Screenshot 20211123 203408 2

BA LABARI BOOK 2 PAGE 28

Posted by

BA LABARI BOOK

 

BA LABARI BOOK 2
BY
FADILA LAMIDO

PAGE 28

Ganin yana Mika mata hannun sa dole ta Mika masa nata, ta rasa abun da yasa bata iya mishi musu ko kadan.

  Mikewa tayi Yana rike da hannun ta suka fita, sai awannan kalokacin ta kalli falon ta sosai taga gurin yayi kyau ba kadan ba, ratsawa suka yi yayin da Yana bude wata Kofa ta gansu a falon shi,  Safna ta hanga tana Kara jare kuloli.

Har suka isa gurin Safna bata juyo ta kalle su ba, kujera ya jawowa Unaisa ta zauna sannan shima ya jawo daya ya zauna tare da shafa kansa, tun daga goshi zuwa ‘keya, a daidai lakacin da Safna take zama tare da fadin, ” Barka da fitowa”

Cikin sauri ya rike hannun ta yakai saitin bakin shi, ganin haka Unaisa tai sauri ta zame nata, Saida ya sunbaci hannun Safna tare da fadin kin tashi lafiya, ta amsa sannan ya juyo ya kalli Unaisa data dauke idon ta akan su.

   Kallon tuhuma ya bita dashi sannan ya sake kamo hannun nata Yana kokarin hada Ido da ita saidai ita taki Bari hakan ya faru sai kawar dakai take.

      Hannunta dake rike anashi ya mintsina hakan yasa tai saurin kallon shi, ‘kyara mata yayi dakai ta gaida Safna, kallon Safna tayi Kamar zata gaidata sai kuma ta kawar da kanta, dan haka ya kara matsa hannun ta ta sake kallon shi, ‘kyara mata ya sake yi yayin data kawar da kanta.

    Cike da Mamaki take kallon Unaisa yayin da Safna ta take kokarin hada abincin, saidai ya kula itama ko inda Unaisa take Bata kalla ba.

   Duk yadda yaso Unaisa ta kallo gunsa ta dauke kanta, kuma fuskanta daure yake babu alamar fara’a ko jiya da dare bata hada Rai Kamar yadda ta hada yazon ba.

  Komawa yayi ya jingina da kujerar tare da daga hannun sa yana shafa gemon sa Yana ma Unaisa kallon kurulla, ganin taki kallon sa ya juya ya kalli Safna dake ta kokarin zuba abun kari, yayin da tabada hankalin ta gaba daya a gurin, A hankali ya sake maida hankalin sa gurin  Unaisa, gyaran murya yayi sannan yace, ” Rahma!!

    :Dagowa tayi ta dube shi.

  Banji kin gaida Auntyn ki ba?

Cikin sauri ta lumshe idon ta sannan ta bude ta dubi inda Safna take tace, ” Ina kwana”

Cikin murmushi Safna tace, Lafiya, ya amarci?

   Dan sunkuyar dakai Unaisa tayi kadan.

Ajiyan zuciya Modibo ya sauke a hankali sannan ya gyara zaman shi tare da Jan abincin da Safna ta aje mishi sannan yasa hannu ya kara jawo na Unaisa gabanta Yana fadin, ” Bismillah.

  Cukalin ta dauka tana juyawa, Modibo ko shi da Safna abincin suka shiga ci yayin da Safna ke fadin, ” jiya Aunty Khadija tasu ku hadu harta wuce baka shigo ba”

  Tazo ne?

  Ya fada Yana kai lumar bakin shi.

Tazo tama jima anan.

Allah sarki, aida kin kirani ai, na dade ban ganta ba, har yanzun tana tare da mijinta nan ko?

Eh suna tare yanzun yaran ta Uku fah.

Ikon Allah kenan, Allah ya raya su.

   Ameen Safna ta fada sannan ta sake dauko Masa wani hiran, suna yi suna dariya har Modibo ya cinye ya kurbi ruwa tare da goge hannun sa adaidai lokacin da Safna kecewa Kallah Hammana bata ciba fa.

