Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 9

Posted by

BA LABARI BOOK

 

 

BA LABARI BOOK 2
By
Fadila Lamido

EXQUISITE WRITER’S FORUM.

page

 

Kallon ta Safna taitayi tana kallon yadda hawayen ta ke jika hijabin ta, wani farin ciki taji cikin ranta ganin inda yasata ta zube akasa.

Basai an fada mata ba tasan itace amaryar tasa, tunda take da Modibo ta sani mutum ne wadda baya son raini, me jajircewa ne idan yaga za’a taba masa mutuncin sa, tana masa laifi yaita fada da hargagi amman be taba cewa tasa guiwarta akasa ba, dan haka wannan yasata tunanin bawani son yariyar yake ba, inda yana sonta ai Amarya bata laifi.

Wasa da hannu Unaisa keyi har yanzun hawaye na zubo mata, Safna banda murmushi babu abu da take yi tare da kallon farin hannun ta da take lankwasawa.

Tsawon lokaci ta dauka ahaka fin awa daya suna a haka.

Zuwa wannan lokacin Safna har dariya take fitarwa me d’an bada sauti wadda ke nuna alamar tana cikin farin ciki.

Zuwa can Modibon ya fara motsowa da alama bacci yayi.

Safna ce tai saurin lalobo hannun sa tana fadin Hamma sannu ka tashi?

Shima rike hannun sa yayi cikin nata tare da motsawa yana kokarin tashi zaune, da alama ya manta da ita agurin sabo da irin kallon da taga ya mata, kawar da kanshi yayi kadan sannan ya mike ya nufi toilet.

Ya jima aciki zuwa can taji fitowan sa, ta bayanta yabi ya wuce tana jin motsin sa a bayan ta tsayon lokaci ya dawo bakin gadon ya zauna tare da fadin, ” Safna kiban waya na.

Mikewa tayi zuwa gefen gadon ta Mika masa ya amsa dannan wayar yayi tare da fadin, “ke tashi ki tafi”

Ko motsi batai ba tsayon lokaci ahankali ya sake cewa kije nace ko, bakomai ai hankali ke gane Ido gululu ne.

Wannan karon ma Bata motsa ba, cike da haushi Safna tace, ” kinaji fa yace kije.

Tamkar ma matajin me suke ciwa haka ta yi, bude baki Safna ta sakeyi da nufin mgn Modibo yai saurin cewa, ” rabu da ita, miskilancin tane ya motsa, kinsan me hali bashi barin hali.

Gum tayi, sai dai wani irin kallo take binta dashi me cike da haushi.

Wayarsa yake dannawa tsayon lokaci sannan ya dago ya kalli Unaisa tare da daga idon sa ya kalli agogo, shabiyu saura ya gani dan haka ya sake kallon Unaisa da dan sakin fuska kadan yace, Rahma kije nace ko.

Wasu hawayen yaga ya sake d’igowa Kan hijabin ta dan haka yai saurin kallon Safna yace, jeki Ina zuwa ganinan fitowa yanzun.

Wani haushi ne ya turnuketa sosai, mikewa tayi ta fita ranta ba haka yaso ba.

Unaisa najin Karan buga kofar da Safna tayi ta dago kanta ta kalleshi tare da saurin mayarwa ta sunkuyar da kanta.

Mikewa tayi Yana binta da kallo ta karasa gaban shi ta tsuguna tare da sunkuyar da kanta kasa.

Cikin Mamaki yake kallon ta tare da rasa manufarta ta zuwa gaban shi kotana nufin gata in karasa ta ne, ni zata ma taurin kai kokarin hasala yake yaji kafar sa cikin hannun ta.

Wani irin abu yaji wadda yasashi lumshe Ido batare daya shirya ba, zuwa can ya bude idon sa akan hannunta dake rike da kafar sa.

Kayi hakuri dan Allah, ka yafe min, wlh bada gangan nayi ba, bani da kowa aduniyar nan sai Dada, ita Innawuro tabawa amanata, ita kuma Dada tabaka, bansan kowa ba anan sai kai, taya zan maka hakan.

Cikin kausarsiya muryan sa yace ai nima d’in baki sanni ba tunda kinsha kawo min hari ba wannan bane na farko.

A hankali tace, ” kayi hakuri na sanka rikice min kuke yi.

Jimmm yayi Yana sauke ajiyan zuciya, sosai ya kosa ta sakar masa kafa dan yarasa da wani suna zai kira abin da yakeji sakamakon rike kafar tasa da tayi.

