Screenshot 20211123 203408 2 1

BA LABARI BOOK 2 PAGE 11

Posted by

BA LABARI BOOK

 

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 11

Zama yayi gefen gadon yayin da Unaisa take zaune a kasa saitin kafar sa.

Hankali yace, ” Aunty ya kike?”

Ji take Kamar an kama bakinta andinki ta kasa amasa masa.

Kallo yanbita dashi tsayon lokaci sannan yace, ” ke! Ji mana”

‘Dagowa tayi ta kalleshi kad’an sannan ta maida kanta da sauri.

Ganin haka ya daga kafarsa ya dunguri cinyanta tare da fadin, “Ke! Mgn nake fa”

‘Dagowa tayi ta kalleshi ta yamutsa fuska sannan tai saurin maida kanta kasa.

Bazaki amsa min ba?

Cikin rawar baki tace, “Ina kwana”

Hmmm, yanzun kwana ne ko wuni ne?, Shikenan, kedai baki da wayau.

Dukar Kai tayi tana Shirin zubo da hawaye gaba daya atakure take.

Shiru sukayi tsayon lokaci zuwa can taji yace, ” toh ya kike?, yau nazo har d’akin ku musamman dan in duba lafiyar ki, na kwana biyu bana ganin ki, me yasa baki zama dakin Ammi yanzun?

Wasa kawai Unaisa take da hanun ta tamkar zata ballah.

Zuwa can taji Yana fadin, ” wanene baki son gani, niko Magaji?

Shiru tayi ganin bazatai mgn ba yashi fadin.

Wato kedai da Afnan kawai Kika saba a gidan nan, da ita kike mgn, shikenan Afnan ta gaya miki gobe zakije makaranta?

Da sauri ta d’aga kanta alamar eh.

Yayi kyau, lokacin da muna yara nida Magaji dakin mu daya kamar yadda kuke keda Afnan, saidai mu bama jituwa, sabo da haka tunkan mu girma aka raba mana daki, Magaji Yana da keta gashi sabo da shigar saurin da yami sai yazamto ni bani da karfi, Ammi tace duka yake min, ni bani da karfi ko na sisi.

Satan kallon shi Unaisa tayi sannan tai saurin maida kanta kasa, yayin da taji yaciga da cewa, ” ban gama mole nonon Ammi ba yai min shigar sauri, hakan yasa naita ciwo kamar bazan yiba, idan fada ya hadamu saiya min duka, wata rana ne nayi zuciya naimasa wani Mummunan cizo a kumatun sa wadda har yanzun tabon sa nan afukar sa, tundaga ranar yake guduna inji Ammi.

Gani yayi fuskarta dauke da Murmushi kanta akasa, leken fuskar yayi tare da fadin, ” “dariya na baki?

Sai alokacin ta kula da murmushin da take batare data sani ba, cikin sauri ta hade fuskar ta.

Murmushi yayi tare da fadin, ” nabaki wannan labarin ne dan ki kara banbancewa tsakanin nida Magaji, a kumatun sa gefen dama akwai tabo sai wadda ya kula yake ganewa.

Sosai taji wani sanyi cikin ranta dan harga Allah har yanzun bata fahimci wani banbancin su ba, kama suke mata sosai.

Saura kuma kibawa Afnan wannan labarin dana baki, taji Yana cigaba da fadin tare da tsareta da Ido.

Mikewa yayi ya fara takawa kamar zai fita sannan ya dawo yace ” bana son fadan da kike hankoron yi da Magaji ki kama kanki ke macece shi namiji ne, ki kama kanki, bana so, bazan sake miki uzuri ba akan rashin gane mu, ya kamata zuwa yanzun ki fara wayau.

Kofar ya tafi ya bude ya fice.

Ji tayi Kamar an kwance ta, mikewa tayi ta isa toilet zuwa can ta fito tana sauke ajiyan zuciya.

*****

Washegari tunda sassafe suka gama shiryawa dakin Ammi suka nufa cikin cikin kayan makaran su.

Masha Allah Ammi take fada ganin yadda kayan makarantar ya karfi jikin Rahma fiye da Afnan, daga can gefen gadon Ammi ta hangi Suraj da Muftahu zaune kowanne kansa nade da rawani cikin shigar alkebba, kallo d’aya ta musu ta dauke idonta yayin da takeji ajikin ta kallon ta suke yi.

Sallama sukawa Ammi akan cewa zasu wuce, Amma Ammi saitace saisun jira Modibo sabo da shine zai mika Rahma makarantar.

Cikin sauri Muftahu yace, “Ammi driver ya kaisu Mana, muda zamu dauki hanya yanzun

Ina zaku Afnan ta tambaya da sauri.

Kano zamu, Mai martaba yayi kira, da tsakar dare mulkin nasa ya ya tashi.

Wlh karkuje, mutumin nan ya cika rigima.

Dariya Muftahu yayi yayi kina ganin ya rikita ‘ya’yan shi tundare suke waya tare da jaddawa atafi da wuri.

Dariya Afnan tayi sannan tace badan makaranta ba dana biku.