Eh rabu da ita, Ina kallon ta ai, rufe min shi  in dauka, in muje daki saina dura mata.

   Murmushi Safna tayi sannan ta rufa, mikewa Modibo yayi ya kwashi wayoyin sa sannan ya Kai hannu zai dauki abincin tare da Fadin tashi muje.

   Hannun ta tasa ta rike abincin ahankali tace, “zanci “

  Cikin sauri ya cire hannun shi sannan ya koma falon tare da fadin, na baki minti 10

    Murmushi Safna tayi, tanajin su suna hira da Safna hartaci kusan rabi sannan ta rufe.

   Bata jima da rufewa ba Modibo yazo gurin, budewa yayi ya duba sannan yace tashi muje.

Mikewa tayi tabi bayan shi, wannan karon afalon ta ya zauna dan haka itama ta zauna, zuwa can ya kunnan tv sanna ya kwanta jefi jefi Yana kallon ta ya kawar dakai.

   Hakan be bata Mamaki ba domin ta kula dazon yaji haushin ta da bata gaida Safna ba.

  Sun dade ahaka, kuma idon shi biyu ba bacci yake ba, zuwa can taga kiran Afnan ya shigo wayar ta, kin dauka tayi dan bazata iyayin mgn a gaban shi ba, har sau uku ta kira Bata dauka ba sannan ta hakura.

  Zuwa can taji an Kira wayar Modibo, dubawa taga yayi sannan ya kara wayar a kunnen sa yana fadin, ” Afnan ya kike? zuwa can taji ya sake fadin, ” ya me gidan? jimm ya sake yi sannan ya kuma cewa meya samu muryan ki ya shake haka? Kara baza kunnenta tayi saidai babu abun da ta iya jiyowa daga cikin wayar ji tayi yace toh Allah ya sauwakale,  gata.

Mika mata wayar ya shiga yi Yana fadin, ” Ga kawar ki”

  Hannun ta Mika ta amsa tasa a kunnen ta,  cikin shakakkiyarr murya tajin Afnan din tace  Sai Aunty mu, yanzun ne zanfi jin dadin Kiran ki da Aunty dacen Auntyn gwangwani ce ke, karake mgnr tayi cikin bushewa da dariya.

    Unaisa kasa furta komai tayi dan haka tace Hmmm kawai.

   Bangane Hmmm ba, wlh yau kewan ki nake sosai, nayi miss din ki yau banji dariyar ki ta asuba ba banji ta safiya ba, nakira Ammi ma tace Wai yau tayi miss din mu Wai tunda da taji bataji dariyar mu da Asuba ba hankalin ta duk ya tashi, tace ke baki kirata ba.

   Kasa kasa da murya tayi kamar me rada tace zan kirata anjima.

Wai ya naji duk kinyi san yi ne?

Ki Bari sai anjima Unaisa ta sake fada.

  Sannan muyi wayar?

Eh.

Lallai Unaisa nagane wato sabo da Hamma Yana gurin shine bazakiyi mgn ba, lallai kina da aiki, nikuma hira nake son muyi.

  ” Anjima”

Unaisa ta sake fada dan haka Afnan ta kyalkyale da dariya sosai sannan ta datse Kiran.

Shi kan shi Modibo yasan dan Yana gurin ne take amsa wayar a haka, kusan mitin latin da yin wayar su da Afnan ta kalli Modibo ta kawar dakai sannan tace, inje in gaida Ammi?

   Tunkan ta rufe baki yace a’a.

     Komawa tayi ta lafe a kujerar ji take rayuwar duk babu dadi yau.

     Misalin 12 ya fita dan haka taji kamar an kwacen ta.

Ammi ta fara Kira suka gaisa sannan ta ta Kira Dada, Nan Dada ke gaya mata gobe zasu koma gida bayan ta sauke wayar Yadikko ta kira suka gaisa sannan ta sauke wayar.

   Jin ana Kiran sallah ta mike ta koma daki alwala tayi tai sallah sannan ta dan kwanta.

    Batafi Minti 15 da kwanciya ba taji an shigo falon da Alama bashi kadai bane m
domin tana jiyo muryoyin muta ne.

Gajiya da kwanciyan yasata yin wanka ta canza Kaya tana kokarin daura Dan kwali Modibo ya kirata awaya.

    Dauka tayi tare da Sallama, daga can cikin wayar yace, ”  ki zo ku gaisa.

   amsawa tayi da toh sannan ta karasa dauren sannan daukin gyale ta fito.

     Suraj Magaji da Muftahu ta hanga baje afalon kowa da abinci a gaban shi, Zama tayi tana gaidasu a tare, suma kusan hada baki suka yi gurin Amsawa, da Mutum biyu suka had’a Ido Muftahu da Suraj, Magaji ko gaba daya hankalin sa nakan abincin dake gaban shi, ta dan jima zaune tanajin yadda suke lomar abincin tare da Surutu cikin daga murya .

  Mikewa tayi ta koma daki sai a yanzun take kallon kayan gadon acikin ranta take fadin, yanzun nice Allah yaiwa irin wannan darajar.

******

Jikin Momy Safna ta fada tana dawowa daga falon Modibo, cikin fashewa da Kuka tace, ” Momy bazan iya gani ba, mijina tare da wata, wlh zuciyata zata fashe.

   Yanzun Safna duk lallashin da nake miki baza kiji ba, duk abun da nagaya miki sai kin nuna kinji daga kin had’u da Mijin ki saiki sake birkice min, idan kikai wasa Zaki rasa Modibo Safna, da Yaya muka samu kanshi har yake kallon ki amatsayin matar auren shi?, kina zaune a gida nikadai nasan wahalar Dana sha, har daji na shiga wajen kokarin in nemo miki farin ciki.

   Shikanshi wannan auren dan an shammace nine amman wallahi da Modibo yayi kadan ya kawo miki wata cikin gidan auren ki, da sunan wai kishiya, tunda abun a yazo ahaka sai kiyi hakuri ki zuba min Ido nikuma nayi alkawarin saina saki farin ciki, badai kishiya bace baki so?, toh kisa ranki a inuwa.

Ammi naso in daure amman bakiga abun da yariyar keyi ba, sai wani shagwargwabewa take yi, shi kuma munafukin Yana wani biye mata, ga wani kallo da take jefa mishi irin na karuwai, Sam Bata da kunya daker ma ta  gaishe ni, Saida yaita mata mgn.

   Kibarni dasu Safna karki yadda ki nuna mata hakan ya daga hankalin ki, koshi kanshi ki bani lokaci zan baki Mamaki.

                      ****

Misalin karfe 10 na dare Modibo ne ya rufe kofar sannan ya shigo cikin dakin cikin Shirin Bacci.

Tuni Safna ta kwanta tare da rufa cikin bargo, ahankali  ya Mika hannun sa ya ya  janye bargon, tare da fadin, ” tashi ki zauna muyi mgn.

  Kamar yadda yace haka tayi sannan ya dubeta yace, ” Bakisan kiga mutum yana fushi bane ki bashi hakuri?

    Nasani, ta fada Ahankali.

Toh meya hana ki bani hakuri alhalin kinsan kin bata min rai.

Kayi hakuri ta fada, saidai can karkashin zuciyarta Kara kulewa tayi dashi.

Kawar da kanshi yayi tsayon lokaci zuwa can ya juya ya kalleta sannan yace kwanta abun ki.

Kamar jira take ta kwanta Kamar yajja yace, mikewan sa taji tsayon lokacin sannan tajishi Yana kwanciya agefenta, can karshen ta matsa duk domin ta bashi ishashshen guri domin karya tashi da safe yace jikin shi na mishi ciwo.

   Ganin ta Kara takurewa guri daya ya dubeta yace, ” ya kika takure kuma? ki kwanta Mana dakyau.

Batace komai ba.

Ina mgn kin min shiru?

Kasa kasa tace nan ya isheni.

A’a ki gyara kwanciyar ki.