Shikenan naji, sake min kafa ya fada yana kawar da idon sa daga gare ta.

Ahankali ta zame hannun ta yayin da taji yana fadin, “shi Magajin me ya miki da baki da wani buri sai nakiga kinji masa ciwo?

Gabanta taji ya fadi, saidai batasan da yadda zata gaya mishi ba, jinta shiru ya sake cewa, ” me Magajin ya miki kike son nakasa shi?

Shine yake yawan zare min ido, kuma ranar nan….

Shiru tayi ta kasa karasawa.

Inajin ki ranar nan d’in meya faru.

Nida Afnan ne da zamu fita, naga yana dingishi saida muka dawo na tambayeta sai tace min bakai bane.

Jimmm yayi sannan yace kinga Yana d’ingishi??

Eh, ta fada a hankali, shiru ya sakeyi tsayon lokaci sannan yace shikenan jeki.

Mikewa tayi ta juya tana kokarin fita taji yace, ” zo”

Juyowa tayi, cikin idonta ya kalla sannan yace, ” ai kina tare da Afnan lokacin har kuka dawo gida ko?

Jimmm tayi sannan tace, ” eh ”

Da hannu yai mata alamar ta tafi saidai ya shiga damuwa sosai.

Daker da tagane hanya dan gidan girma garai sosai, tana tafe tana share hawaye yayin da abu biyu ya tsaya mata azuciya, yadda ta kasa gane Magaji da ta nufi yi masa abu saitama Modibo, wannan ke matukar kona mata rai, sai abu na biyu wadda take ta kokarin kore shi azuciyarta saidai yazo ya tokare mata kahon zuciyar ta.

Sabo da yadda abun ke Kona mata rai wata zuciyarta ta shiga tambayan ta, yaushe Kika fara shiga mutane?, Har yaushe aka fara miki kallon mutum dahar wannan zai bata miki rai, ki share kawai.

Yin wannan tunanin yasata share hawaye sannan ta nufi part din Ammi.

Bata shiga dakin Ammi ba nasu ta wuce, toilet shiga tai wanka sannan ta ta fito har yanzun idonta yaki barin zubar hawaye.

Wata riga tasa doguwa daga cikin kayan da aka dinka mata, komai bata shafa ba ta gabatar da sallar azahar sannan ta fada kan gadon.

Kwance kawai take hawaye na zobo mata tana gogewa tunda ta kwanta sallah kawai ke tadata.

Sai bayan magariba Afnan ta shigo ganin Unaisa kwance taji mamaki yaushe Kika dawo?

Tun da rana ta bata amsa batare tabari sun hada Ido ba.

Ya dake ki ne?

Wannan karon ma dakai ta Bata amsa.

Ficewa Afnan tayi zuwa can ya dawo tace, Ammi tace kizo.

Mikewa tayi tana jin kanta Kamar zai fado, dakin Ammi ta nufa, itama Ammi tambayan ta tayi ya daketa ne?

Girgiza kai tayi tare da share hawaye .

Cikin rarrashi Ammi tace kwanta nan Kan gadon ki huta.

Abinci aka kawo mata saidai tagaza saka komai a bakin ta.

*****

Daker Ammi tasata ta danci sannan ta koma gadon ta kwanta, Ammi da Afnan ke dan taba hira sama sama, wayar Afnan ce tayi kara wayar ta kalla sannan ta kalli agogo tare da fadin, Hamma Modibo ne, lafiya kuwa?

Wayar tasa a kunnen ta tare da Sallama.

Jimmm, tayi alamar tana sauraron sa, zuwa can tace, “eh yadai turani gidan su Hamma Muftaho in karbo masa sako kafin nazo gidan nasame su.

Shiru ta danyi zuwa can tace, ” eh”

Sauke wayar tayi sannan ta mike tana cewa Ammi Bari muje mu kwanta.

Kije ki kwanta kibar min Rahma anan dan fuskan nan tata kunburi take kila ta kasa bacci.

Sallama tayi ta fice, Unaisa kosan daga kanta bata yi, sabo da tsabar radadin da yake mata, bacci ne ya dan fara daukan ta cikin baccin ta taji Muryan Safna tana fadin, kina ji ai?