Shiko Suraj duk wannan mgnr da ake hankalin sa nakan Unaisa Satan kallon ta kawai yake tare da yaba kyau da Surar jikin ta, cikin ransa yake fadin bantaba ganin mutumin da yake kyau da kayan makaranta ba kamar wannan yariyar, komai nata me kyau ne.

Sai misalin 8:14 Modibo ya shigo shida Magaji Sallama kawai sukama Ammi suka fice, shima cikin irin shirgar su Muftahu ta ganshi.

Suma fitowa harabar gidan Motocine birjik wannan yanayin ya tuna mata da sanda suke bibiyan ta lakaci da tana gidan su, hawaye taji Yana son zobo mata sosai take son gidan su, sabo da yadda take son gidan yasa zaman kadaicin baya damun ta.

Cikin motocin suka fara shiga, lokacin da aka budewa Modibo motar da zaije acikin ta saiyace Afnan da Rahma su shiga shi kuma ya shiga gaba.

Lankwasa Hannu Unaisa taitayi tsintan kanta tayi da faduwan gaba akan wannan tafiyar da zasuyi wata kila dadewa zasuyi Kamar yadda sukayi garin su, hakanan takejin Bata son tafiyar sa, domin anan ganin sa take tamkar Dada, Koda bashine yake kula da itaba tafi son dai ace Yana nan domin koma menene shine ya kawota gidan sannan kuma shine take ganin kadai zai iya maidata gurin Dada.

Har cikin makarantar jerin motocin suka shiga, makaranta ce mekyau da ‘ya’yan manya daganin ta, sakkowa sukayi a gaban wani office umarni yabawa Afnan data wuce abun ta yayin da yacewa Unaisa biyo ni.

Ciki suka shiga da girmamawa suke gaisawa da Modibo sannan sannan aka farawa Unaisa gwaji.

Beyi tunanin zatayi mgn ba dan haka yaso ce masu asata ajin farko kawai, abun da ya bashi Mamaki ji yayi suna jefa mata tambaya yayin da take Basu amsa babu wani inda inda a tattare da ita.

Wani sansamya ajiyan zuciya ya sauke, sabo da yadda take amsa tambayan da ake jefa mata, gaba daya Malam dake wajen guri ta suka isa yayin da ake jefa mata tambayar cikin harcen turancin itama take maida amsa.

Wani irin farin ciki ne ya baibaye Modibo kafin d’aya daga cikin Malaman ya dawo gaban Modibo Yana fadin, Ranka ya dad’e zasu iya tafiya tare da Afnan.

Amsawa yayi ciki da kwarin guiwa betaba tunanin tana da kokari haka ba duk da cewa Dada ta gaya masa tasata makaranta harta kare, lallai Dada tayi kokari yafada azuciyar sa.

Sallama ya masu ya fito, bayan motar da suka fito ya nufa ya zauna yayin da Suraj ya fito a wadda yake ciki ya dawo ta Modibo.

Har motocin su na Shirin tashi ya hange Unaisa tsaya gaban Office din tana share hawaye.

Dakatar da motar yayi sannan ya sauka, ya isa gabanta cikin tuhuma yace, ” menene?

Hawaye ne kawai ke ziraro mata tanasa bayan hannun ta tana sharewa.

Meke faruwa ya fada yana waigen motocin nasu daya kula duk su suka zubawa Ido.

A hankali ta furta Dada.

Runtse Ido yayi sannan yace, “me kike nufi?, Inace kinbar wannan mgnr ashe baki barta ba, mena gaya miki ?, sannan kuma anan gurin ne zaki sa min rigima meyasa bakiyi ba tun agida.

Yanayin yadda yake mata mgnr cikin fada yasa ta fara komawa da baya tare da fashewa da kuka.

Hakalin du su Suraj Muftahu da Magaji duk Yana kansu, yadda suka tsaya agurin sosai abun ke bada sha’wa, Unaisa cikin kayan makaranta siket da kad’an ya wuce guiwarta tare da karamin hijjabi, sai jakar makaranta katowa dake rataye a kafadan ta, yayin da Modibo yake cikin manyan kaya alkebba irin ta sarakai tare da daurin rawani, farin gilashi sanyi a idon sa.

Dukan su farare ne tass ita da Modibo sai dai barin nasu ya banbanta.

Ajiyan zuciya Suraj yayi sannan yace wai kukan me take?, babu me amsa masa dan haka yabisu da ido kawai.

Hakama Magaji da Muftahu Ido suka zuba masu yayin da Magaji yace, iyeee lallai,Muftahu kana ganin ikon Allah ko?

Cike da takaice Muftahu yace, ” Hmmm naga kamar har wani kulawa yake bata.

Ni har yanzun ban yadda Yana sonta ba, inda yana sonta me yake jira, gurin fa Ammi yabarta gaba daya hankalin sa yana kan Safna,

Muftahu ne yace dubi abun da take masa.

Cike da haushi Magaji yace ai munafukar yariya ce, Ina rasa lokacin da Modibo yake mgn da ita, ahaka dai zakaga ba wani mgn suke ba amman muguwar magulmaciya ce.

Modibo kuwa cike da mamaki yake kallon Unaisa ganin bazatabar kukan ba ya rufeta da fada, hawayen ta fara sharewa tana kallon cikin idonshi dayake mata mazurai…