Dan matsowa yayi kadan dan dan haka ya rabo da ita hakan, bayan kaman minti biyar taji hucin shi daf da ita, duk da cewa baya ta juya masa tasan yana kusa da ita Kara baza kunnenta tayi sosai, karaf taji ya zagayeta da hannun shi, da karfin ta ta fara ture shi tare da tarin Mamaki a tattare da ita, sosai takejin fargaban abun dake Shirin faruwa tsakanin su, ganin yadda take turesa shi iya karfinta yasashi ya bita da kallo yana fadin, ” danbe zakiyi dani?

  A’a ta fada jikinta na matsanancin rawa.

  Toh ki maida hankalin ki jikin ki, duk inda kike tunanin abun ya wuce haka, aure ba abun wasa bane, nayi hakuri iya wadda zan iya, dan haka bazan saurari shirmen ki ba.

Toh-toh Ina zuwa tsaya kaji!

Me zanji me zaki Kaya min? Modibo ke fadin haka hannun shi runtse da cikin ta.

  Hannunta tasa tana kokarin cire nashi tare da fadin, ” dan Allah ka tsaya kaji”

    Ni banason jin wata mgn daga gareki Unaiss, domin ko anki ko anso yau zan amshi hakkina.

  Kasa cewa komai tayi wannan karon yayin da take tunoshi lokacin da yake shigowa gidan Innaworo kamulallan mutum me mutunci, wadda baya kallon mace da sigar sha’awa wai shine yau ke neman wani Abu ajikin ta, sosai abun ke mata girma, tana jinjina yadda wannan abun zai kasance tsakanin su, sannan wani abun daya Kara bata Mamaki yadda Modibo ko digon kunya babu a tattare dashi yake cewa saita bashi hakkin shi Kamar ba Modibon da ta sani ba.

  Tuni hawaye ya kece mata har yanzun tana rike da hannun shi yayin da ya dago yasa kanshi a wuyanta Yana goga mata gemun shi tare da fadin, ” ki sakeni in biki ahankali karki bari muyi dambe in jigata ki.

Wayyo Allah na ta fada ta karfi tare da ture gemon da yake mata waiwayi dashi awuya, ganin yana Kara shige mata sake rikicewa da karfi take Kiran kabarni zan kira Ammi fa!!

Ko Abba Zaki Kira Unaiss bakomai, ban ki ajimu ako Ina ba, ke matata ce, aurene ya bani daman kebewa cikin daki dake, kuma kowa yasan hakan, idan kin ga dama kita kurma ihu har gari ya waye kunyan ki ce.

Toh Bari kaji, tsaya Ina zuwa, barin gyara *Hamma Modibo* Ina zuwa dan Allah.

Basai kin gyara ba, ni zan gyaraki yadda nake so, kawai Ina baki shawara ne ki tsaya kawai karkice zakiyi danbe dani.

A’a bazanyi danbe dakai ba, wane ni, Unaisa ta fad’a jikinta na buka uban rawa.

  Toh ki tsaya kawai.

Naji toh zan tsaya, amman akwai zazzabi ajikina, dan Allah ka barni ko zuwa gobe ne.

  Naji Zazzabin naki ai, magani zan Baki, bana bukatar shi anan gidan, naga alama kina wasa dani, nariga nasan halin ki, idan har zazzabi da amai zaisa in barki kin dinga bayar min da bara bana kenan, domin wannan rudewan naki shine yake kawo miki zazzabi, adanci daya zan iya miki, shine na baki minti goma ki maido da hankalin ki jikin ki, idan ko har Kika bari na rikeki da zazzabi ajikin ki bazan sake ki ba sainaji zazzabin naki ya sauka.

17 comments

  1. Pingback: ricco888
  2. Pingback: Gifts
  3. Pingback: šeit
  4. Pingback: นิยาย
  5. Pingback: mostbet
  6. Excellent post. I used to be checking constantly this blog and I’m inspired! Very useful information particularly the closing phase 🙂 I handle such information a lot. I used to be looking for this particular information for a very lengthy time. Thanks and good luck.

  7. Do you mind if I quote a few of your articles as long as I provide credit and sources back to your blog? My blog site is in the exact same area of interest as yours and my users would really benefit from some of the information you provide here. Please let me know if this ok with you. Thanks a lot!

  8. Pingback: ISIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *