyawa yayi ya kalli Modibo yace, Modibo ina hoton da kace min akwai?

     Hannu Modibo yasa a aljihu ya ciro hotuna guda Uku sannan ya cire daya ya maida biyu Aljihun sa, Daddy ya mikawa Hoton bayan Daddy ya kalla ya mikawa Yadikko.

        Kyakkyawar jaririya ce me sanye da wannan kayan dake hannun  yadikko  kwance kan zanin dake hannun yadikko, cikin sauri Yadikko ta dago irin kayan dake jikin jaririyar sanda akwai hoton ta rike tare da ware zani ɗaya wadda akai hutun dashi ta rike tam a hannun ta tare da kara zubawa hoton ido.

      Zoben zinari guda biyu dake yatsun jariyar ta kula dasu, daya zinari daya a zurfa, nan ta tuna da zoben suma duk na Suraj ne, nan take ta tuna da inda ta aje zoben a wancan lokacin dan haka ta nufi jakar can cikin ta ta bude wani zip saiga dan karamin akwati ya bayyana, ciroshi tayi tana kallon hoton tana kallon zoben, yayin da idon ta ke zubar da hawaye,  bulin kunnen yariyar ta kalla sannan ta sauke idonta a kafar yariyar tare da ya tsun hannun ta gani tayi suna tsananin kama dana Moh’d dan haka ta dago tana fadin, Moh’d ya min karya, mace na haifa amman yace min na miji ne, macece ‘yata ce wannan ina zan ganta, Alhaji ina zan ganta?

     Kowa Adakin a birkice yake, tuni Afnan ta mike tsaye sabo da tsananin tausayin Yadikko, Unaisa ko ta kasa tashi sabo da inda cikinata yai girma sosai, amman tunda taga Yadikko ta rikice tun farko nan ta fara kuka har yanzun bata bari ba, balakin tausayin Yadikko takeji ta rasa dalili hakan, sosai damuwarta ta taɓa zuciyar Unaisa, har takan tambayi kanta meyasa lamarin Yadikko ke damun ta fiye da lamarin kowa, wani lokacin boye soyayyar ta take ga Yadikko dan gudun kar a ga ta cika shishigi, shiyasa tun lokacin da Suraj yai mata masifa ta rage shige mata, dan haka yanzun ma da takejin sautin kukanta ta rasa inda zata sa kanta.

          Muryan Ammi taji tana fadin, “Alhaji kai ma baya ni muna cikin duhun kai, dan Allah ka warware mana Abun da ka sani.

      Daddy Suraj ne ya juya ya kalli Modibo, Modibo ma kallon Daddy yayi sannan ya saki hannun ya dikko dake rike cikin nashi ya zaga bayan Yadikko da Unaisa ke zaune ya mika hannu ya roko hannun ta tare da fadin, ” taso”

     Ɗagowa tayi ta kalleshi, idonta na zubar da hawaye, kallonta yayi sannan yace, Kuka kike yi, taso taso ki gani.

    Da taimakon sa ta mike sannan ya zagayo da ita gaban gadon, suna tsaye saitin kafar Yadikko ya mika hannun sa ya riko na Yadikko yasa na Rahama  tare da fadin, ga ‘yarki nan agaban ki Yadikko yau kukan ki ya kare.

     Axabure Yadikko tago ta  kalli yariyar dake tsaye a gabanta, batare  da wata wata ba ta jawo Unaisa ta faɗa jikin ta  cikin tsananin rikicewa take fadin, Rahma kece?? taba Unaisa take ko ina take dubawa tana fadin Rahma?  kece wannan jaririyar?  innalillahi wa’innalaihir raju un, tabbas ko da ban shaida ki ba kaunar da nake miki ta isa.

      Kowa Adakin zare ido yayi itako Ammi baki ta kama cikin tsananin mamaki, shiko Suraj hannu sa biyu ya daura aka yana kiran sunayen Allah.

      Sosai Yadikko ta ƙanƙame Unaisa, itama Unaisa runtse idonta tayi tana tsiyayar da hawaye, dadi takeji sosai data jita jikin Yadikko, yayin da take jin yadda Yadikko ke roƙurƙumar ta tare da sunbatan ta kota ina, bazata iya musawa cewa ita ɗin ba ‘yar Yadikko bace, domin ta kallah hoton dake hannun Ammi ayanzun hoto ta ne tana karama, sannan shaidu duk sun nuna amsan wannan suturon wadda ta dad’ɗe da sanin kayanta ne na jarirantaka, ita kanta tasha mamaki tunda ta mallaki hankalin kanta cewa Ina Baffa da Innawuro suka samu irin wannan kayan, saidai takan watsar da zancen ne idan ta rasa wadda zai bata amsa, sannan ta tuna yadda mutane ke gudunta, yayin da dayawa suke cewa ita ɗin aljanna ce kawai dan suna ganin ko kusa batai kama da su Baffa ba.

    Kuka Unaisa take ajikin Yadikko, haka itama Yadikkon

    Ammi ko tana rike da Yadikko har yanzun itama hawaye take sharewa tare da fadin, toh ya isa haka, saketa kin matse ta kuma kinsan ba ita kadai bace.

Modibo murmushi yake yana binsu da ido, yayin da hawaye ke sauka akan fuskan sa batare da yana sani ba.

    Kusan kowa na dakin saida yai kuka cikin harda Dada tabi Yadikko da ido tare da kallon tausayi.

     Ganin Yadikko ta kasa sakin Unaisa Ammi ta mike zuwa can ta dawo hannun ta rike da hotuna, haɗawa tayi ta kara da hoton Unaisa dake hannun ta sannan ta matso tan nunawa Unaisa tare da fadin kalli nan Unaisa wannan hoton Suraj ne ne kalle shi sannan kiduba hotun ki kina karama kayan Suraj ne a jikin ki.

       Kallon Hutun Unaisa tayi yayin da hawaye kebin kumatunta kamar an bude famfu.

Hutunan na rike a hannun ta juya da kalli Dada tare da fadin, Dada daman basu Baffa bane suka haife ni?

     Basu bane Unaisa, dukkan alamomin sun tabbatar da hakan, ga mahaifiyar ki nan kusa dake, ko tantama bana yi Unaisa, Ni kaina nasan cewa ba Innawuro bace ta haifeki ki Unaisa, domin lokacin innawuro harta durkusa sabo da tsofa, kuma Babu Labarin cikin babu naƙuda, ‘yar kawai muka gani, daya yawan mutane suna kawo misali da tufafin da ake saka miki alokacin kowa ya kalli kayan yasan kaya ne da suka fito daga wani guri me daraja, beyi kama da namu na yaku bayi ba, dan haka ma da su Innaworo suka nace cewa su suka haife ki wasu ke cewa kila aljanu ne suka basu ke.

        Modibo ya fara min wannan mgnr tun ranar da sukazo suka tafi dake da daddare ya kirani, nan ya bani labarin batan ɗan Yadikko, sannan ya gaya min zargin sa, naso in Musa amman nima dai irin tunanin nasa nayi daga baya, domin Tabbas a da Baffa yayi wanki da goga, kuma tundaga ranar da jama’a sukasan dake acikin gidan be sake zuwa kasuwa ba, sabo da yadda jama suka nuna masa tsangwama dan haka ya canza sana’a.

         Har yanzun da yawa kuka akeyi adakin, Itako Ammi tana kukan take buga waya tana gayawa mutane yan uwa da abokan arziki, nan danan saiga Abba ya shigo yanayiwa Allah godiya, Mai martaba kuwa waya ya bugo yaiwa su Ammi murna sannan yace ya nan zuwa.

      Cikin kankanin lokaci gidan ya fara cika duk da cewa dare ne, abokiyar zaman Yadikko ma tazo  kowa taya Yadikko Murna yake, Sai kusan sha daya sannan aka fara ragowa, Daddy tare suka tafi da abokiyar zaman Yadikko Hajiya Binta yayin da Ammi ta roka abar Yadikko ta kara nutsuwa da ‘yarta

Ayanzun dakin ya rage daga Ammi sai Magaji Modibo Muftahu da Suraj, sai kuma su Yadikko da har yanzun suke makale da juna.

      Suraj ne yai murmushi tare da fadin,” toh Mama yau dai hankalin ki ya kwanta, har yanzun ɗimin jikin ta be ishe ki bane?, ki barta mana haka?

     Ammice tace zaka fara ko?

   Toh Ammi kina gani fa, wlh saikin mata faɗa yanzun zata dinga nuna fifiko.

    Dariya Ammi tayi tare da fadin, ” saika dinga kawar da kanka.

      Komawa Modibo yayi ya zauna tare da sauke ajiyan zuciya sannan yace, Bazai iya ba Ammi kishi gare shi kamar mace.

      Magaji ne yai wata muguwar dariya duk dakin saida aka kalleshi Ammi ce tace lafiyar ka?, menene haka?

      Ammi Suraj da Modibo sunce duk ranar da aka ga jaririn ki sai sun nannaushe shi,

Dariya akayi yayin da Modibo ya mike ya dube Unaisa yana murmushi tare da fadin, ” Toh ni dai zanje in huta yau ko wanka banyi ba.

     Yadikko ce ta saki Unaisa tana fadin tashi ku wuce.