Afirgice ta bude idonta Bata san meyasa ba wannan kalamin ke kona mata rai, sosai takejin ta tsana Safna, tun daga lokacin Bata iya komawa Bacci ba, kalmar nan daya keta mata yawa cikkin kanta, abun da yafi Bata Mamaki ansha gaya mata bakaken mgn na batanan ci tare da kyara da cin fuska amman bata tabajin haushi ba kamar yadda taji haushi wannan kalmar ta matar Modibo, duk da cewa tasan mgnr da ya fada ne ta maimaita mata.

Duk Abin da take Ammi na kula da ita, saidai ita tunanin ta fuskarta ne ya hanata bacci, dan haka tace cikin ranta da gari ya waye za’a kaita Asibiti.

Misalin daya saura ta kula bacci ya dauki Unaisa, mikewa tayi ta rage wutan dakin sannan ta kwanta, har bacci ya fara daukanta kara waya ya tashe ta, tashi tayi zaune cikin yanayin bacci take laluban wayarta, gani tayi ba tata wayar bace dan haka ta kalli Inda Unaisa ke kwance.

Hasken wayar ta hanga gefen Unaisa dan haka ta mike cike da mamakin Kiran wayar cikin dare, kallo wayar tayi sunan Modibo ne baro baro akan wayar harzata dauka sai kuma ta fasa tare da mayar da wayar ta aje gefen ta sannan ta koma ta kwanta.

Tanajin wayar harta katse sannan ta kuma daukan kid’a, tana daga kwancrn ta fara Kiran Rahma! Rahma!

Amsawa tayi yayin da Ammi tace dauki wayar ki a na Kira.

Tashi tayi a matukar firgice dan daukan ta Dada ce, domin da ita kadai take waya, lokacin da take tsaka dataji muryan Dada saita tsinci muryan Modibo a dake yake fadin, “ki gaya min abun da kike boye min?, Ranar da Magaji ya dauke ku keda Afnan ya sauke Afnan ahanya ke ya tafi dake, Ina ya kai ki??

Gidan da zamu ne kawai bayan nan babu inda mukaje, ta tsinci kanta da gaya masa haka.

Sai yace miki me a hanya??

Wlh bece min komai ba.

Jimmm yayi tsayon lokaci sannan yayi kasa da murya ahankali yace, naji na kuma gamsu da hakan, bekai ki ko Ina ma kuma bece miki komai ba, Amman ya taba jikin ki.

Cikin sauri tace a’a fah.

Wani uban tsawa ya buga tare da fadin, ” karki raina min hankali, ni ba yaro bane karami koya aka min karya Ina ganewa, bama wannan ba, kewai shashar inace?, Kina da hankali kuwa?

Yadda yake mgnr kamar zai fasa mata kunne yasata rikecewa sosai kukane keson kubuce mata cikin sauri tasa hannun ta ta toshe bakin ta, sai dai kuma tuni Ammi ta fahimci kiran bana dadi bane domin tajin sautin sa da karfi cikin wayar saidai Bata gane me yake cewa.

Wayar na rike a hannun ta yayin da take kara karfin kukan ta, ganin haka Ammi ta mike ta karbi wayar daga hannun Unaisa tasa wayar a kunnen ta cikin fada take cewa Modibo menene haka?, sabo gudun irin haka naturo maka ita, ashe duk be ishe kaba, saika saika hanata bacci cikin dare dan masifa.

Ammi ba wannan bane bari kiji.

A’a bazanji ba Modibo, dare ne yanzun kabari Saida safe….

Ammi barin gaya miki Mana.

Nace maka kabari ko, kashe wayar tayi gaba daya cikin yanayin dake nuna tana cikin bacin rai, ajiye wayar tayi sannan ta kalli Unaisa tace kwanta abunki, tunkan ta rufe baki ta hangi wayarta nakara tana dosan ta gane Modibo ne daukan wayar tayi itama ta kasheta baki daya tare da fadin, ” matsalan Modibo kenan”

Kwanciya tayi tare da kallon Unaisa tace, kwanta kijin da safe zamuje asibiti..

Batakai ga rufe baki ba suka fara jin ana dokan wata ko daga cikin gidan, zubur Ammi ta tashi zaune tana kara baza kunnen ta, Magaji!! Magaji!! Sine abun da taji ana fada tare da dukan kofar da karfin ta yadda duk wani dake cikin gidan duk nauyin baccin sa saiyaji yo amon Kiran sunan Magajin.

9 comments

  1. Pingback: pk789
  2. Pingback: Mostbet
  3. Pingback: online casino
  4. Pingback: Ver aquí
  5. Pingback: pg168
  6. Pingback: pizza168

Comments are closed.