
BA LABARI BOOK 2
by
FADILA LAMIDO
page 19
Yanzun kuna Ina?
Shiru yayi tsayon lokaci sannan ya sauke wayar.
Yadikko ce tace lafiya?
Jimmm yayi kadan zuwa can yace Yadikko abun da ya faru shekarun baya ne ya sake faruwa.
Subuhanallahi, wai me yake faruwa ne?, menene haka?
Suraj ne yace, ” Yi ake yi ai wasu mutan nan azalumai ne fa.
Jigum taga sunyi hankalin su duk a tashe.
Suraj ne ya fara juyawa sannan yace ma Modibo muje.
Fita sukayi, yayin da Yadikko take fadin, Allah ya bata lafiya.
Bayan sun fita Yadikko da maido da hankalin ta kan Unaisa, kallon ta tayi sosai sannan tace, ” ke kuma meye matsalar? me zaisa ace har yanzun baza banbance tsakanin su ba?
Yadikko inafa gane shi kawai yau ban kalle shi bane, kuma afalon shine tare da matar sa suke zaune.
Jimmm Yadikko tayi zuwa can taji agaban matar tasa kikai hakan?
Kawar dakai Unaisa tayi hawaye na zubo mata tare da fadin eh har dariya ma tai min.
Dole ta miki dariya Rahma, mijin ki ne fa.
Kamar jira Rahma take ta Kara fashewa da kuka dariyar da Safna ta mata kawai take tunawa, ahankali tace wlh ammi ban kalleshi bane.
Idan baki kalleshi ba ai yayi mgn ko muryan tasu ma iri daya ce?, ke wacce irin mashiriciyar yariya ce, kitashi kiyi wayau ki bude idon ki dakyau zaman kishi zakiyi karki bada kofar da za’a raina ki.
Hawaye Unaisa ta share yayin da Yadikko tacigaba da cewa, ” Safna atsaye take, kuma gida daya zaku zauna, ai saiki jama kanki raini gurin kishiya, dole sai kinyi wayau idan ba hakaba kuwa Ina kallo mijin zai gagare ki, sannan ki tsayo da addu’a domin akwai wasu al’amura da suke faruwa, wadda dole mutum yai tunanin sihiri ne yanzun gashi nan yau aka kai akwatin auren Modibo yau yariya tafara yage kayan jikin ta, yanzun kina ganin ina labarin daura auren?
Sunkuyar dakai Unaisa tayi tana sauraron Yadikko tare da share hawaye, Yaddiko cigaba tayi da cewa, ” biyu kenan wadda irin hakan ya faru, wani kuwa saidai iyayen sukira sune sun fasa bashi, na karshen wadda akayi ko Yana hanya zashi ganin yariyar mota ta wuntsula dashi tun kafin ayi asibiti dashi yake cewa ya fasa, wannan dalilin yasa naji tsoro Dana ganshi cikin damuwa ayau, dan Allah kisa hankalin ki ki kula da kyau miji fa ba abun wasa bane.
Yaddiko ta jima tanama Unaisa fada sannan ta barta ta fice adakin.
Gefen gadon Yadikko ta kwanta har yanzun abun nai mata ciwo yadda Safna taita mata dariya.
Da daddre tana zaune afalon Yadikko Dada ta kirata cikin waya, bayan ta daga fada taita mata akan lafin datama Modibo daxon, tsayon lokaci ta dauka tana fadan Saida tagama Unaisa tace, Ina fa gane su ban kalle shi bane, ta inda Dada take shiga batanan take fita ba dan haka bayan ta sauke wayar duk jikin ta yai sanyi, sabo da damuwa harji take daman adawo da lokacin baya ta gyara kuskuren ta.
Da daddare ma zazzabi ne ya rufeta bata tashi sannin damuwar Modibo ya dameta ba saidata kwanta taji bacci ya gagare ta, data rufe Ido tunanin sa take, ganin sa take lokacin da yake ta fadan cikin motar, tsintan kanta tayi dason ta bashi hakuri, Bata kawo tunanin komai ba ta shiga Kiran shi, saidai harta katse be daga ba, kallon wayar tayi sai lokacin da kula da lokaci karfe daya da da kwata, gefen ta aje wayar tana Dana sanin Kira, bayan kusan minti goma da Kiran sa taji kira ya shigo wayar ta, da sauri ta dauka Ganin Modibon ne ta diriri ce da Sanyin jiki sosai ta d’aga wayar.
Ina wuni, ta fada ahankali.
Muryan sa cike da bacci taji yace, ” lafiya lau, ya kike?
Kasa kasa tace lafiya lau.
Jimmm suka danyin sannan yace Lafiya kuwa?
lafiya lau ta sake fadin.
Toh me ya hanaki bacci har wannan lokacin baki bacci ba?
Kayi hakuri dan Allah, Tafad’a a hankali.
Har cikin zuciyan shi yaji wani sanyi ya ratsashi, toh shikenan badamuwa, kiyi baccin ki nayi waya da Yadikko gobe zanzo na dauke ki.
Tam ta fada ahankali, sannan ta sauke wayar.
Washegari ta tashi zuciyarta da sauki damuwa dan haka ta shiga harkokin ta da yaran abokiyar zaman Yadikko Khadija da Amina, hira sukayi sosai sai gurin sha daya na safe ta baro part din su, Samun Yaddiko tayi tagana shiri tana yafa bayafi.
Yadikko fita zakiyi ne?
Eh zani gidan ku, kina nan ko inje abu na?
Ina nan nikam.
Tafiya tayi yayin da Unaisa ta fara yi mata ‘yan aikace aikace.
Tun daga ranar Bata sake sanin halin da gidan ke ciki ba har aka dauki tsayon sati biyu, tun Afnan na Kiran ta awaya tana tambayan ta yaushe zata dawo har tagaji ta bari.
Zaman su suke ita da Yadiko har abincin sunaci cikin kwano daya, sosai suka saba, ranar data cika sati na Uku a gidan Ammi ta kirata cikin waya bayan sun gaisa tace, Yaushe zaki dawo tun da baki zauna kinga saukan amaryar ba ai sai ki dawo haka ko?
Nakusa dawowa fa Ammi.
A toh zaman dai ya isa haka, ki dawo ko sai an biyo sawun ki??
Yadda Ammi ke mata mgn yasata jin kunya tare da kasa yin mgn.
Afnan tazo ta taho dake?, Ammi ta sake fada cikin sigar tambaya.
Ahankali Unaisa tace a’a.
Toh Sai Modibo yazo da kanshi kenan?
Cikin kukan shagwaba Unaisa tace a’a Ammi ki Bari, zan dawo fa.
Kidai Bari yazo da kanshi daman ya fada yace fushi kikayi kibar gidan.
A’a gobe zan dawo Ammi ba haka bane.
Hmmm, toh sai mun ganki, ba Maman taku wayar.
Mikawa Yaddiko tayi tanajin Yadiko tanata dariya tare da kallon Unaisa tana fadin, aiba laifi bane ko haka din ne, wato shiyasa ko lekowa baya yi.
Dariya Yaddiko taitayi sannan ta mikawa Unaisa wayar tare da fadin, kinsan an fasa auren ma kuwa?
Jimmm tayi Saida gaban ta ya fadi sannan tace bikin wa?
Auren Modibo.
Girgiza Kai tayi tare dajin ta Kamar cikin bacci take.
Allah besa zamuyi mgnr ba, ai tun daga ranar da akai akwatin mgnr auren ya fasu, sunkai akwati suna hanyar dawowa akace yariyar babu lafiya haka waccen karon akayi itama kamar tayi hauka sai a hankali ta dawo hayyacin ta.
Shiru tayi tana nazarin wannan al’amarin wadda takejin sa tamkar a mafarki Bata kawo komai ba saidai ta rasa me takeji farin ciki ne ko farin ciki.
Adaren ranar ta fara Shirin tafiya gida,
Washegari bayan tayi sallar Asuba tana d’akin su Khadija taji gidan ya cika hayaniya da yawa, kuma tun kafin ashiga masallaci takejin Karar motoci na shigowa dan haka ta fito ta nufi dakin Yadikko saidai tana tura kofar taja ta tsaya ganin dakin cike makil da mutane.
Cak ta tsaya rike da kofar tana kallon cikin dakin da hasken fitulo ya haske kowa, Wani gafjejen mutun ta hanga babu riga du’ke akan wadda tafi kyautata zaton Yadikko ce, gefe kuwa dama da haku mutane ne mata da maza, Magaji tsaye rigarsa a baibai, kowa kagani a gurin a yamutse yake hango Ammi tayi akan gadon Yaddiko itama rigar bacci ne da mayafi kawai ajikin kita.
Sakin kofar tayi a hankali sannan ta fara takawa cikin dakin a matukar firgice domin gani take kamar yadikon muwa tayi.
Tana isa tsakiyar dakin taja ta tsaya, ganin har yanzun wadda ke duke akanta be dagoba yasata fashewa da kuka.
Cikin fada taji yace waye wannan??
Ammi ce tace yishiru Rahma ba’ason hayaniyar dawo nan ki zauna.
Gefen Ammi ta zauna tare da Satan kallon Yadikko dake kwance kamar gawa.
Kallon ta ta maida Kan mutumin dake gefen ta din, Modibo ne sai a yanzun ta kula, Ammi ya kalla sannan ya dan dago Yana fadin, ” ta samu bacci”
Alhamdulillah ya fada, sannan ya juyo kadan ya kalli Rahma, kawar da kansa yayi yace, Suraj bani riga insa.
Juyawa Suraj yayi yayin da Modibo ma ya tashi ya bi bayan sa.
Ahankali sukayi ta fita ya rage daga Ammi sai Rahma.
Har gari ya waye suna zaune, misalin bakwai da rabi Yadikko ta tashi hawaye take sharewa ta gefen idonta yayin da Ammin ta shiga fadin, Kibar kukan nan haka ko?
Abun namin ciwo ne, duk iya kokari na na kawar dashi abun ya dame ni, nakasa goge abun araina.
Nasan akwai ciwo, amman ki jure ki cinye wannan jarabawar, kinga dai dun inda ake tunanin ganin shi BA LABARI
Wani sabon hawaye ne ya zubo mata, adaidai lokacin da Modibo da Suraj suka shigo.
Modibo ne yace, Yadikko wlh banason ganin kwalla a idon ki, nasan dole abun ba dadi, amman yaci ace kinsa ma zuciyarki sauki.
Suraj ne yace, aini wlh Mama Mamaki take bani, sabo da wannan abun da kike na tsana duk wani abu daya dangaci *Abdurrahaman Masood* shekara sama da goma kullum cikin rarrashin ki nike ance kibar mgnr kingi ki bari.
Bazan Bari ba Suraj, nasan dakai ubana ne da yanzun ka tsini min, ka tafi kaje kayi harkokin ka, naji sauki, nagaji da korafin ka.
Modibo ne yace, A’a Yadikko hakuri zakiyi, Suraj Kai kuma Kai shiru, wannan karon dakan mu zamuyi bincike indai ba mutuwa yayi ba za’a ganshi, insha Alhahu indai akan wannan ne kin kusa daina kuka, ko ki ganshi ko kije tabbataccen labarin mutuwar sa daga bakin makusantan shi.
Da haka suka rarrashi yaddiko, da rana suka wuce bayan sun tabbar jinin yadikko ya sauka yadda ake so, Afnan kuwa sai yamma tazo tagaida Yadikko sannan suka koma tare da Rahma.
Ta koma da kwana uku suka koma makaranta, dan haka sosai suka maida hankalin su Kan karatu su, tana daukan kwana uku hudu Bata hado da Modibo ba, amman Magaji da Muftaho kullum suna dakin Ammi, Nan ne gurin hirar su, kullum dare ita da Afnan suna dakin Ammi hakama Magaji da Muftahu a yanzun ta lura dasu tsakanin Magaji da Muftahu Shirin suke sosai hakama Suraj da Modibo, abakin Ammi takejin ai sai hali yazo daidai ake abota, yanzun Magaji baya kulata, saidai har yanxun Yana nan da yawan kallon shi, sai ita tun da ta kula Modibo baya son fadan da take da Magaji ta daina bin takan sa
BAYAN SHEKARA DAYA
Babban falon Abba su Modibo ne cike makil da baki maza wadda sukasha manyan kaya na alfarma, bayan gaisawa ne , daya daga cikin bakin yace, “Alhaji wani abun alheri ne ke tafe damu, d’an waje nane yaga ‘yar wajen ka yake son a bashi auren ta, tunda ya gaya gaya min nace toh zamuzo mu nemi izini.
Dariya sukayi gaba daya cikin zallar farin ciki, Abba ne yace, ” Allah ya daidai tasu, indai sun daidai ta ai wannan babu matsala bsne, samarin dake gefe Abba ya kalla sannan yace wanne acikin su.
Daya daga cikin Samarin ne ya nuna dayan, murmushi Abba yayi tare da fadin toh Allah ya daidaita ku.
Amin kuwa yace sannan Maifin Samarin ya sake cewa ita dayar yariyar ka mata Miji ne?
Abbane yace ai ni ‘ya mace daya gare ni, ita daya ce Afnan.
A’a akace min yaran biyu ne?
‘Yata daya itace Afnan
Juyawa Mutumin yayi yace kukace min su biyu ne?
Daya daga cikin Samarin ne ya sake cewa su biyu ne muke gani tare tare suke zowa makaranta
Kai A’a, Afnan ita daya ce agidan nan
Daya saurayin ne yai karaf yace, Unaisa ita wadda mukazo mgn akai din sunanta Unaisa
Unaisa Abba ya maimaita sannan ya juya ya kalli Modibo, saurin mikewa Modibo yayi yana kokarin ficewa, Abba ne yace Modibo, akwai wata yariya ne acikin gidan nan me irin wannan sunan?
7 comments
Comments are closed.