    A’a Yadikko ki barta ta kwana anan.

    A’a sam Modibo bazai yiyuba kuje abin ku.

    Ammi ce tace ki barta mana kai jeka abun ka Allah yai maka Albarka.

     Juyawa yayi, yayin da Suraj ma ya mike Yana fadin, nima zan wuce asamin albarka.

      Albarka Ammi da Yadikko sukaita sa masu, gaba dayan su suka fita dakin ya rage daga Ammi sai Yadikko da Unaisa.

       Har wannan lokacin Yadikko kallon Unaisa takeji tare da wani irin soyayyar ta dake shirta, haka itama Unaisa anata bangaren sosai takewa Yadikkon kallon uwa mahaifiya dan hakama ta kasa daina kuka.

     Ammi ce ta dube Unaisa dake share hawaye tace, ya isa haka Rahma, wannan ai abun farin ciki ne bana kuka ba, wannan ikon Allah ne, shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, gashi Moh’d ya rabamu dake bayan kin girma kuma Allah ya gwada mana ikon shi, bayan sakoki cikin mu kuma ya kulla aure tsaftatacce tsakanin ki da Modibo tare da wata irin soyayya me zafi da kukewa junan ku.

    Yadikko ce ta kama fuskan Unaisa tana share mata hawaye take fadin, kiyi hakuri kinji, Mahaifin ki cemin yayi namiji na haifa, beko bari nasaki cikin idona ba, ya rabani dake, hawaye ta share na tsananin tausayin Unaisa sannan tacigaba da cewa, ” mahaifin ki shine yai miki haramiyan nonon mahaifiyar ki, nayi bakin ciki nayi kuka idan naji nunuwa na na zubar da ruwa babu abun da na haifa, dan haka bazan taba yafewa Moh’d ba, amman ke ruwan ki ne kiyafe mishi ko akasin haka.

       Ammi ce tace a’a kibar wannan zancen, ya kamata ma asanar masu, koda mahaifiyar tashi ce a gaya mata.

      Karki gaya musu ki rabo dasu kawai.

   Baza’ayi hakaba Ammi ta fada sannan ta daga waya ta kira Yasmeen wato mahaifiyar Moh’d kakar Unaisa.

    Sosai mata ta nuna zallar farin cikin ta, sannan tace gobe da safe suna nan zuwa.

                        *****

Safna kuwa tukan Modibo ya isa Momyn ta ta sanar mata, wannan labarin sai yafi labarin cikin Rahma kona ran Safna, kuka taci ta koshi lokacin da Momy ta sanar da ita gobe memartaba zai taso musamman yazo ganin Rahma.

     Wannan abu ya tashi hankali Safna da mahaifiyar ta, domin kowa yasan yadda dangi suke bakin cikin muguntan da Muh’d yaiwa Yadikko, yanzun Rahma ta zama yar gata, gobe zava taho daga Kano mota mota ganin Rahma, ciki harda me martaba, tana tsaka da wannan tunanin Modibo ya shigo, daka ganshi kasan yana cikin farin ciki.

          Suraj ko bayan ya koma gida kasa kwanciya yayi, balakin mamaki ne ya rufeshi dan haka yaita zaware a cikin dakin sa, farin ciki yake ji sosai saidai wani lokacin wani dan karamin tunani na bata farin cikin nasa, ganin ya kasa kawar da tunanin ya yanke shawaran kawai zai tuntubi Yadikko da zanjen.

                          ****

   Yadikko da Unaisa kwance kan gadon Ammi, kan filo daya suka kwanta, tuni Unaisa tai bacci sai ajiyan zuciya kawai da take saukewa, Itako Yadikko kwance take tana fukantan Unaisa idonta kur kanta, yau sam bayanin bacci yayin da ta rasa wanni irin farin ciki take ciki, Ahankali ta dago ta subaci Unaisa dake bacci tare da fadin, Allah yai miki Albarka Rahma, Allah kuma ya sauke ki lafiya ya saukaka miki naƙuda.

     Idon Ammi cike da kwalla tace Ammi ita kanta ta kasa bacci yau sai sauran kallon su take tana kwance kan kujera…..

     Wayar Ammi ce tai kara, mikewa tayi duk da dare yayi amman tasan be wuce tayasu farin ciki ne, bakuwar Number tagani Kamar baza ta daga ba sai kuma ta daga.

      Wata murya taje wadda yasata faduwan gaba dan haka bata iya amsa gaisuwar da ake mata ba tace, ” dawa nake mgn.

       Jimmm yayi Sannan yace Nine”

     Kaine wa?

6 comments

  1. Pingback: plinko
  2. Pingback: นิยาย
  3. Pingback: Brians Club

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *